Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya kai gwamnonin hamayya cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu?
- Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jawo hankalin 'yan siyasa da masu sharhi bayan da jam'iyyar APC ta fitar da sabon tsarin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2027, inda aka bai wa wasu manyan 'yan siyasar da ba mambobin APC ba muƙamai masu muhimmanci
A cikin jerin sunayen da APC ta fitar, gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke, wanda yanzu yake ƙarƙashin jam'iyyar Accord, da gwamnan jihar Anambra Charles Chukwuma Soludo na APGA, sun samu muƙaman jagorantar ayyukan yaƙin neman zaɓen Tinubu a jihohinsu.
Haka kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, duk da kasancewarsa ɗan PDP, zai jagoranci kamfen ɗin Tinubu a jihar Rivers da Abuja.
Bugu da ƙari, tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanatan PDP, Ibrahim Hassan Danƙwambo, ya samu matsayi na mai ba da shawara a kwamitin
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Laraba a Banquet Hall na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a wani mataki da APC ke ganin zai ƙarfafa shirye-shiryenta gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Abin da matakin ke nuna wa
Masu sharhi na ganin cewa wannan tsari na iya zama yunƙurin Tinubu na faɗaɗa tasirinsa a yankunan da APC ke da ƙalubale.
A jihar Anambra misali, APGA ce ke da rinjaye, yayin da a Osun Adeleke ya kasance ɗaya daga cikin fitattun gwamnoni masu farin jini a yankin Kudu maso Yamma.
Haka kuma, Nyesom Wike ya kasance ɗaya daga cikin ƙusoshin siyasar Najeriya duk da rikicin da ya dabaibaye PDP. Tun bayan kafa gwamnatin Tinubu, Wike ya ci gaba da nuna kusanci da shugaban ƙasar, lamarin da ya sanya wasu ke kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan abokan siyasar Tinubu da ba sa cikin APC.
Farfesa Abubakar Kari, na Jami'ar Abuja ya ce, ''mataki ne da bai zo da mamaki ba, idan za a iya tunawa tun 2023 wannan abin ya fara faruwa, a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP inda gwamnoninta guda biyar cike har da Ministan birnbin Abuja na yanzu suka fanɗare suka marawa shugaba Bola Ahmed Tinubu baya".
A cewar Kari, "Tun daga wancan lokacin irin wannan lamari ya fara zama jiki har ma waɗansu suka soma rungumarsa akan cewa ba kome ba ne mutum ya yi ungulu da kan zabo".
Martanin Wike
Da yake magana kan sabon tsarin, Wike ya bayyana matakin a matsayin shaidar ƙwarewar Tinubu a siyasa da kuma burinsa na haɗa kan ƙasa.
A cewarsa, shugaban ƙasar ya nuna cewa siyasa ba ta kamata ta kasance ta rabuwar kai ba, domin ana iya haɗa mutane daga jam'iyyu daban-daban domin cimma manufofin ƙasa.
Shigar da gwamnoni da manyan jiga-jigan da ba 'yan APC ba cikin kwamitin kamfen na Bola Ahmed Tinubu na 2027 na ɗauke da manyan saƙonni na siyasa, musamman ga jam'iyyun hamayya kamar PDP, APGA da Accord.
Farfesa Abubakar Kari ya ce, "kasancewar a yanzu, da dama daga 'ya'yan jam'iyyun sun soma tu'ajjubi cikin takaici ganin wani tsarin ungulu da kan zabo da wasu daga cikin gwamnoninsu ke yi musu".
Sannan masanin ya ce a baya jam'iyyar PDP ta mulki Najeriya kuma tana da tagomashi, amma irin yadda aka samu ɓangarori biyu, na Ministan Abuja Wike da na Tanimu Kabiru Turaki, na nuna waɗansu na cewa babu mamaki za a iya share tarihinta kwata-kwata".
1. Raunin haɗin kan hamayya
A siyasar Najeriya, gwamnoni su ne gimshiƙan kowace jam'iyya a jihar da suke jagoranta. Lokacin da gwamnan wata jam'iyya ko jigo mai tasiri ya shiga aikin kamfen na ɗan takarar wata jam'iyya, hakan kan nuna cewa jam'iyyar tasa ba ta da cikakken iko a kansa ko kuma akwai rikice-rikice a cikinta.
Farfesa Kari ya ce, "kasancewar Nyesom Wike na PDP da Ademola Adeleke da Charles Soludo suna cikin tsarin kamfen na APC na iya ƙara nuna cewa hamayya ba ta da cikakken haɗin kai gabanin zaɓen 2027".
2. Shin Tinubu na ƙoƙarin karya ganuwar jam'iyyu?
Masanin ya bayyana cewa a baya APC kan dogara ne kan gwamnoninta da jiga-jiganta kawai. Amma yanzu ana ganin Tinubu yana ƙoƙarin gina wata babbar tafiya ta siyasa da ta zarce iyakar APC.
"Sanya Soludo a Anambra, Adeleke a Osun da Wike a Rivers da Abuja na nufin shugaban ƙasar yana neman samun kariya da goyon baya a jihohin da ba APC ke da cikakken iko ba", in ji shi.
Mafi girman tasiri zai iya kasancewa a PDP. Jam'iyyar ta riga ta fuskanci rikice-rikice tun bayan zaɓen 2023, kuma rawar da Wike da Ibrahim Dankwambo ke takawa a kwamitin Tinubu na iya haifar da sabon rikici tsakanin masu son a ci gaba da zama a hamayya da masu neman kusanci da gwamnatin tarayya
3. Zai iya jawo cigaba da sauya sheƙa
Masana siyasa na ganin irin waɗannan naɗe-naɗe kan zama mataki na farko kafin sauya sheƙa ko ƙulla ƙawancen siyasa.
Ko da yake babu wanda daga cikin waɗannan gwamnoni ya sanar da komawa APC, kasancewarsu cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban APC na iya ƙarfafa zargin cewa akwai yiwuwar kusantar siyasa tsakaninsu da jam'iyyar mai mulki.
A cewar Farfesa Kari, "babu mamaki wannan yana nuna cewa duka jam'iyyun nan na da buri na kansu kawai kuma mutane na amfani da su ne a matsayin wata lema da ake amfani da ita kawai a cimma buri, babu akida babu alkibla, jam'iyyu ne kawai na yuyuyu".
"Haka kuma jam'iyyu ne tunda da safe za ka iya zama ɗan wannan jam'iyyar da rana ka koma wata da yamma ka shiga wata mai yuwa zuwa dare ma ka shiga wata", in ji shi.
5. Barazana ga ƙawancen hamayya na 2027
Farfesa Abubakar Kari, ya bayyana cewa duk yadda jam'iyyun hamayya suka yi, su sani haɗin kansu zai taimaka wajen samun nasararsu kuma, "bai kamata a ce 'yan siyasa su dawo suna yin abu ɗaya ba, ya kamata su kwana da sanin cewa, muddin suna so Najeriya a riƙa ƙirgata cikin ƙasashen da ke bin tafarkin dimukuraɗiyya to dole ne su raya jam'iyyu, su kafa jam'iyyu ba su riƙa tsalle yau suna nan gobe suna can ba", in ji shi.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyun hamayya ke ƙoƙarin gina wata babbar haɗaka da za ta iya fuskantar APC a zaɓen 2027. Sai dai shigar fitattun gwamnoni da jiga-jigan hamayya cikin tsarin kamfen na Tinubu na iya ƙara raunana yunƙurin haɗin kan hamayya, musamman a yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa matakin zai iya ƙara haifar da ce-ce-ku-ce a cikin PDP da sauran jam'iyyun hamayya, yayin da APC ke ƙoƙarin faɗaɗa tasirinta kafin fara gangamin zaɓen 2027.
Rahotanni na nuna cewa saka Adeleke, Soludo, Wike da Danƙwambo cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan siyasar da suka fi ɗaukar hankali a Najeriya, kuma zai iya sauya yanayin siyasar ƙasar yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.