Chelsea na son Scott, Marseille za ta hana Arsenal Paixao

    • Marubuci, Muhammad Annur Muhammad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea na shirin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Bournemouth, Alex Scott mai shekara 23, a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasan Argentina Enzo Fernandez mai shekara 25 idan ya koma Manchester City. (The Sun)

Al-Hilal ta cimma yarjejeniya da Aston Villa kan sayen ɗan wasan gaba na Ingila Ollie Watkins mai shekara 30 kan kuɗin da ya kai kusan fam miliyan 50. (Fabrizio Romano)

Ana sa ran ɗan wasan gefe na Portugal Rafael Leao mai shekara 27 zai bar AC Milan, inda Galatasaray ke dab da kulla yarjejeniyar sayensa kan kusan fam miliyan 38. Leao dai na cikin 'yan wasan da Aston Villa ke sha'awa. (Corriere dello Sport)

Sunderland ta miƙa wa Manchester City tayi domin aron ɗan wasan gefe na Ingila Jack Grealish mai shekara 30. (The Athletic)

Chelsea na dab da kammala sayen matashin ɗan bayan Italiya Honest Ahanor mai shekara 18 daga Atalanta kan fam miliyan 36. (Sky Sport Italy)

Ɗan bayan hagu na Barcelona da Sifaniya, Alejandro Balde mai shekara 22, na ci gaba da kasancewa cikin jerin 'yan wasan da Manchester United ke son ɗauka domin ƙarfafa bayanta. (Fichajes)

Newcastle United ba ta janye daga zawarcin ɗan wasan gefe na Belgium Matias Fernandez-Pardo mai shekara 21 na Lille ba, amma ba ta son karya ƙa'idojin kashe kuɗi na Firemiya da UEFA. (Daily Mail)

Lille na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba na Faransa Martin Terrier mai shekara 29 daga Bayer Leverkusen a matsayin wanda zai maye gurbin Fernandez-Pardo idan ya tashi. (L'Equipe)

Fiorentina ta yi watsi da tayin farko na fam miliyan shida da Nottingham Forest ta yi domin sayen ɗan bayanta na Brazil Dodo mai shekara 27. (Sky Sport Italy)

Marseille na da kwarin gwiwar cewa za ta iya ci gaba da riƙe ɗan wasan gabanta na Brazil Igor Paixao mai shekara 26 duk da sha'awar da Arsenal da Sunderland ke nuna masa. (Teamtalk)

Aston Villa ta nemi bayani kan yiwuwar sayen ɗan bayan Faransa Jean-Clair Todibo mai shekara 26 daga West Ham, yayin da take neman sabon ɗan bayan tsakiya. (Daily Mail)

Ɗan wasan tsakiyar Argentina Exequiel Palacios mai shekara 27 na Bayer Leverkusen na dab da kammala komawa Ipswich Town kan kuɗin da ya kai fam miliyan 23.5. (Sky Sports)

Everton na shirin sayen ɗan wasan gaba na Guinea-Bissau Franculino mai shekara 22 daga Midtjylland, sannan kuma a shirye take ta saurari tayin sayen ɗan bayanta na Jamhuriyar Ireland Jake O'Brien mai shekara 25. (Teamtalk)