Arsenal na neman ɓarar da garin Man U kan Jeremy Monga, Liverpool da Chelsea na son Kroupi

Jeremy Monga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jeremy Monga
Lokacin karatu: Minti 2

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United na son kara karfin tsakiyarta a wannan bazarar, inda take sa ido kan dan wasan tsakiya na Manchester United, Manuel Ugarte mai shekara 25, a matsayin babban burinta. (Football Insider)

Tottenham Hotspur da West Ham United duk suna sha'awar daukar dan wasan tsakiya na Barcelona, Marc Casado mai shekara 22. (Tuttomercato)

Liverpool da Chelsea na shirin fafatawa wajen sayen dan wasan gaba na Bournemouth mai shekara 19, Eli Junior Kroupi, yayin da kungiyar ke shirin amincewa da tayin da zai kai kusan fam miliyan 60. (Caught Offside)

Coventry City na son mayar da aron mai tsaron ragar Brighton, Carl Rushworth mai shekara 24, ya zama na dindindin a bazara, amma za su fuskanci gogayya daga Leeds United. (Teamtalk)

Dan wasan gaba na Leeds United, Joel Piroe mai shekara 26, na iya barin kungiyar a wannan bazarar sakamakon rashin samun damar taka leda, inda ake ganin Rangers na iya zama sabuwar kungiyarsa. (Football Insider)

Manchester United na shirin daukar matashin dan wasan gefe na Leicester City mai shekara 16, Jeremy Monga, a wani mataki mai ba wa mutane mamaki, yayin da Manchester City da Arsenal ma ke sha'awar dan wasan. (Teamtalk)

Fulham na duba yiwuwar kulla yarjejeniya da dan wasan tsakiya na Bayer Leverkusen, Malik Tillman mai shekara 23, yayin da suke shirin rayuwa ba tare da Harry Wilson ba, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara. (Daily Mail)