Ko akwai ƙasar da za ta iya taka wa Faransa birki a gasar bana?

    • Marubuci, Neil Johnston
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist at New York New Jersey Stadium
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ba wai ƙwarewarsu a ɓangaren cin ƙwallo ne kaɗai ya kamata abokan hamayyar Faransa a gasar cin kofin duniya su damu da shi ba.

Bajinta da haɗin kai da ƙawarewar ƴan wasan wannan tawagar ta Les Bleus ya kamata ya tayar da hankalin ragowar tawagogin da suka rage a gasar - kuma an baje kolin wannan bajninta a wasan da aka yi a ranar Talata inda faransa ta lallasa Sweden da ci 3-0.

Bayan da Kylian Mbappe ya zura ƙwallo ta farko a raga, ɗan wasan da ya fi kowa zura kwallo a tawagar Faransa ya ruga kai tsaye ya rungumi mai horaswa Didier Deschamps.

Babban kocin tawagar ya koma aiki gadan-gadan a karon farko tun bayan da ya dawo daga Faransa, inda ya halarci jana'izar mahaifiyarsa.

Murnar da suka yi da Mbappe abu ne mai sosa zuciya.

Sauran ƴan wasa sun zo daga baya sun rungumi Mbappe da Deschamps.

Bayan wasu ƴan kwanaki masu cike da baƙin ciki, Deschamps ya samu dalilin da zai yi murmushi a lokancin da ƴan wasansa suka nuna bajintar su a wasan da aka buga a filin wasan New Jersey, inda suka samu gurbi a zagayen ƴan 16 na gasar bana wanda za su kece raini da Paraguay a Philadelphia ranar Asabar, 4 ga watan Yuli.

"Akwai cikakken haɗin kai tsakanin ƴan wasan wannan tagawar kuma sun yi abin da ya kamata a lokacin da ba na nan [makon da ya gabata]," in ji Deschamps bayan wasan.

"Haɗin kai kaɗai ba zai sanya ku yi nasara a wasanni ba. Amma na san idan aka samu akasin haka, za ku iya yin rashin nasara a wasanni. Haɗin gwiwa da aiki tare ya fi komai."

Ɗan wasan tsakiya Aurelien Tchouameni ya ƙara da cewa: "Mun san kocin yana cikin wani mawuyacin hali, muna yin bakin ƙoƙarin mu ga cewa mun faranta masa rai."

Bradley Barcola ne ya ci ƙwallo na 2 kafin Mbappe ya ƙara ta uku inda ya kamo Lionel Messi na Argentina da kwallaye shida a fafatawar neman zama ɗan ƙwallon da ya fi zura ƙwallo a wannan gasar.

"Ba za ku iya dakushe irin wannan bajintar ba," tsohon ɗan wasan Ingila Ian Wright ya shaida wa ITV Sport.

"Faransa na ɗaya daga cikin waɗanda za su iya lashe gasar nan, nesa ba kusa ba, suna da dama fiye da yadda aka taɓa gani a gasar cin kofin duniya."

Tsohon abokin wasan Wright na Arsenal, Patrick Vieira, wanda ya lashe gasar cin kofin duniya da Faransa a 1998, ya ƙara da cewa: "Sun nuna wa kowa cewa su ne ƙungiyar da kowa zai sha wahalar dokewa."

Bai yi kuskure ba.

Yayin da Mbappe ya taka rawar gani wurin cin ƙwallo biyu, Michael Olise ya taimaka an zura ƙwallaye biyu a raga, inda ya kai 5 a gasar, yayin da Faransa ta zama ƙungiya ta farko da ta zura ƙwallaye uku ko fiye a wasanni biyar a jere a gasar cin kofin duniya.

Wasa ne da ya burge ɗaukacin ƴan kallo 80,000 da suka taki sa'an kasancewa a cikin filin wasan, wanda hakan ya haifar da tambayar: shin akwai ƙasar da za ta iya gwada ƙwanji da Faransa a gasar 2026 kuwa?

'Ban ga tawagar da ta kai ta Faransa ba'

Shekaru huɗu bayan ta sha mamaki a bugun fenariti a wasan ƙarshe da ta kara da Argentina a Qatar, tawagar Les Bleus ta ƙuduri aniyar yin gyara da kuma lashe kofin a wannan karon.

Sun zubar da ƙwallaye da dama a wasansu da Sweden inda suka kai hari har sau 25 - adadi mafi yawa da suka taɓa samu a wasan gasar cin kofin duniya tun 1998.

Amma duk da haka Faransa ta zura ƙwallaye 13 a wasanni huɗu da ta buga a Amurka kuma alƙaluman ta ba irin na kowa ba ne.

Wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or, Ousmane Dembele ya na da hannu a ƙwallaye shida da aka zura a raga (Ya ci huɗu, ya taimaka an zura biyu), Michael Olise ya taimaka an zura ƙwallo biyar ya bugi turken raga inda ya watse da ƙwallon a wasansu da Sweden.

Amma da Mbappe, suna da ɗan wasa da ke kan ganiyarsa, wanda ke ji da kansa, kuma yana gaskanta kirarin da ake yi masa na ɗaya daga cikin waɗanda suka fi iya zura ƙwallaye duniya.

Ba gogayya kan lashe takalmin zinaren gasar bana kaɗai yake yi ba - ɗan wasan na Real Madrid a yanzu yana da ƙwallaye 18 a tarihin gasar cin kofin duniya, ƙwallo ɗaya a bayan Messi wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin gasar.

Kyaftin ɗin Faransa ya zura ƙwallaye biyu ko fiye da haka a wasanni bakwai daban-daban na gasar cin kofin duniya, fiye da kowane ɗan wasa.

"Abin da muka gani daga Faransa zallar iyawa ne da tsantsan bajinta," tsohon ɗan wasan Ingila Gary Neville ya shaida wa ITV Sport.

"Ƴan wasa huɗu na gaba da suka fara wasan (Mbappe, Dembele, Olise da Barcola) - za su haifar da tashin hankali a zuciyar duk wani mai tsaron baya a gasar kuma a haƙiƙanin gaskiya ban san yadda za su iya daƙile haɗarinsu ba.

"Suna matsayin da ya fi na kowa, Brazil ta samu nasara a minti na ƙarshe, Jamus da Netherlands sun fita, Faransa na nuna wa kowa a wannan zagaye yadda ya kamata a ce ana yi.

"Sauran suna kallonsu suna tunani: 'Wannan shi ne matakin da ya kamata mu kai'."

Ko kocin Sweden Graham Potter ya yarda: "Ba abin kunya ba ne a ce wannan tawagar ta Faransa ce ta fitar da mu.

"Ban ga wata tawaga da ta fi ta kyau ba."

'Ta na cike da zaratan ƴan wasa'

Olise ya fara taka leda ne a Hayes & Yeading United yana da shekara shida.

Shekara 18 bayan wannan lokaci, tsohon ɗan wasan Crystal Palace yana nuna wa duniya cewa shi ba kanwar lasa ba ne kuma a dandali mafi girma a duniya.

An haife shi a Hammersmit, mahaifinsa ɗan Najeriya ne kuma mahaifiyarsa ƴar Faransa ce amma ƴar asalin Algeria, Olise shi ne ɗan wasa na farko da ya taimaka aka ci ƙwallo biyar ko fiye da haka a gasar cin kofin duniya ɗaya tun 1994.

Deschamps ya ce "Michael yana buga ingantaciyar ƙwallon ƙafa."

"Ya na matuƙar tasiri a cikin tawagar ƴan wasan kuma shi ne ya ke zama mahaɗi tsakanin ƴan wasan gaba da masu tsaron baya.

"Shi mutum ne da bai cika hayaniya ba, amma ba haka yake a cikin filin wasa."

Wannan tawagar ta Faransa tana kafa tarihi a duk lokacin da ta buga wasa.

Dembele da Mbappe sun haɗa hannu a ƙwallaye shida a Amurka – Dembele ya taimaka wa Mbappe sau huɗu yayin da shi kuma Mbappe ya taimakawa Dembele sau biyu.

Wannan adadin ya fi na kowane yan wasa biyu da aka samu tun gasar1966.

"Suna da tawaga ce da ke cike da fitattun ƴan wasan gaba," kamar yadda tsohon ɗan wasan Scotland Ally McCoist ya shaida wa ITV Sport.

"Babu wani ƙarin bayani da za a yi da ya wuce haka. Su ne aka fi kyautata zaton za su lashe gasar, waɗanda aka fi sanya wa rai ba koyaushe ne suke yin nasara ba, amma akwai dalilin da ya sa ake kyautata musu zato, kuma mun ga haka a yau."

'A tafi sannu a hankali'

Idan har Faransa ta yi nasara a wasanni biyar a cikin biyar sannan ta hanyar doke Paraguay, za ta kara da waɗanda suka yi nasara a wasa tsakanin Canada da Morocco a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a filin wasan Boston a ranar Alhamis 9 ga watan Yuli.

Duk da haka Deschamps yana taka tsantsan.

"Don Allah, a bi sannu a hankali," in ji shi lokacin da aka tambaye shi a taron manema labarai bayan wasan ko tawagarsa za ta iya lashe gasar baki ɗaya.

"Mun kai zagaye na 16. Mu yi farin cikin hakan, mun san abin da ake buƙata daga gare mu.

"Mun yi abin da ya kamata mu yi duk da cewa mintuna 15 na farko sun kasance masu wahala.

"Da mun ɗan iya ƙara ƙoƙari a farkon wasan, mun kai zagaye na ƴan 16, amma zagayen ƴan 16 ne kaɗai. Dole ne mu kwantar da hankalinmu."