Bayern na harin Olmo, Alexander - Arnold ba zai bar Madrid ba

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Bayern Munich na shirin miƙa tayin fam miliyan 69 kan ɗan wasan gaban Barcelona da Spain, Dani Olmo, mai shekara 28. (Sport)

Trent Alexander-Arnold na Real Madrid, mai shekara 27, ba ya tunanin barin ƙungiyar, duk da cewa Arsenal da Liverpool na nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan bayan na Ingila. (TeamTalk)

Manchester United na sa ido kan ɗan wasan bayan na Spain mai taka leda a bangaren hagu, Alejandro Balde, mai shekara 22, wanda ka iya barin Barcelona a watan Janairu. (Mundo Deportivo)

Liverpool da Manchester United duk suna sha'awar ɗan wasan bayan na Netherlands, Micky van de Ven, amma za a buƙaci maƙudan kuɗaɗe kafin a iya ɗaukar ɗan wasan mai shekara 25 daga Tottenham. (Caught Offside)

Ana sa ran ɗan wasan baya Fikayo Tomori, mai shekara 28, da ɗan wasan tsakiya Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 30, za su bar AC Milan a shekara mai zuwa, kasancewar kwangilolin ƴan wasan biyu na ƙasar Ingila za su ƙare a watan Yuni. (Gazzetta)

Bayern Munich na zawarcin ɗan wasan baya na Benfica, Tomas Araujo, ɗan ƙasar Portugal mai shekara 24. (Bild)

Barcelona na ci gaba da sa ido sosai kan ɗan wasan gaba na Norway, Erling Haaland, tare da fatan cewa ɗan wasan mai shekara 26 zai iya zama ɗan wasan da za ta iya ɗauka cikin sauƙi a lokacin bazara, bayan da aka samu Manchester City da laifin karya dokokin kashe kuɗi na gasar Premier League. (El Nacional)

Ana sa ran AS Roma za ta ninka kuɗin da take son sayar da Manu Kone, ɗan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara 25 da Chelsea ke zawarci, zuwa fam miliyan 86 a watan Janairu, bayan da aka ruwaito cewa ƙungiyar ta yammacin Landan ta yi watsi da damar ɗaukar ɗan wasan kan fam miliyan 43 a lokacin bazara. (La Gazzetta dello Sport)

Ɗan wasan baya na Real Madrid ɗan ƙasar Spain Raul Asencio, mai shekara 23, ya samu tayi masu tsoka guda uku a lokacin bazara—ciki har da daga ƙungiyoyin Premier League guda biyu, Chelsea da Liverpool—amma ya zaɓi ci gaba da zama a ƙungiyar ta Madrid. (Marca)

Yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan baya na Spain Alex Jimenez daga Bournemouth zuwa Fiorentina a matsayin aro ta ƙunshi zaɓin da ƙungiyar ta Italiya ke da shi na sayen ɗan wasan mai shekara 21 kan kuɗi £17m. (Tuttomercatoweb)