Yadda ƴan Najeriya suka fi ƴan kowace ƙasa ta duniya yin sadaka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mamadou Faye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Rahoton wani nazari da gidauniyar bayar da sadaka ta Charity Aid Foundation ta fitar kan ƙasashen duniya da suka fi yin kyauta a shekara ta 2025, ya nuna cewa 6 daga cikin ƙasashe 10 da suka fi bayar da sadaka a duniya daga nahiyar Afirka suke.
Rahoton ya ce mutane a nahiyar Afirka na bayar da sadakar gwargwadon kashi 1.6% na abin da suke samu, yayin da a nahiyar Turai mutane ke bayar da kashi 0.6% na abin da suke samu a matsayin sadaka.
An gudanar da nazarin ne kan sama da mutum 500,000 a ƙasashe 101 na duniya.
Rahoton ya ce yanzu ana tantance girmar sadaka ne ba ta hanyar yawan mutanen da ke bayar da sadaka a ƙasa kawai ba, amma ana la'akari ne da yawan kuɗin da mutum ke bayarwa sadaka idan aka kwatanta da abin da yake samu, wanda ya bayar ga mabuƙata ko kuma domin ayyukan addini.
Ga ƙasashe 10 da suka fi bayar da sadaka da kuma dalilan da suka sanya suke a kan gaba.
1. Najeriya: 2.83%

Asalin hoton, Getty Images
Kashi 89% na ƴan Najeriya ne suka bayar da sadaka a shekarar 2024 - wanda wannan ne mafi yawa tsakanin ƙasashe 101 da aka yi nazari - wanda hakan ya sanya Najeriya ta zamo ta ɗaya a duniya cikin ƙasashen da mutanensu suka fi bayar da sadaka.
Nazarin ya kuma ce ƴan Najeriya na sadaukar da gwargwadon awa 13.5 wajen yin aikin hidimta wa al'umma a shekara, wanda hakan ya zarce gwargwadon yadda mutanen wasu ƙasashen ke sadaukar da lokutansu, gwargwadon awa 9.
Rahoton ya alaƙanta wannan sadaukarwa ta ƴan Najeriya ga tanade-tanaden addini, inda yan Najeriya masu ibada ke bayar da baiko a majami'u, sannan Musulmai ke bayar da zakka, wanda hakan ya zama wani ɓangare na rayuwarsu.
Sai dai ƴan Najeriya da dama na ganin cewa za su iya zuwa a matsayi na 22 cikin jerin ƙasashen da mutanensu suka fi bayar da sadaka, wanda hakan ke nuna yadda ɗabi'ar bayar da sadaka ta zamo jiki a gare su.
2. Masar: 2.45%
Masar ce ƙasa ta biyu a duniya wajen bayar da sadaka, sanadiyyar yadda mutanenta suka aminta da ƙungiyoyin bayar da taimako.
Ƙarfin amincin da al'umma ke da shi da irin waɗannan ƙungiyoyi ne ya sanya mutane ke yawan ba da gudumawa, wani abu da ke da matuƙar tasiri a ƙasashe da dama da aka yi nazari a kai.
3. Ghana: 2.19%
Ghana da China ne a matsayi na uku.
Ghana na cikin ƙasashen da al'ummarta suka fi bayar da taimako a Afirka, musamman kai-tsaye ga mabuƙata da kuma domin ayyukan addini.
3. China: 2.19%

Asalin hoton, Getty Images
Ita ce wata ƙasa da ba ta Afirka ba da take cikin ƙasashen da suka fi bayar da tallafi a duniya.
Hakan ya nuna cewa ba ƙasashe marasa ƙarfi ne kawai ba ake da yawan masu bayar da taimako ba.
Sai dai rahoton ya ce mutane a ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na bayar da taimako, amma idan aka yi la'akari da abin da suke bayarwa gwargwadon abin da suke samu, hakan ya yi ƙasa da abin da mutane a ƙasashe masu raunin tattalin arziki ke bayarwa.
5. Kenya : 2.13 %
Kenya ta yi fice da daɗaɗɗiyar al'adarta ta taimaka wa juna a tsakanin al'umma: kashi 86% na al'ummar ƙasar na bayar da gudunmawa domin ayyuka daban-daban.
Haka nan kimanin rabin al'ummar ƙasar sun gudanar da ayyukan hidimar al'umma.
Ƙasar ta fito da dabi'ar da aka gani tsakanin mutanen yankin: inda kowa ke jin cewa al'ummarsa sun damu da damuwarsa, wanda rahoton ya alaƙanta hakan kai-tsaye ga yawan bayar da taimako.
6. Uganda : 2.04 %

Asalin hoton, Getty Images
Kasancewar Uganda a wannan matsayi ya tabbatar da yawan ƙasashen gabacin Afirka a wannan jadawali. Idan aka lura da ƙasashe irin su Kenya da Tanzania, wadanda bayar da taimako ta zama ɗabi'ar al'ummar ƙasashen.
Rahoton Charities Aid Foundation ya nuna cewa al'ummar ƙasar na bayar da gwargwadon kashi 1.7% na abin da suke samu, akasin kashi 0.6% a ƙasashen da ba su cika bayar da sadaka ba.
7. Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa: 1.92%
Ƙasashe uku ne suke a matsayi na bakwai.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na daga cikin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi da al'ummarsu suke bayar da taimako kamar yadda al'ummun ƙasashe marasa ƙarfi ke bayarwa.
Rahoton ya bayyana cewa gwamnati ta taka rawa ta musamman a wannan bangare.
Kimanin mutum 9 cikin 10 a ƙasar sun yi amannar cewa gwamnati ta taka rawa wajen yadda al'umma ke bayar da taimako.
7. Qatar: 1.92%
Kamar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, rahoton Qatar ya nuna yadda duk da cewa ƙasar na da ƙarfin tattalin arziki amma kuma al'ummarta na bayar da kyauta sosai.
Mutane sun yarda da ƙungiyoyi masu tara gudunmawa da kyautuka, wani abu da ya zama ruwan dare a ƙasashen yankin Gulf.
7. India: 1.92%

Asalin hoton, Getty Images
Indiya ce ƙasa ɗaya tilo daga yankin Kudancin nahiyar Asia da ta samu shiga cikin ƙasashe 10 na farko a cikin rahoton.
Hakan ya tabbatar da kyakkyawar rawar da ƙasashen nahiyar Asia suka taka a wannan fanni, inda gwargwadon kyautar da suke bayarwa ya kai kashi 1.28% na abin da suke samu, wanda hakan ya zarce gwargwadon yadda mutanen sauran ƙasashen duniya ke bayar da tallafi na kashi 1.4%.
10. Malawi: 1.80%
Malawi ce ta cike matsayi na 10, kuma hakan ya tabbatar da ƙarfin nahiyar Afirka a wannan ɓangare.
Duk da cewa al'ummar ƙasar na daga cikin mafiya ƙarancin samun kuɗaɗen shiga, al'ummar tata na ware kaso mafi tsoka da suke yin sadaka da shi fiye da mazauna ƙasashe masu ƙarfin arziki.
Me ya sa ƙasashen Afirka suka mamaye jerin?

Asalin hoton, Getty Images
Rahoton ya bayyana dalilai da dama da suka sanya ƙasashen Afirka suka nuna bajinta a wannan ɓangare:
Haɗin kan al'umma: A ƙasashen da fiye da kashi 80% na mutane suka ce al'ummar da suke ciki ta damu da damuwarsu, gwargwadon taimakon da mutane ke bayarwa ya kai kashi 1.7% na abin da suke samu.
Yarda da ƙungiyoyin al'umma: Kashi 75% na mutanen Afirka sun amince da cewa ƙungiyoyin al'umma na yin kyakkyawan tasiri a tsakaninsu, wanda hakan ne maki mafi yawa idan aka hada da sauran ƙasashen duniya.
Yarda da gwamnati: Kashi 51% na mutanen Afirka sun amince da cewa gwamnatocin ƙasashensu na ƙarfafa musu gwiwa wajen bayar da tallafi, wanda hakan ya zarta na sauran ƙasashen duniya da ake da kashi 40%.
Bayar da sadaka da kuma ayyukan addini: A ƙasashen Afirka yawancin tallafin da mutane ke bayarwa suna bayarwa ne kai-tsaye ga masu buƙata ko kuma ta hanyar bayar da gudumawa a ayyukan addini.











