BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Hukumar leƙen asirin Iran ta kama mutum 62 da ta bayyana da maƙiya
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 31 ga watan Maris, 2026.
Mece ce mashigar Bab al-Mandab da Iran ke barazanar sake rufewa?
Barzanar da Iran ta yi na rufe wata hanyar ruwa mai muhimmanci a Tekun Maliya ya janyo fargabar, kan yadda hakan zai ƙara kawo tsaiko ga kasuwanci a duniya.
Yadda naɗin ɗan ƙabilar Igbo a Afirka ta Kudu ya janyo tashin rikici
Rahotonni sun ce batun naɗin sarauta ne ya janyo rikicin, inda aka yi yunƙurin naɗa Solomon Egbonna Eziko a matsayin jagoran ƴan ƙasashen waje.
'A gabanmu aka yi wa wata fyaɗe har ta mutu' - Yadda fyaɗe ya zama ruwan-dare a sassan Sudan
Wasu mata da aka ci zarafinsu sun bayyana yadda gungun maza ke faɗa musu a lokacin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Darussa uku da ya kamata Trump ya ɗauka daga tarihi kan yaƙin Iran
Tarihi na neman maimaita kansa dangane da yaƙin da Amurka da Isra'ila suke yi kan ƙasar Iran tun kimanin wata guda, inda masu fashin baƙi da masharhanta ke ƙokarin gane alƙiblar yaƙin ta hanyar komawa baya a nazarci wasu abubuwa da da suka faru a tari. Abubuwan kuwa sun kasance guda uku:
Mece ce makomar Kwankwasiyya bayan sauya sheƙar Kwankwaso?
Ficewar jagororin tafiyar biyu za ta sauya fasalin ƙungiyar Kwankwasiyyar, wadda tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya kafa tun bayan komawarsa mulki tsakanin 2011 zuwa 2015.
Yadda aka zargi ƴansanda da ƙona gidaje da dukiya a jihar Kano
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne bayan wani samame wanda ya kai ga arangamar da aka kashe ɗansanda tsakanin mutanen wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Wudil, kan wasu gonaki.
Spain ta rufe sararin samaniyarta don ka da Amurka ta kai wa Iran hari
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 30 ga watan Maris 2026.
Ko sulhun da Pantami ya yi wa El-Rufai da Uba Sani zai ɗore?
Ƴan Najeriya na ci gaba da tafka muhawara musamman a shafukan sada zumunka game da sulhu da fitaccen malamin Addinin Musulunci Sheikh Ali Isa Pantami ya yi wa El-Rufai da Uba Sani.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 31 Maris 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 31 Maris 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 31 Maris 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 31 Maris 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
Ƴan wasan gaba da suka fi ƙwazo da zura ƙwallo a wannan ƙarni
Wannan maƙala ta yi duba da nazari ne dangane da ƴan wasan ƙwallon ƙafa da ke gaba da suka fi ƙwazo da yawan zura ƙwallo a tarihin ƙwallo a ƙarni na 21.
Madrid na son Fernandez, Juventus na harin Ugarte na United
Ɗan wasan tsakiyar Chelsea Enzo Fernandez na cikin jerin wadanda Real Madrid ke son ɗaukowa, yayin da Juventus ke sa ido kan ɗan wasan Man United Manuel Ugarte.
Bayern na fargaba kan masu son ɗaukar Kane, Silva na son barin City
Bayern Munich na kaffa- kaffa da ƙungiyoyin Saudiyya da ke son ɗaukar Harry Kane, Bernardo Silva na shirin barin Manchester City, Inter Miami ta fara tattaunawa da Manchester United kan Casemiro.
Newcastle na son Trafford, yayin da Madrid ke son ɗauko Wharton
Har yanzu dan wasan Manchester City James Trafford na cikin ƴan wasan da Newcastle ke son ɗauka, yayin da Real Madrid na cikin jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke son ɗaukar ɗan wasan Crystal Palace Adam Wharton.
Ina Salah zai koma idan ya bar Liverpool?
A tsawon shekarun da ya shafe a Anfield, Salah ya ci kwallaye 255 a wasanni 435, inda ya taimaka wa kungiyar lashe kofuna da dama ciki har da gasar Firimiya biyu da kofin Zakarun Nahiyar Turai.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Kwankwaso ya koma jam'iyyar ADC bayan fita daga NNPP
An gudanar da bikin komawarsa ne a gidansa da ke Kano, inda shugabannin jam'iyyar da ɗimbin magoya bayansa suka hallara domin tarbar sa.
Miyagun makaman da Amurka ke amfani da su wajen kai wa Iran hari
A wannan yaƙi, wannan jirgi ya yi tafiyar sama da sa'a 30 daga Amurka zuwa Iran, inda ya kai hari kan muhimman wurare.
Abin da muka sani kan kashe-kashe a Jos
Bayanan da aka samu sun bayyana cewa wasu mutane ne a kan babura suka kai harin na ranar Lahadi, inda suka kashe mutane a unguwar ta Rukuba.
Dalilanmu na tsawaita wa'adin rijistar ƴan jam'iyyu - INEC
Mai magana da yawun INEC, Zainab Aminu ta ce hukumar zaben ta fitar da sabon jadawalin ne bayan ƙorafi ko jan hankali da jam'iyyun siyasar ƙasar suka gabatar wa da hukumar.
'Irin lalatar da Epstein ya yi da mu' - Matan da suka fuskanci cin zarafi
Wani shirin BBC ya tattauna da Harrison da wasu matan da suka fuskanci cin zarafin su huɗu.
Iran ta lalata jirgin sojin Amurka da ke sansaninta na Saudiyya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 29/03/2026
Abin da ya sa na fice daga jam'iyyar NNPP - Kwankwaso
Matakin na zuwa ne bayan da manyan jiga-jigan adawar ƙasar ke ƙoƙarin ƙulla wani ƙawancen siyasa domin ''kawar da jam'iyyar APC a 2027''.
Wane ne zai maye gurbin mataimakin gwamman Kano?
Ajiye aikin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar ta fara yunkurin tsige shi saboda wasu zarge-zarge da ta ce suna da alaka da almundahanar kuɗaɗe, zargin da mataimakin gwamnan ya sha musantawa.
Amfanin shan ruwan zafi da safe ga lafiyar jikin ɗan'adam
Batun shan ruwan zafi da safe na ta karaɗe shafukan sada zumunta - amma shin wannan daɗaɗɗiyar ɗabi'a za ta inganta lafiya?
Yadda ake zargin Rasha da ingiza zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Angola
Wasu ƴan Rasha da Angola na fuskantar shari’a bayan zarginsu da shirya zanga-zanga, abin da suka musanta.
Makaman linzamin Iran sun faɗa tsakiyar Isra'ila
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassana duniya, Asabar 28/03/2026
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.



























































