Me yarjejeniyar zaman lafiya da jam'iyyu suka sanya wa hannu ta ƙunsa?

mahalarta taron sanya hannu

Asalin hoton, Prof. Nentawe/X

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Talatya ne manyan jam'iyyun siyasa da ƴan takararsu suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya (Peace Accord) a Abuja, inda suka yi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓen cikin lumana da mutunta dokokin zaɓe.

Taron sanya hannu kan yarjejeniyar, wanda Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya shirya, ya samu halartar wakilan gwamnati da shugabannin jam'iyyun siyasa da ƴan takarar shugaban ƙasa da shugaban hukumar zaɓe ta INEC da jami'an tsaro da kuma jakadun ƙasashen waje.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, yayin da ƴan takara irin su Peter Obi da Omoyele Sowore suka halarta tare da sanya hannu a yarjejeniyar.

To ko me yarjejeniyar ta ƙunsa, kuma ta yaya za ta taimaka don tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana? Waɗannan ne tambayoyin da mutane da dama ke yi game da batun.

BBC ta samu ganin yarjejeniyar, ga kuma wasu daga cikin abubuwan da ta ƙunsa.

Yin yaƙin neman zaɓe cikin lumana

Yarjejeniyar ta yi tanadin gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana, bisa doka da kuma mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi jama'a.

''Za a yi hakan ne ta hanyar kauce wa duk wani abu da zai rage ƙimar siyasar ƙasarmu'', a cewar yarjejeniyar.

Peter Obi

Asalin hoton, Peter Obi/X

Kauce wa yaɗa labaran ƙarya

Yarjejeniyar ta kuma yi alƙawarin tabbatar da cewa masu magana da yawun jam'iyyun da jami'an yaƙin neman zaɓe da magoya bayansu ba za su ƙirƙira da wallafa ko yaɗawa ko goyon bayan labaran ƙarya.

Haka kuma a kauce wa bayanan da ke yaudarar jama'a ba, musamman waɗanda za su iya tunzura tashin hankali ko kuma su lalata sahihancin tsarin zaɓe.

Kare mata da masu rauni

Yarjejeniyar ta kuma tanadi cewa masu dole ne masu yaƙin neman zaɓe da magoya bayan jam'iyyu su kare mata, matasa da masu bukata ta musamman daga cin zarafi da tsoratarwa da musgunawa da tashin hankali.

''A kuma kauce wa wariya da sauran nau'o'in cin mutunci, tare da ɗaukar matakan da za su tabbatar da sun samu damar shiga harkokin zaɓe cikin aminci da adalci'', in ji shi.

Aiki da INEC da hukumar tsaro

Peter Obi

Asalin hoton, Peter Obi/X

Yarjejniyar ta amince da yin cikakken aiki da dukkan hukumomin da kundin tsarin mulki da doka suka ɗora wa alhakin gudanarwa da kula da kuma tsaron zaɓe, musamman Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro.

Girmama juna

Prof. Nentawe da Akume

Asalin hoton, Prof. Nentawe/X

Yarjejeniyar ta kuma yi alƙawarin amfani da dabarun sadarwa na siyasa da suka ginu kan zaman lafiya da girmama juna, haɗa kowa da kowa, ilimantarwa da kuma tattauna muhimman batutuwa.

Haka kuma sun yi alƙawarin guje wa cin mutunci da ɓata suna da yin kalaman tunzura jama'a, kalaman ƙiyayya da duk wata magana da za ta iya haddasa wariya da gaba ko tashin hankali.

Aiki da kwamitin zaman lafiya

Yarjejeniyar ta yi tanadin cewa masu sanya hannu za su yi aiki tare da Kwamitin Zaman Lafiyar domin sa ido kan yadda ake aiki da yarjejeniyar.

Sannan ta yi tanadin cewa dole ne masu sanya hannun su taimaka wajen sasanta duk wani rikici da ka iya tasowa sakamakon rashin bin ƙa'idojinta.

Mutunta kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe

Peter Obi

Asalin hoton, Peter Obi/X

Masu sanya hannun sun kuma yi alƙawarin mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya da Dokar Zaɓe ta 2026 da sauran dokokin da suka shafi mutunta ƴancin ɗan'adam da dimokraɗiyya.

Sun kuma amince da kauce wa duk wani aiki ko sakaci da zai iya kawo cikas ga sahihancin tsarin zaɓe da miƙa mulki cikin lumana ko kuma ƴancin masu zaɓe na bayyana ra'ayinsu.