Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko matsin lambar Trump zai yi tasiri kan Iran a wannan karo?
- Marubuci, Amir Azimi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian editor
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Amurka ta ce ta kaddamar da “gagarumin hari kan tattalin arziki da hanyoyin hada-hadar kudin Iran a fadin duniya”. Sakataren baitul-malin Amurka Scott Bessent ya ce takunkumin na Amurka sun shafi bangaren arzikin Iran na intanet da kere-kere da zinare da sufurin jiragen sama da kuma na ruwa. Ya ce duk wata kasa da ta yi hukda da Iran ita ma za a mayar da ita saniyar ware.
Sai dai sanarwar da Bessent ya bayar da alama ta fi zafi a Amurka idan aka kwatanta da yadda Iran ta dauke shi.
Jim kadan bayan sanarwar, ministan tattalin arziki na Iran Ali Madanizadeh ya bayyana lamarin a matsayin “abin da aka saba ji” sannan ya ce Iran a shirye take kan “ko mene ne zai faru”. Ya ce tuntuni Iran ta yi tsammanin za a kai ga hakan kuma ta shirya yadda za ta magance lamarin.
Martanin da ya mayar na nuni zuwa ga babbar tambayar da shugabannin Iran za su rika yi: Me Amurka za ta yi a yanzu wanda ba ta riga ta yi ba a baya?
Bessent ya yi barazanar kakaba takunkumi kan wasu kasashen da bankuna da kamfanonin da suka ci gaba da yin mu’amala da Iran. To amma tushen tsarin ba sabon abu ba ne.
Iran ta dade tana fuskantar takunkuman Amurka na tsawon shekaru, har da tarar da ake yi wa kamfanonin kasashen waje da ke hulda da ita.
Abin da zai damu Iran kawai shi ne idan Amurka za ta iya tilasta wa kasashe aiwatar da takunkumin fiye da na baya.
Toshe tashoshin ruwan Iran da Amurka ta yi ya yi tasiri, akalla ya rage yawan danyen man fetur din da Iran ke iya fitarwa idan aka kwatanta da baya kuma hakan ya kara wa Iran shan wahala wajen shigo da kaya daga waje.
Iran na da iyakoki ta kasa masu tsawo da kasashe bakwai kuma tana da kwarewa a tsawon shekaru wajen yin amfani da su tana tsallake takunkumai.
Sai dai hanyoyin kasa ba za su iya zama makwafin hanyoyin kasuwanci ta ruwa cikin sauki ba, musamman wajen fitar da danyen mai.
Saboda haka matsin zai iya yin illa sosai idan Amurka ta samu nasarar datse hanyoyin sufuri ta ruwa wadanda takunkuman baya ba su shafa ba, musamman wadanda suka shafi China da kuma makwaftan Iran.
Sai dai akwai babbar ayar tambaya a nan.
A ranar Talata ma’aikatar harkokin wajen China ta ce tana matukar adawa da takunkuman, inda ta bayyana su a matsayin haramtattu.
Idan takunkuman suka gaza, barazanar da Bessent ya yi za ta karfafa tasirin Iraniyawa wadanda suke adawa da cimma yarjejeniya da Amurka.
Za su iya cewa Amurka ta koma matsa lamba ta fannin tattalin arziki ne saboda ba ta da isassun zabi. Fara sabon yaki na da nasa hadurran, yayin da kuma shekarun da aka kwashe ana kakaba takunkumai sun gaza tursasa Iran ta amince da bukatun Amurka.
Haka nan Amurka ta lalata hanyoyi da dama na diflomasiyya.
Duk da cewa Pakistan da sauran kasashe masu shiga tsakani na ta kokarin farfado da batun tattaunawa, Amurka ba ta kawar da yiwuwar sake komawa kai hare-hare ba. Sabbin barazanar za su iya kashe kwarin gwiwar jami’an Iran masu ra’ayin cimma yarjejeniya.
Kasar na cikin tsaka mai wiya tun kafin yakin, inda ake fama da tashin farashin kaya da kuma zubewar darajar kudi, ka darajar ta ci gaba da zubewa a tun bayan fara yakin a ranar 28 ga watan Fabarairu.
Durkushewar darajar kudin Iran, Riyal, ta shafi bangarori da dama. Shigar da kaya kasar ta kara tsada, sana’o’i sun shiga garari sannan darajar kudin da mutane ke tsimi ta zube. Haka nan tarnakin da gwamnati ta samu wajen sayar da danyen man fetur ya sa tana fama da karancin kudin ketare.
Negin - wadda ba sunanta na asali kenan ba - mai shekara 34, ta ce albashinta bai fi dala 100 a yanzu. Ta shaida wa BBC cewa: “Ba na iya zuwa silima kon wurin kallon masu nishadantarwa. Ban iya sayen kyaututtuka wa ‘yan’uwa ko abokai kuma ba na iya zuwa bukukuwa. Abin da kawai zan iya yi shi ne sayen nama, shi ma sai da katin tallafi na gwamnati, in ba haka ba shi ma naman ba zan iya saye ba.
Mona, wata mata mai ‘ya’ya biyu ta ce mijinta ya rasa aikinsa tun bayan fara yaki. Ta kara da cewa: “Muna cikin fargaba musamman bayan fara aikin takunkumai a jiya. Tun bayan fara yaki maigidana bai sake samun aiki ba. A baya yana aiki me cikin jiragen ruwa.”
Ta kara da cewa: “Muna bakin kokarinmu wajen tsuke bakin aljihu, amma tabbas dole ta sa mun daina sayen duk wani abu da bai zama wajibi ba ko kuma wani abu na jin dadi.”
Sai dai akwai yiwuwar gwamnatin Iran za ta yi tunanin cewa ci gaba da tsawaita yakin zai jefa shugaba Trump cikin matsi. Tsananta datse Mashigar Hormuz zai iya ingiza tashin farashin danyen mai, ya kara tashin farashin kaya a Amurka sannan ya zamo wa Trump matsala a siyasance gabanin zaben rabin wa’adi da za a yi a watan Nuwamba.
Tattalin arzikin Iran zai iya kara tabarbarewa kafin lokacin.
Sannan akwai wani hadari bayan zaben na rabin wa’adi.
Kasancewar Trump ba zai nemi a zabe shi ba a zaben 2028, gwamnatinsa za ta ga cewa tana da ‘yancin ci gaba da fito na fito da Iran tare da shanye duk wani matsi.
Saboda haka Iran na kallon hagu ne kuma tana kallon dama.
Daya daga ciki shi ne siyasa da kuma yadda lamurra suke sauyawa a Amurka. Sai kuma na biyu tattalin arziki da kuma yadda abubuwa ke tafiya a cikin Iran.
Duk wani wata daya da zai wuce ana samun karancin sayar da danyen man fetur, toshe hanyoyin kasuwanci da kuma matsi a kan takardar kudin riyal, hakan zai sanya jiran lokaci kafin cimma yarjejeniya abu mai hadari.
Wannan ya sanya shugabanni Iran cikjn tsaka mai wuya. Amincewa da wasu bukatun Amurka zai zama tamkar mika wuya ne kuma hakan zai kara wa masu tsattsauran ra’ayi kwarin gwiwar yin suka.
Sai dai ci gaba da kira zai iya bai wa Iran dama idan Trump ya ci kari da matsaloli na siyasa ko na tattalin arziki. To amma Iran za ta iya tsintar kanta da rarrunan tattalin arziki kafin cimma yarjejeniyar.
Abubuwa da dama kuma sun dogara ne kan yadda al’amura za su wakana a wajen Iran.
Idan bankunan China da kasashen masu makwaftaka da ke da alakar kasuwanci suka yanke shawarar janye jiki don taoron Amurka, akwai yiwuwar Iran ta sauya salo.
Idan kuma ba haka ba to za a samu akasi. Iraniyawan da ke adawa da cimma yarjejeniya da Amurka za su iya cewa matakin Amurka bai yi nasarar a zo a gani ba, Iran ta ci gaba da jira.