Da gaske ne mata sun fi maza tausayi?

Asalin hoton, Getty Images/ Javier Hirschfeld/ BBC
Binciken kimiyya ya ƙaryata abubuwa da dama game da ɗabi'ar nuna tausayi, sannan ya kawo sabbin bayanai kan abin da ya shafi tunanin maza.
Wani lokaci mutane na da tunani daban-daban kan jinsi, misali 'Bahaushe kan ce mace mai kamar maza', tamkar ana nuna cewa mace ba za ta iya nuna jarumta ba sai namiji.
Akwai wani lokaci da Sarauniyar Birtaniya Elizabeth ta ɗaya, ta ce za ta mulki Birtaniya duk da cewa tana da "rauni irin na mata."
Duk da cewa irin wadanan abu da mutane suka yi imani da su ababe ne da suka tsufa, amma har yanzu mutane na yi wa jinsi daban-daban kuɗin-goro.
Har yanzu muna da tunanin cewa asali a wuri halitta mata sun fi maza tausayi tausayi, haka nan kuma ana kallon maza a matsayin masu son babakere da nuna iko.
Ko da mace tana ƙoƙarin nuna iko, za a ga cewa namiji ya fi ta zaƙewa da jajircewa wajen yin babakere.
Amma ɗaya daga cikin ɗabi'ar da aka shaidi mata da ita, ita ce tausayi.
Mata na da tausayi kuma zuciyarsu na da saurin yin rauni, amma ana kallon maza masu tausayi a matsayin masu rauni.
Amma me ya sa ake da wannan tunanin? Da gaske ne mata sun fi maza tausayi ko kuwa kawai tunanin mutane ne?
Wannan kuɗin-goro da muke wa jinsuna kan shafi yadda muke bai wa ƴaƴanmu tarbiyya, da yadda muke tafiyar da lamurra a wurin aiki.
Amma wani abu da ba mu cika lura da shi be shi ne yadda irin wannan kuɗin-goro kan yi tasiri ga mutane tun suna ƙanana kuma ya ci gaba har zuwa girmansu.
Sinadaran jiki da ke sa tausayi
Tausayi ya ƙunshi iya gane halin da mutum ke ciki da tunanin da yake yi sannan a ba shi taimakon da yake buƙata.
Ana kuma iya fahimtar tausayi a matsayin iya gane yanayin da mutum ke ciki sannan a taimaka masa.
Masana kimiyya na amfani da hanyoyi daban-daban wajen gwada ƙarfin tausayi ko karayar zuciyar mutum ta hanyar ba su wani aiki ko kuma amsa wasu tambayoyi.
Kuma nazarin ya nuna cewa yawan tausayin mata ya fi na maza.
Simon Baron-Cohen, wani masanin tunanin ɗan'adam a jami'ar Cambridge ya ce "ita ƙwaƙwalwar mace tun asali an halicce ta ta zama mai tausayi" wannan ne ya sa mata suka fi ƙwarewa wajen raino, amma ita ƙwaƙwalwar namiji an halicce ta ne "ta fahimta tare da tsara abubuwa."

Asalin hoton, Alamy/ Javier Hirschfeld/ BBC
Baron Cohen ya ce yayin da abubuwa na yau da kullum ke shafar ɗabi'ar tausayi, bincikensa ya gano cewa sinadaran halitta da ɗan'adam kan samu tun yana cikin mahaifiyarsa na tasiri sosai kan yadda halayyarsa za ta kasance a cikin al'umma.
Nazarin da ya gudanara shekatrar 2006, wanda ya sama da yara 200 wadanda shekarunsu suka kama daga 6 zuwa 9 ya nuna cewa wasu daga cikin sinadaran jikinsu na tasiri ga ɗabi'unsu.
Yawan sinadarin maza na 'testerone' da ɗan tayi ke samu a cikin mahaifa yana da tasiri sosai wajen tantance tausayinsa da kuma jinsinsa.
Wani nazarin kuma a shearar 2007 ya nuna cewa yawan sinadarin maza na testesterone da ɗan tayi ke samu a cikin mahaifa na haifar da naƙasu ga yanayin tausayinsa.
Baron Cohen ya ce "babban abin da ya fito fili shi ne batun tausayi da nuna fahimtar abubuwa ne masu sarƙaƙiya waɗanda halitta da kuma yanayin rayuwa ke tasiri a kansu."
Shin tausayi a halitta yake?
Wani bincike ya nuna cewa jinsin mutum ba ya da tasiri sosai a ayyukan da ke buƙatar nuna tausayi.
Mata sun fi nuna tausayi a ƙasashe 36 daga cikin ƙasashe 57 da aka yi binciken.
Amma a ƙasashe 21, sakamakon ya zama daidai wa daida, kuma masu binciken sun ce ba su gano mene ne dalilin hakan ba.
Sai dai mata sun fi samun maki mai yawa wajen nuna tausayi fiye da maza.
A shekarar 2018, wani nazari kan ƙwayoyin gado da aka yi wa mutane sama da 46,000, waɗanda suka amsa wasu tambayoyi, sannan suka bayar da ƙwayoyin gwajin halittarsu, gwajin ya nuna cewa ƙwayar halittar gadonsu ba ta taka rawa wajen kasancewarsu masu tausayi ko marasa tausayi ba.
Sai dai wurn da mutum ya girma na taka rawa wajen tausayinsa.
Za mu iya koyon tausayi
Tausayi abu ne da za mu iya koyo, in ji Nathan Spreng, wani masanin aika saƙonnin gangar jiki a jami'ar McGill University da ke Canada.
"Da zarar muka fahimci ɗabi'ar tausayi, za mu iya mayar da hankali sannan mu koyi tausayi daga wasu, sai mu bunƙasa tausayin da muke da shi," kamar yadda Spreng ya shaida wa BBC.

Asalin hoton, Alamy/ Javier Hirschfeld/ BBC
Wani bincike ya gano cewa mata sun fi maza iya gano halin da mutum ke ciki.
Amfani da rashin amfanin tausayi
Ana kallon mata a matsayin wadanda ba su fiye cancanta su mulki maza ba, domin ana kallon masu mulki a matsayin waɗanda ke nuna izza, da tilastawa da tsayawa kan abu, wadanda duk wadannan halayya ne da ake alaƙantawa da maza.
Amma idan mutane suka tsinci kansu cikin kaɗaici, mata sun fi shiga yiwuwar kai kukansu a shafukan sada zumunta fiye da maza.
Kaɗaici wani abu ne da ke ingiza mutum ya kashe kansa, kuma maza na cikin mutanen da suka fi kashe kansu.

Asalin hoton, Alamy/ Javier Hirschfeld/ BBC
Imanin da mutane ke da shi kan muhimmancin gane halin da mutane ke ciki, a tsakanin maza da mata na sauyawa, musamman muhimmancin nuna tausayi ga wasu da raino, in ji Niall Hanlon, masanin halayyar ɗan'adam a jami'ar fasaha ta Dublin da ke Ireland.
To amma yanzu al'umma sun sauya ta yadda maza suka rungumi al'adar raino da kuma nuna tausayi a bayyane.
A yanzu maza na kwashe tsawon lokaci tare da ƴaƴansu fiye da yadda suke yi a baya, duk da cewa mata ne suka fi ɗawainiya wajen kula da yara.











