KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 19 ga watan Agusta, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello, Haruna Kakangi

  1. Iran ta musanta harba wa Daular Larabawa makamai

    Mojtaba Khamenei

    Asalin hoton, TASNIM

    Bayanan hoto, Jagoran addini na Iran Mojtaba Khamenei

    Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Iran ya musanta zargin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi na cewa Iran ɗin ta harba mata makamai masu linzami.

    Ismael Beqai ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa “zargin na UAE ba shi da tushe balle makama”.

    Mai Magana da yawun na Iran ya ce: “Matakin na Háɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya saɓa da tsarin zama na maƙwaftaka kuma hakan zai iya yin cikas ga yunƙurin da ake yi na yayyafa wutar rikici tsakanin ƙasashen yankin.”

    Sa’o’i bayan Iran ta sanar da cewa ta harba makamai ne ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce ta dakatar da duk wata alaƙa ta kasuwanci ko kuɗi da Iran har sai abin da hali ya yi.

    Tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Iran da Amurka, Daular Larabawa ta kasance ƙasar da ta fi shan hare-hare daga Iran a yankin.

  2. Ruftawar mahaƙar ma'adanai ta kashe mutum 107 a Kamaru

    Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya

    Aƙalla mutum 107 sun mutu sanadiyyar ruftawar ramin haƙar ma'adanai a ƙauyen Zamboi da ke kan iyakar Kamaru da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kamar yadda wani jami'i a yankin ya bayyana wa BBC.

    Adamou Abdon, wanda shi ne magajin garin Garoua-Boulai a yankin gabashin Kamaru ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

    "An zaƙulo gawarwaki 107 daga cikin ƙasa," kamar yadda ya shaida wa BBC, inda ya ƙara da cewa lamarin "ya faru ne a wani wurin haƙar ma'adanai da ke bangaren Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kusa da kan iyaka da ƙasar Kamaru."

    Har yanzu babu tabbas kan abin da ya haddasa ruftawar ƙasar. Bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ƙasa ta rufta kan masu haƙar zinare da ke a mahaƙar.

    Ana ƙoƙarin gudanar da aikin ceto a yankin sannan ana fargabar cewa yawan waɗanda suka mutu zai ƙaru.

    Haƙar ma'adanai ɗaya ne daga cikin manyan hanyoyin dogaro na mutanen gabashin Kamaru.

    Sai dai babu yanayi mai kyau a wuraren haƙar ma'adanan, inda a mafi yawan lokuta masu aikin kan fada cikin haɗarin kamuwa da cutuka ko kuma bala'o'i.

    Haka nan kuma ruftawar wuraren haƙar ma'adanai abu ne da ya yawaita a ƙasar.

  3. Tsohon ministan tsaron Ukraine na son a yi sabon zaɓe a ƙasar

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, na fuskantar ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen siyasa ga ikonsa tun bayan fara mamayar da Rasha ta kai wa ƙasar, bayan da tsohon ministan tsaronsa ya yi kira da a gudanar da zaɓe.

    Mykhailo Fedorov, wanda aka kora daga muƙaminsa a watan da ya gabata lamarin da ya haifar da zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar, ya ce bai kamata dimokuraɗiyya ta zama abin da Rasha za ta iya dakatarwa ba.

    Sai dai dokar ta-ɓaci da ake aiwatarwa a Ukraine tun bayan fara yaƙi har yanzu ta haramta gudanar da zaɓe a lokacin da ake fama da yaƙi.

    Har zuwa yanzu, Shugaba Zelensky bai mayar da martani a hukumance kan kiran da Fedorov ya yi ba. A gefe guda kuma, sojojin Ukraine na ci gaba da kai hare-hare a cikin yankunan Rasha.

    Gwamnan yankin Bashkortostan na Rasha, Radiy Khabirov, ya ce wasu jiragen sama marasa matuƙa na Ukraine sun haddasa gobara a wani wurin masana'antu da ke yankin.

  4. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku daga yanzu zuwa ƙarfe 4 na yamma in sha Allah.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.