Yadda wani likita ya riƙa kashe marassa lafiya a Jamus

Asalin hoton, Getty Images
An yanke wa wani likitan kula da marasa lafiya masu fama da cututtukan da ba sa warkewa daga Jamus hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifin kashe marasa lafiya 15.
Wata kotu a Berlin, babban birnin kasar ta samu mutumin mai shekara 41, wanda aka bayyana sunansa da Johannes M. kawai bisa dokokin kare bayanan sirri na Jamus, da laifin kashe mata 12 da maza uku tsakanin watan Satumban 2021 da Yulin 2024.
A halin yanzu masu gabatar da kara na binciken wasu daruruwan zarge-zarge da ke da alaka da likitan, lamarin da zai iya zama daya daga cikin manyan shari'un kisan gilla a tarihin Jamus.
Mahukunta a kasar na zargin cewa kisan da aka tabbatar da su ka iya zama kadan ne daga cikin laifukan da likitan ya aikata, domin a yanzu masu gabatar da kara na binciken wasu karin al'amura da dama da suka shafe shi.
Mutanen da aka kashe din na da shekaru tsakanin 25 zuwa 94. Kotun ta ji yadda dukkansu ke fama da matsananciyar rashin lafiya, amma kuma mutuwarsu ba ta zo nan take ba.
Masu gabatar da kara sun ce likitan kan ziyarci marasa lafiya a gidajensu, inda yake ba su hadin wasu magunguna masu haddasa mutuwa ba tare da amincewarsu ba.
Sun kuma ce a wasu lokuta ya kan banka wa gidaje wuta domin boye shaidun laifinsa.
A watan Yulin 2024, kwanaki kadan kafin kama shi, masu gabatar da kara sun ce likitan ya kashe marasa lafiya biyu a rana guda: wani mutum mai shekaru 75 a gidansa da ke tsakiyar Berlin, sannan bayan wasu sa'o'i kadan ya kashe wata mata mai shekaru 76 a wata unguwa da ke makwabtaka.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sun ce ya yi kokarin kona gidan matar domin boye laifin, amma bai yi nasara ba.
A mafi yawancin zaman shari'ar, wadda ta shafe kusan shekara guda ana yi, likitan bai ce komai ba. Sai dai a watan da ya gabata ya amsa cewa ya kashe mutane, ciki har da marasa lafiya 12 da ke fama da matsananciyar rashin lafiya.
Ya shaida wa kotu cewa ya gamsar da kansa cewa abin da yake yi daidai ne, yana mai cewa yana kubutar da su daga wahala da kuma nakasa.
Ya ce, "A duk tsawon wannan lokaci, na yi tunanin cewa wannan shi ne mafi alheri ga kowa."
Haka kuma ya nemi afuwa kan radadin da ya jawo wa iyalai da sauran jama'a.
Sai dai hukumomi na zargin cewa ya kashe wasu karin mutane. Masu gabatar da kara na ci gaba da binciken wasu karin shari'u 76 da ake dangantawa da shi.
Kafafen yada labarai na Jamus sun ce idan aka tabbatar da wadannan karin zarge-zargen kuma aka same shi da laifi, lamarin zai kasance daya daga cikin manyan shari'un kisan gilla a tarihin kasar.
Likitan ya shaida wa kotun cewa zai ba da cikakken hadin kai a shari'un da za a ci gaba da yi nan gaba.
Tun a farkon shari'ar, wasu daga cikin dangin wadanda suka mutu sun shaida wa kotu cewa har yanzu ba su iya gaskata abin da ya faru ba.
Mahaifiyar mafi karancin shekaru cikin wadanda abin ya shafa, wata mata mai shekara 25 da ta mutu a shekarar 2021, ta fashe da kuka yayin zaman kotu.
Ta ce, "Ba ta taba cewa ta gaji da rayuwa ko kuma ba ta son ci gaba da rayuwa ba."
Shi ma dan wata mata mai shekara 72 da ta mutu a shekarar 2024 ya ce mahaifiyarsa na da shirye-shiryen zuwa gabar tekun Baltic tare da 'yar uwarta.
Ya ce, "Mahaifiyata tana son ci gaba da rayuwa."
Kotun ta yanke cewa laifin da likitan ya aikata yana da matukar muni. Saboda haka ta ba da umarnin a tsare shi karkashin kulawa ta musamman bayan ya kammala zaman gidan yari.
Haka kuma kotun ta haramta masa yin likitanci har abada.










