KAI TSAYE, Gasar cin kofin duniya 2026: Sifaniya 0-0 Cape Verde

Takaitaccen Bayanin Wasa

Spain 0 , Cape Verde 0
Spain
Cape Verde
80 minutes , in progress
Hutun rabin lokaci Spain 0 , Cape Verde 0

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Cape Verde ta sauya dan wasa, Spain 0-0 Cape Verde

    Sidny Cabral wanda yake da katin gargadi sakamakon ketar da ya yi wa Lamine Yamal a cire shi daga wasan an maye gurbinsa da Joao Paulo.

  2. , Spain 0-0 Cape Verde

    Sai kuwwa ake da tafi da zarar Lamine Yamal ya taɓa kwallo.

  3. Sifaniya ta yi canjin yan wasa, Spain 0-0 Cape Verde

    Gavi da Fabian Ruiz sun fita daga fili, an kuma maye gurbinsu da Lamine Yamal da Mikel Merino.

    Yan kallo sai sowa suke lokacin da Yamal zai shiga filin wasa na Atlanta.

    Lamine Yamal # 19 na Spain ya mayar da martani yayin da aka maye gurbinsa

    Asalin hoton, Getty Images

  4. An je hutun shan ruwa

  5. , Spain 0-0 Cape Verde

    Har yanzu ba ci, ana kuma sa ran Sifaniya za ta ratsa bayan Cape Verde ta ci kwallo, amma har yanzu abin ya gagara.

  6. Cape Verde ce ta fara yin canji, Spain 0-0 Cape Verde

    Cape Verde ta fara yin canji inda Laros Duarte da Jovane Cabral da kuma Dailon Livramento aka maye gurbinsu da Willy Semedo da Deroy Duarte da kuma Nuno da Costa.

  7. Shiga cikin

    Pedri (Spain) ya dubi

    Asalin hoton, Getty Images

  8. , Spain 0-0 Cape Verde

    Vozinha yanzu ya hana kwallo ya shiga ragarsa a manyan hari biyar da Sifaniya ta buga masa a wannan wasan.

    Mai tsaron ragar Cape Verde #01 Vozinha yana riƙe da kwallon

    Asalin hoton, Getty Images

  9. , Spain 0-0 Cape Verde

    Gavi ya nemi takwaransa a Barcelona, Pedri daga gefen hagu ya kuma daga kwallon zuwa Mikel Oyarzabal, wanda ya kasa sa mata kai, sai dai Marcos Llorente ya samu dama ya buga amma ta yi sama da fadi.

  10. , Spain 0-0 Cape Verde

    Na tabbata Luis de la Fuente ya sanar da yan wasan Sifaniya mahimmacin cin wasan farko a cikin rukuni da yadda yake bai wa tawaga damar kaiwa zagayen gaba cikin ruwan sanyi.

    Luis de la Fuente (Spain) ya dubi

    Asalin hoton, Getty Images

  11. , Sifaniya 0-0 Cape Verde

    Spain sun fara matsawa sosai a yanzu

    Sun kwace ƙwallon a sama, sannan suka fara kai hari kai tsaye. Fabián Ruiz ya samu fili ya gwada buga kwallon daga nesa, amma ya wuce sama da raga sosai

    Wata dama ce daga Sifaniya wacce ta ci gaba da mamaye wasan, amma har yanzu Cape Verde tana da karfi wajen tare baya.

  12. Mun koma zagaye na biyu

    Ko Sifaniya za ta ci Cape Verde ko kuma za a ga abin mamaki.

  13. An busa hutu

    Za su hutu minti 15 daga baya su dawo su kuma yin hutun zuwa shan ruwa sannan a karkare wasan.

    Watakila kamar wasan Netherlands da Japan za a buga da suka ci kwallaye a zagaye na biyu.

  14. An shiga cikin karin lokaci, Spain 0-0 Cape Verde

    Har yanzu Sifaniya ba ta ci kwallo ba, wadda aka yi hasashen za ta yi wani abin kirki tun farko

  15. , Spain 0-0 Cape Verde

    Ferran Torres ya kara samun dama, amma da ya buga sai mai tsaron ragar Cape Verde ya kwanta ya tare da tuni ta fada cikin raga.!

  16. , Spain 0-0 Cape Verde

    Magoya bayan Cape Verde sun yi murna

    Asalin hoton, Getty Images

  17. An buga kwallo ya bugi turke, Sifaniya 0-0 Cape Verde

    Rodri ya bai wa Marc Cucurella kwallo, wanda ya mayar da ita cikin gidan cape verde, Sai Ferran Torres ya buga ƙwallon da ƙarfi sai ta daki sandar raga daga sama.

    Nan take kuma Mikel Oyarzabal ya biyo baya ya sa kai, amma mai tsaron gida Vozinha ya yi wani tsalle sama ya taba ƙwallo ta yi waje.

  18. , Sifaniya 0-0 Cape Verde

    A yau dai Sidny Cabral na taka rawar gani sosai a wasan.

    Ya kwace ƙwallo cikin ruwan sanyi, sai ya zura a guje ta gefen hagu. Yayin da yake ƙoƙarin ci gaba da kai hari, ya yi karo da Ferran Torres, wanda ya sa alkalin wasa ya ba Cape Verde bugun tazara.

    Cabral na nuna ƙwazo sosai, duk da cewa tuni ya riga ya samu katin gargadi a wasan.

  19. , Spain 0-0 Cape Verde

    Wata ƙwallo da 'yan wasan Cape Verde suka yi sakaci da ita daga baya ta ba Sifaniya damar kai hari.

    Ferran Torres ya yi wani kyakkyawar pass zuwa ga Mikel Oyarzabal, wanda ya kusa samun damar zura ƙwallo a raga. Amma sai Sidny Cabral ya tare wajen duk da zamewa da ya yi ya hana harin ya yi tasiri.

  20. , Spain 0-0 Cape Verde

    Marc Cucurella sai kazar-kazar yake ko ina ka ganshi, sai kokari yake domin tun kan hutu Sifaniya ta ci kwallo.