Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda zargin sauya sunayen ƴan takara ke haifar da barazana a APC
Yayin da jam'iyyun siyasar Najeriya suka fara shigar da sunayen ƴan takararsu na kujeru daban-daban a shafin Hukumar Zaɓe ta Ƙasar INEC, wata sabuwar ƙura ta sake tashi a cikin jam'iyyar APC mai mulki, inda wasu daga cikin ƴan takarar da suka yi nasara a zaɓukan fidda gwani ke zargin cewa an sauya ko kuma ana shirin sauya sunayensu duk da cewa su ne suka lashe zaɓe.
Dama dai tun bayan kammala zaɓukan fidda gwanin ne wasu mambobin jam'iyyar suka riƙa bayyana ƙorafe-ƙorafe kan yadda aka gudanar da zaɓukan, lamarin da ya sa jam'iyyar ta kafa kwamiti na musamman domin sauraron waɗanda ke zargin an yi musu rashin adalci.
Bayan kafa kwamitin ne kuma aka ga ƙorafe-ƙorafen sun ɗan lafa, wataƙila saboda fatan da masu ƙorafin ke yi na cewa za a sake duba koke-kokensu tare da gyara duk wani kuskure da aka samu.
Sai dai bayan da INEC ta ba wa jam'iyyun siyasa damar amfani da lambobin sirri domin shigar da sunayen ƴan takararsu a shafinta, sai aka fara ganin rahotanni iri-iri suna yawo a kafafen sada zumunta, waɗanda ke ikirarin cewa an maye gurbin sunayen wasu ƴan takara a wasu jihohi, lamarin da ya sake haifar da ce-ce-ku-ce da muhawara a tsakanin mambobin jam'iyyar da masu bibiyar harkokin siyasa.
Sai dai a wata hira da BBC Hausa, Daraktan Yaɗa Labarai na jam'iyyar APC, Malam Bala Ibrahim, ya ce jam'iyyar za ta tabbatar da yin adalci ga dukkanin ƴan takararta wajen shigar da sunayensu ga hukumar zaɓe.
Ya ƙara da cewa bai kamata a ɗauki jita-jita ko zarge-zargen da ba a tabbatar da su a matsayin gaskiya ba, yana mai kira ga mambobin jam'iyyar da su jira matakan hukuma kafin su yanke hukunci kan lamarin.
Ya ce ko da an sauya sunayen wasu ƴan takara a wasu wuraren ma, bai kamata duk wani ɗan jama'iyya ya tada jijiyar wuya ba, domin za a tabbatar da an sama mashi makomar da ta dace da shi.
A cewrasa ''Yanzu an riga an mika fama-famai ga wadanda suka samu nasara, muna jiran a dawo da su daga nan ne za a daura sunayensu, kafin karewar wa'adin da aka bayar''
Ya ƙara da cewa ''An bayar da dama masu korafi su gabatar, kuma an saurare su, kuma an yi adalci har ma kwamiti ya gabatar da rahotonsa ga jama'iyya, yanzu haka ana kan aikin dubawa, kuma abun da aka amince da shi shi ne zai ba wa jama'iyyar haske kan sunayen waɗanda za a sanya sunayensu, don haka ba abun mamaki bane a ga an sauya wasu sunayen''
''Muna sa ran duk wanda abun da za a yi bai masa dadi ba zai ci gaba da bayar da gudummawa da fatan idan an samu nasara za a iya waiwayar ka don ka ba da wata gudummawar, ƙila ma wadda za ta fi tasiri kan abun da kai ka so ka yi''
A lokutan shirye-shiryen zaɓe, musamman bayan kammala zaɓukan fidda gwani, jam'iyyun siyasa kan tattara sunayen waɗanda suka samu tikitin takara domin miƙa su ga Hukumar Zaɓe.
Sai dai a wasu lokuta, ana samun ƙorafe-ƙorafe daga wasu mambobi da ke zargin cewa ana ƙoƙarin maye gurbin wasu sunaye ko kuma sauya waɗanda suka yi nasara a zaɓukan fidda gwani.
Masana harkokin siyasa dai na ganin cewa duk lokacin da aka samu zargin sauya sunayen ƴan takara, akwai yiwuwar hakan ya haifar da matsaloli iri-iri.
Daga cikin irin waɗannan matsalolin akwai ƙarin ƙararraki a kotu, ƙorafe-ƙorafe ga shugabancin jam'iyya, da rashin gamsuwa daga magoya baya da kuma yiwuwar sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyu.
A wasu lokuta kuma, irin waɗannan saɓani kan shafi yadda jam'iyya ke gudanar da yaƙin neman zaɓe, musamman idan rikicin bai warware ba kafin fara kamfen.
Masanan sun kuma ce jam'iyya kan fi samun ƙarfi idan mambobinta sun amince da tsarin da aka bi wajen zaɓen ƴan takara, ko da kuwa ba kowa ne ya samu abin da yake so ba.
Ita dai jama'iyyar APCn ta bukaci mambobi da magoya bayanta su guji ɗaukar mataki bisa jita-jita kawai.
Ta ce abin da ya dace shi ne a jira bayanan hukuma kafin a yanke hukunci kan duk wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta.
A cewarsu, hakan zai taimaka wajen rage tashin hankali da kuma kare haɗin kan jam'iyyar.