Amurka za ta ƙaddamar da rundunar amfani da jirage marasa matuƙa

Asalin hoton, US Central Command via Getty Images
Rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta sanar da shirin kafa rundunar farko da za ta haɗa ƙasashe da dama domin amfani da jirage marasa matuƙa na kai hare-hare a yankin.
Amurka ta ce ta fara tattaunawa da ƙasashen yankin tare da aika musu gayyata a hukumance domin su shiga wannan shiri.
An sanar da hakan ne a daidai lokacin da kwamandan CENTCOM, Janar Brad Cooper, ke gudanar da ziyara a wasu ƙasashen yankin, ciki har da Saudiyya.
A cewar CENTCOM, sabuwar rundunar da aka sanya wa suna Falcon Strike Task Force, za ta ƙunshi jirage marasa matuƙa masu kai hare-hare da za su iya aiki a sararin sama, a saman ruwa, har ma a ƙarƙashin ruwa.
Rundunar ta ce Amurka da ƙasashen yankin ne za su riƙa tafiyar da wannan shiri tare.
Haka kuma, ta bayyana cewa wannan sabon shiri faɗaɗawa ne ga wani shirin da Amurka ta fara watanni tara da suka gabata mai suna Scorpion Strike, wanda shi ma ya dogara ne kan amfani da jirage marasa matuƙa wajen ayyukan soja.
Amurka ta ce ta yi amfani da jiragen marasa matuƙa na rundunar Scorpion Strike wajen kai hare-hare kan wasu tashoshin jiragen ruwa da ke kudancin Iran, kuma jami'an da suka yi aiki a wannan runduna su ne za su ci gaba da tafiyar da sabon shirin Falcon Strike tare da haɗin gwiwar ƙasashen yankin.





















