Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu uku da ke sa ana yi wa yara mata auren wuri a arewacin Najeriya
Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta wallafa a ranar 23 ga watan Afirilun 2025, ya nuna cewa a kowace shekara, ana ƙiyasin kimanin ƴan mata miliyan 21 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 19 a ƙasashe masu ƙarami da matsakaicin kuɗin shiga ko masu tasowa suna ɗaukar ciki.
A sassa da dama na duniya, matasa ba sa samun isassun bayanai da ba su damar yanke shawara mai kyau game da lafiyar jima'i da haihuwa .
Wannan yana sa su kasance cikin haɗarin samun cikin da ba a shirya ba. Haka kuma, auren yara na ƙara tsananta wannan matsala.
A kwanan nan, WHO ta fitar da sabbin dabarun hana ɗaukar ciki da wuri da kuma rage munanan matsalolin lafiya da ke biyo ya yin ɗaukar ciki da haihuwa ga matasa musamman ƴaƴa mata
Matsalar aurar da ƴaƴa mata da wuri a tsakanin shekaru 12 da 14 da kuma 15 na ƙara yawaita ba wai a ƙasashe masu tasowa kaɗai ba, ana ganin haka a ƙasashen Afurka da yankin Asiya da Gabas ta tsakiya.
Ko a baya-bayan nan uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga iyaye da shugabanni da al'umma gaba ɗaya su haɗa kai wajen kawo ƙarshen auren wuri tare da tabbatar da kare haƙƙoƙin ƴaƴa mata.
Ta bayyana haka ne a saƙon ranar bikin Ranar 'Yar Mace ta 2026, wanda aka gudanar a ƙarƙashin taken "kawo ƙarshen auren yara da zuba jari a kula da haƙƙoƙin ƴaƴa mata,".
Inda ta ƙara da cewa buƙatar bai wa kowace yarinya damar samun ilimi da kiwon lafiya da kuma yanayin da zai ba ta damar cimma burikanta.
Ta jaddada cewa kowace ƴa mace na da haƙƙin yin karatu, girma da kuma gina makomarta ba tare da fuskantar wariya, tashin hankali ko wasu munanan al'adu da ke hana ta cimma burinta ba.
Sanata Oluremi Tinubu ta yi kira ga iyalai, al'umma, shugabannin addini da na gargajiya, da masu tsara manufofi da su ɗauki matakan kare haƙƙin 'ya'ya mata tare da kawo ƙarshen auren yara, wanda ke hana yara mata damar cigaba da karatu da samun ingantacciyar rayuwa.
Ta ce idan aka bai wa 'ya'ya mata damar bunƙasa da cimma burinsu, hakan zai amfani iyalai, al'umma da kuma ƙasa baki ɗaya.
"Lokacin da 'ya'ya mata suka samu damar bunƙasa, iyalai suna samun ci gaba, al'umma suna ƙara ƙarfi, ƙasa kuma tana samun cigaba mai ɗorewa," in ji ta.
Mene ne auren wuri?
Auren wuri, wanda ake kira auren yara na nufin idan ɗaya ko duka ma'auratan ba su kai shekara 18 ba, yana faruwa ne saboda dalilai na zamantakewa da al'adu da tattalin arziki da kuma na iyali.
A arewacin Najeriya da sauran sassan duniya, waɗannan dalilai kan sa iyaye su aurar da 'ya'yansu tun suna ƙanana.
Ba tare da la'akari da ƙanƙantar shekarunsu, ko sani kan abin da za su tarar bayan auren.
Abin da ke janyo yi wa yara mata auren wuri a Arewa
Lauya Huwaila mai rajin kare hakkin mata ta shaida wa BBC cewa matsalar na ƙara yawa a arewacin Najeriya, ta kuma zayyano wasu dalilai da suke janyo hakan.
Talauci
Talauci na taka muhimmiyar rawa wajen sanya iyaye aurar da ƴaƴansu mata da kanƙantar shekaru.
Ta ce yawancin matsalar na farawa ne da zarar yarinay ta ɗan tasa, batun zuwa makaranta kan shiririce ko dai saboda tsarabe-tsaraben da ke cikin harkar karatu da suka haɗa da kayan makaranta da na karatu ko kuɗaɗen da akan buƙata a makaranta.
Hakan na sanya a janye ƴanmatan da ɗora musu talla domin samun abin kai wa baka, daga nan kuma da zarar wani ya nuna sha'awar auren ƴarsu shikenan.
Wasu iyaye na ganin hakan a matsayin hanya sassauƙa da za a ɗauke musu nauyin ciyarwa da tufarawa da sauran buƙatun ƴaƴa mata.
Al'ada
Al'ada na taka muhimmiyar rawa a fannin aurar da ƴaƴa mata da wuri, wasu al'ummomi suna ganin aure da wuri a matsayin al'ada ko hanyar kare mutuncin iyali, al'adu da bin tsarin gargajiya suna ƙarfafa auren yara tun suna ƙanana.
Zumunci
Wasu iyaye suna ganin auren wuri zai ba ƴaƴansu kariya ko kuma ya inganta dangantaka tsakanin iyalai, ba lallai sai waɗanda suka hada jini ko zuriya ba.
A sakamakon haka, waɗannan abubuwa na iya rinjayar iyalai su aurar da 'ya'yansu a lokacin ƙuruciya, ba tare da la'akkari da matsalolin da ke biyo bayan auren ba.
Wani rahoto na Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya fitar, ya yi ƙiyasin sama da mata miliyan 24 ne aka aurar da ƙanƙantar shekaru a Najeriya.
Rahoton ya ce mata 3 cikin 10 sun fuskanci wannan matsalar ta auren wuri, wannan ya sanya hakan a matakin kashi 30 cikin 100.
Sai kuma matan da aka aurar kafin su kai shekara 18 da ya kai kashi 12 cikin 100.
Ana samun kaso mafi yawa daga iyalai matalauta, sai masu dan ƙaramin ƙarfi, sai matsakaita, ya yin da adadin ba shi da yawa ga iyalai masu arziki.
Illolin auren wuri
Auren wuri na iya haifar da matsaloli da dama ga yara, musamman ga ƴan mata.
Barista Huwaila ta lissafo wasu daga cikin illolinsa kamar haka:
- Katsewar karatu
Yara da aka aurar da wuri sau da yawa kan daina zuwa makaranta, wanda ke rage damar samun ilimi da aikin yi a nan gaba.
- Matsalolin lafiya
Ciki da haihuwa a ƙuruciya na iya jawo matsaloli ga uwa da jariri, saboda jikinta bai gama girma ba.
- Talauci
Rashin ilimi da ƙwarewa na iya sa ma'auratan su ci gaba da rayuwa cikin talauci, kuma cikin kanƙanin lokaci za su tara iyalin da ba su da halin kula da ciyarwa, tufatarwa, ilimi da ba su kariya daga faɗawa mawuyacin hali nan gaba.
- Matsalolin tunani da damuwa
Nauyin aure da kula da iyali tun da wuri na iya haifar wa ƴa mace damuwa, tsoro, da wasu matsalolin ƙwaƙwalwa.
- Rashin ƴancin yanke shawara
Yaran da aka aura da wuri kan rasa damar yi wa kansu tunani, ko mafita daga wata matsala, ko zaɓawa kai muhimman abu da ka iya inganta rayuwarsu ko akasin haka.
- Yiwuwar rashin zaman lafiya
Wasu yara kan fuskanci cin zarafi ko matsaloli a zaman aurensu saboda ƙarancin shekaru da rashin ƙarfin kare kansu, matsalar na faɗaɗa kan ƴayan da mace ta haifa su taso cikin tsangwa da wahala.