Jam'iyyun adawa a India sun zargi hukumar zaɓen da yunƙurin taimakon jam'iyya mai mulki
Hukumar zaɓen ƙasar Indiya ta bayar da umarnin a sake duba manhajar da ke kula da rajistar masu kaɗa ƙuri'a a ƙasar, bayan rahotannin da ke cewa an cire miliyoyin masu kaɗa ƙuri'a daga jerin sunayen da aka sabunta.
Jam'iyyun adawa na zargin cewa an yi wa jerin sunayen kwaskwarima ne domin a taimakawa jam'iyyar BJP ta Firaminista Narendra Modi.
Wakilin BBC ya ce hukumar zaɓen ta musanta zargin, tare da jaddada cewa ta bi doka wurin aiwatar da dukkan ayyukanta.
Jami'an zaɓe sun bayyana cewa wani kwamiti, wanda ya ƙunshi ƙwararre mai zaman kansa a fannin fasaha, zai tantance ko an bi dokoki da ƙa'idojin zabe.
Jam'iyyun adawa, ciki har da jam'iyyar 'Cockroach Janta Party' da matasa ke jagoranta, sun buƙaci shugaban hukumar zaɓen, Gyanesh Kumar ya yi murabus.