Abin da Mufti Menk ya cewa Rahama Sadau
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta koka kan salon wasu kamfanonin tsara tafiye-tafiye na ɗaukar bidiyon masu ibadar Umrah da suka je ƙasa mai tsarki ta kamfaninsu a wani ɓangare na tallata kamfanonin nasu.
Rahama Sadau ta bayyana damuwarta ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta ce tana sha’awar zuwa Umra cikin rukunin jama’a amma salon kamfanonin da ke nema zama ruwan dare na matuƙar sanyaya gwiwa.
Ta ce ya kamata Umrah ta kasance ibada maimakon mayar da ita wata dama ta samar da hotuna ko bidiyon da za a wallafa a shafukan sada zumunta.
Saƙon nata ya ja hankalin mutane da dama inda fitaccen malamin addinin Musulunci Mufti Menk, ya yi martani kan saƙon nata inda kuma ya ba ta shawarar kamfanin da za ta iya zuwa umarah ta hannunsu wanda ya ce yana bai wa mahajjata damar gudanar da ibadarsu cikin sirri.
Sai dai y ace a zamanin da ake ciki, mutane da dama kan samu ƙwarin gwiwar zuwa Umrah ne bayan sun ga wasu sun je amma a caerwa shi “abin da ya fi dacewa shi ne kada ɗaukar hotunan ya zama abin da aka fi mayar da hankali a kai.”