''Yadda muka shiga cikin ƙunci bayan sace ƴaƴanmu yayin zana jarabawa a Borno’’

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Iyayen ɗaliban nan da wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ko ISWAP ne suka yi awon gaba da su yayin da suke rubuta jarabawar NECO a makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Lassa, a ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno, sun ce suna cikin matsanancin tashin hankali tun bayan aukuwar lamarin.

Wasu daga cikin iyayen sun shaida wa BBC Hausa cewa tun daga safiyar Litinin da suka samu labarin harin, rayuwarsu ta sauya, domin har yanzu ba su san inda 'ya'yansu suke ba, balle su san halin da suke ciki.

Sun ce abin da ya fi ƙara musu damuwa shi ne yadda har zuwa yanzu babu wani cikakken bayani daga hukumomi kan adadin ɗaliban da aka yi awon gaba da su, da kuma halin da ake ciki game da ƙoƙarin kuɓutar da su.

Wani mazaunin garin na Lassa, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce shaida wa BBC Hausa cewa tun bayan da aka fara jin karar harbe-harbe a makarantar ya garzaya wurin, amma ya tarar mutane na ta gudu domin tsira da rayukansu.

"Ni dai ƴaƴana sun tsira, amma har yanzu mutane da dama basu san inda 'ya'yansu suke ba. Mun zagaya asibitoci da wuraren da jami'an tsaro suka tara waɗanda suka tsira, amma ba mu gansu ba. Yanzu abin da muke yi kawai shi ne addu'a."

Ya ce suna tunanin maharan sun yi awon gaba da aƙalla ɗalibai 50, ko da yake daga bisani an ceto takwas daga cikinsu.

Ita kuwa wata uwa, cewa ta yi tun bayan da ta tabbatar cewa an kai hari makarantar da ɗiyarta ke rubuta jarabawa, ba ta sake samun sukuni ba.

"Mun tura 'ya'yanmu makaranta ne domin su rubuta jarabawa. Ba mu yi tunanin cewa za a zo a ɗauke su daga cikin azuzuwansu ba. Muna roƙon Allah ya dawo mana da su lafiya."

Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safiyar Litinin, lokacin da ɗalibai ke ci gaba da rubuta jarabawar NECO.

Shaidu sun ce wasu da ake zargin mayaƙan ISWAP ne sun shiga garin na Lassa a kan babura, inda suka nufi makarantar sakandaren gwamnati bayan sun bi ta kasuwar garin, wadda ke ci ranar Litinin.

Da isarsu makarantar suka fara harbe-harbe, lamarin da ya jefa ɗalibai, da malamai da sauran mutanen da ke harabar makarantar cikin ruɗani.

Bayan haka ne suka yi awon gaba da wasu daga cikin ɗaliban da kuma mata masu sayar da abinci a cikin harabar makarantar kafin su tsere zuwa cikin daji.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Borno, DSP Nahum Daso, ya tabbatar da aukuwar harin.

Ya ce jami'an tsaro sun yi artabu da maharan jim kaɗan bayan kai harin, lamarin da ya hana su cim ma duk abin da suka shirya.

"A kusan ƙarfe tara na safe ne aka kai hari makarantar sakandaren gwamnati ta Lassa. Maharan sun yi ta harbe-harbe sannan suka yi awon gaba da adadin ɗaliban da har yanzu ba a tantance ba. Kwamishinan 'yan sanda ya tura Area Commander na Askira/Uba tare da ƙarin jami'an tsaro, kuma suna ci gaba da laluben maharan a cikin daji" in ji shi.

Ya ƙara da cewa rundunar ba ta kammala tantance yawan mutanen da aka yi awon gaba da su ba, saboda bincike na ci gaba.

Wannan hari dai ya sake tayar da hankalin mazauna jihar Borno, inda hare-haren masu tayar da ƙayar baya ke ci gaba da barazana ga rayuwar al'umma duk da iƙirarin hukumomi cewa an samu ci gaba wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.

Ko a watan Mayun wannan shekara ma, wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari makarantar firamare da ƙaramar makarantar sakandare ta Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba.

A wancan lokacin, Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya shaida wa BBC Hausa cewa an yi awon gaba da yara 42, waɗanda suka haɗa da ɗaliban makarantar sakandare, da na firamare da kuma wasu yara da aka ɗauke su daga gidajensu, kuma har yanzu ba a gano su ba.

Ko da yake jami'an tsaro sun ce sun fara bincike bayan harin, lamarin ya sake nuna irin ƙalubalen tsaron da yankin ke fuskanta.

Tun daga shekarar 2014, lokacin da mayaƙan Boko Haram suka yi awon gaba da ɗalibai mata 276 daga makarantar gwamnati ta Chibok, makarantu a wasu sassan arewa maso gabashin Najeriya ke ci gaba da kasancewa cikin fargabar hare-haren masu tayar da ƙayar baya.

Daga bisani an kuɓutar da wasu daga cikin ɗaliban na Chibok, yayin da wasu suka tsere, amma har yanzu akwai waɗanda ba a san inda suke ba.

Masana harkokin tsaro na cewa hare-haren da ake ci gaba da kai wa yankunan kudancin Borno na nuna cewa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP har yanzu na da ƙarfin kai hare-hare a wasu yankunan da ke da nisa da manyan sansanonin jami'an tsaro.

Ga iyalan ɗaliban Lassa kuwa, babban abin da ya fi damunsu a yanzu shi ne su sake ganin 'ya'yansu.