Jami'o'in Najeriya 10 da suka ciri tuta - Rahoto

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Najeriya ta samu ƙarin tagomashi a jerin jami'o'i mafiya inganci na duniya, bayan da shafin Times Higher Education ya fitar da jerin jami'o'in da suka ciri tuta a shekarar 2026.

Jami'o'in Najeriya 24 ne suka samu shiga cikin jerin na bana, idan aka kwatanta da guda 21 da suka samu shiga a shekarar da ta gabata.

Ana wa jerin jami'o'in da shafin ke fitarwa kallon ɗaya daga cikin mafiya inganci a duniya.

Shafin ya ce ya fitar da jerin ne ta hanyar la'akari da abubuwa kamar ingancin koyarwa, da hanyoyin bincike, da haɗin gwiwa da jami'o'i na ƙasashen waje, da kuma alaƙa da kamfanoni.

A cewar shafin, rahoton da yake fitarwa duk shekara na taimaka wa masana da jagorori a ɓangaren ilimi da hukumomi da kuma ɗalibai wajen yanke hukunci a ɓangaren ilimi.

Jerin jami'o'in na wannan shekara ya sanya Jami'ar Ibadan (University of Ibadan) a matsayin ta farko a Najeriya, yayin da Jami'ar Legas (University of Lagos) take a matsayi na biyu.

Ita kuwa Jami'ar Bayero da ke Kano ta zo ne a matsayi na uku.

Ga yadda jerin jami'o'in na Najeriya yake daga matsayi na ɗaya zuwa na 10:

  • Jami'ar Ibadan (University of Ibadan)
  • Jami'ar Legas (University of Lagos)
  • Jami'ar Bayero (Bayero University Kano)
  • Jami'ar Covenant (Covenant University)
  • Jami'ar Landmark (Landmark University)
  • Jami'ar Ahmadu Bello (Ahmadu Bello University)
  • Jami'ar kimiyya ta tarayya (Federal University of Technology), Minna
  • Jami'ar Ilorin (University of Ilorin)
  • Jami'ar Jos (University of Jos)
  • Jami'ar Najeriya, Nsukka (University of Nigeria), Nsukka

Sai dai duk da wannan nasara da Najeriya ta samu, jami'o'i daga ƙasashen Afirka ta Kudu da Masar su ne suka kankane matsayi na farko-farko a jerin jami'o'in mafiya inganci a Afirka, inda Jami'ar University of Cape Town, da Stellenbosch University da kuma University of the Witwatersrand suke a matsayi na ɗaya da na biyu da na uku a nahiyar.

Jami'ar University Mohammed VI Polytechnic da ke Morocco ita ce ta huɗu, sannan jami'o'in Afirka ta kudu suka sake mamaye gurabe na biyar da na shida da na bakwai a jerin.

University of Ibadan da take a matsayi na ɗaya a Najeriya tana a matsayi na 22 ne a Afirka.

Waɗanne jami'o'i ne suka ciri tuta a duniya?

Jami'o'i biyar da suka fi inganci a duniya suna a ƙasashen Birtaniya da Amurka ne:

Jami'ar Oxford (University of Oxford) da ke Birtaniya ita ce a matsayi na ɗaya.

Jami'ar Kimiyya ta Massachusetts (Massachusetts Institute of Technology) da Jami'ar Princeton (Princeton University) da ke Amurka sun zo a matsayi na biyu da na uku.

Daga nan sai jami'ar Cambridge (University of Cambridge) daga Birtaniya da kuma Jami'ar Harvard (Harvard University) ta Amurka:

  • University of Oxford
  • Massachusetts Institute of Technology
  • Princeton University
  • University of Cambridge
  • Harvard University

Me masana ke cewa?

Masana a bangaren ilimi na ganin cewa jerin ya nuna cewa idan jami'o'in Najeriya suka himmatu za su iya gogawa da sauran jami'o'i na duniya, kasancewar a baya ba a samun jami'o'i da dama da ke shiga jerin.

"Samun jami'o'i 24 waɗanda mafi yawancinsu na gwamnati ne abu ne da ke ƙarfafa gwiwa sosai," in ji Aliyu Tilde, masani kan harkar ilimi a Najeriya, wanda ya ce a baya ba a cika samun jami'o'in Najeriya na samun gurbi a jerin ba.

Ya bayyana cewa babban darasi ga Najeriya shi ne ta mayar da hankali sosai wajen ƙarfafa wa jami'o'i da manyan makarantu gwiwa wajen zurfafa bincike ta yadda za a san su a faɗin duniya.

"Ya kamata a bai wa malaman jami'o'i ƙwarin gwiwa wajen ganin sun yi hakan," in ji shi.

Sai dai ya ce ya kamata su ma jami'o'i masu zaman kansu su ƙara zage damtse wajen ganin sun samu wakilci sosai a irin wannan jeri da ake fitarwa.