Yadda masu zanga-zanga suka cinna wa asibitin masu Ebola wuta a Congo

Fire and smoke at the of burnt tents on the grounds of Rwampara General Hospital. A police officer with a gun can be seen to the right of the shot in front of other makeshift tents.

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Emery Makumeno
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Kinshasa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wasu fusatattun gungun mutane sun cinna wuta a wasu sassan asibitin da ake kwantar da masu cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, bayan da aka hana ƴan'uwan wani matashi aka ce ya mutu sakamakon kamuwa da cutar ɗaukar gawarsa domin yi masa jana'iza.

"Sun fara jefa wasu abubuwan fashewa a asibitin. Sun kuma cinna wa tantunan da ake killace masu cutar wuta," in ji wani ɗansiyasa a yankin Luc Malembe Malembe, inda ya shaida wa BBC abin da ya gani a asibitin.

A yayin hatsaniyar, ƴansanda sun yi harbin gargaɗi domin tarwatsa mutanen.

Gawar mutumin da ya kamu da cutar Ebola na iya yaɗa ta, shi ya sa hukumomi ke ƙoƙarin ganin an binne ta cikin taka tsan-tsan domin daƙile yaɗuwarta.

An killace duk ma'aikatan lafiyar asibitin Rwampara da ke kusa da birnin Bunia da ke Ituri ƙarƙashin kulawar sojoji, inda aka fi samun masu kamuwa da cutar, yayin da ƴansanda ke ƙoƙarin daidaita lamura a yankin.

Wani jami'in lafiya ya ji rauni a yayin da masu zanga-zangar suka jefa duwatsu a asibitin, kafin jami'ai su isa wurin, kamar yadda wani ma'aikacin asibitin ya shaida wa APF

Jami'in da ke kula da agajin gaggawa kan masu Ebola a yankin Ituri, Jean Claude Mukendi, ya shaida wa AP cewa mutumin ya rasu sananne ne a yankin kuma waɗanda suka fusata da mutuwar tasa ba su san illar cutar ba ne.

Wasu ganau sun shaida wa Reuters cewa matashin fitaccen ɗanwasan ƙwallon kafa ne da yake buga wasa ƙungiyoyi da dama. Mahaifiyarsa ta shaida wa kamfanin dillancin labaran cewa ta yi amanna cewa ɗanta ya rasu ne sakamakon cutar typhoid ba Ebola ba.

Malembe ya ce masu zanga-zangar ba su yarda cutar Ebola gaskiya ba ce, duk da ta kashe sama da mutum 130 a gabashin DR Congo.

Mutane ba su da masaniya kuma ba a wayar musu da kai kan abin da ke faruwa ba. Musamman a yankunan karkara, wasu sun yi amanna cewa shigo da cutar aka yi," in ji ɗansiyasar.

"A ganinsu ƙungiyoyi da asibitoci ne suka ƙirƙiri cutar domin samun kuɗi, wannan kuma abin tayar da hankali ne."

Ya ce an ƙona wasu tantuna da wata gawa da ake shirin binne ta.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da shawarar yin jana'izar mutanen da suka kamu da Ebola cikin kulawa, tare da sa ido daga ƙwararru da za su ba da kariya.

Marasa lafiya shida ne ke samun kulawa a tantunan da ke asibitin, inda suka gudu domin neman mafaka.

Sai dai ƙungiyar ba da agaji ta Alima da ke kula da tantunan ta ce ana kula da su yanzu haka a asibitin.

Medical staff climb aboard a military vehicle on the grounds of Rwampara General Hospital. One soldier pictured in camouflage has a large machine gun.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sojoji ne ke kula da ma'aikatan lafiyar
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Zanga-zangar na zuwa a daidai lokacin da aka sanar da cewa ƙungiyar ƙwallon kafa ta DR Congo ta soke atisayen da take yi na tunkarar gasar cin kofin duniya a Kinshasa babban birnin ƙasar saboda ɓarkewar cutar.

WHO ta bayyana ta a matsayin "barazanar lafiya da ke buƙatar kulawar gaggawa a duniya", amma ta ce ba ta kai matakin da za a kira ta da annoba ba.

A ranar Laraba, WHO ta ce ana hasashen mutum 139 a DR Congo sun mutu sakamakon cutar Ebola, daga cikin 600 da ake zargi sun kamu da ita.

Sai dai a wannan rana, ministan lafiya na Congo Samuel Roger Kamba ya shaidawa gidan talabijin na RTNC cewa hukumomi sun yi samu rahoton mutuwar mutane 159.

An kuma gano wasu mutane biyu da suka kamu da cutar a makwabciyar ƙasar, Uganda.

Hukumomin sun dakatar da zirga-zirgar jirage da bas-bas da duk wasu zirga-zirgar jama'a na wani ɗan lokaci sakamakon barkewar cutar. Haka kuma ba a ba da izinin zirga-zirga a kogin Semliki ba, wanda ke kan iyaka tsakanin DR Congo da Uganda.

An samu ɓarkewar cutar ne sakamakon ɓullar wani nau'in cutar Ebola da ba kasafai ba da aka fi sani da ake kira Bundibugyo. A halin yanzu babu wata allurar rigakafi ga wannan nau'in, kuma WHO ta ce zai iya ɗaukar watanni tara kafin a samu.

A jiya Alhamis ƙungiyar ƴan tawayen M23 da ke iko da wasu sassan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ta ce ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a karon farko a kudancin lardin Kivu, wanda ke da nisan daruruwan kilomita daga yankin Ituri.

Matashin mai shekaru 28, wanda ya taso daga yankin Kisangani, ya mutu ne kafin a tabbatar da cutar, a cewar wata sanarwar ƴan tawayen suka fitar.

Kisangani babban birni ne da ke arewa ta tsakiyar lardin Tsopo inda a halin yanzu ba a samu rahoton ɓullar cutar Ebola ba.

Ana kara shiga damuwa game da rashin samun damar shiga yankunan da ke karkashin ikon M23.

Kungiyar ba ta taɓa aikin daƙile cuta irin Ebola ba, amma ta ce za ta yi aiki da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin daƙile yaɗuwar cutar.