Tottenham ba ta da niyyar sayar da van de Ven, ƙungiyoyin Premier na neman Matanovic

Micky van de Ven
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tottenham ba ta da wata niyyar sayar da ɗan wasan baya Micky van de Ven, mai shekara 25, yayin da Liverpool ke shirin zawarcin ɗan wasan na tawagar Netherlands a shekara mai zuwa. (Football Insider)

Manchester United da Arsenal da Chelsea na cikin jerin ƙungiyoyin da ke sa ido kan ɗan wasan gaba na Freiburg ɗan ƙasar Croatia, Igor Matanovic, mai shekara 23. (Caughtoffside)

Juventus na son ɗaukar ɗan wasan baya na Liverpool, Giovanni Leoni, mai shekara 19, yayin da ƙungiyar ta gasar Serie A ke son ƙara yawan ƴan wasan Italiya a cikin tawagarta. (Gazzetta dello Sport)

Newcastle United a shirye take ta bar Joe Willock, mai shekara 27, ya bar ƙungiyar a lokacin kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu, ganin cewa kwantiraginsa zai ƙare a lokacin bazara kuma har yanzu bai fara tattaunawa kan sabuwar kwantiragi ba. (Football Insider)

AC Milan na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Brighton kuma ɗan ƙasar Sweden, Yasin Ayari mai shekara 22, a matsayin wanda zai maye gurbin Luka Modric idan har ɗan wasan na Croatia mai shekara 41 ya yanke shawarar yin ritaya. (Tuttosport)

Brighton da Bournemouth sun tura wakilansu zuwa birnin Medellin domin kallon ɗan wasan baya na tsakiya ɗan ƙasar Colombia, Neider Parra mai shekara 21, wanda ke buga wa ƙungiyar Atletico Nacional wasa. (El Deportivo)

Babban jami'in gudanarwar Brighton, Paul Barber, ya shirya matakan da za a bi idan manyan ƙungiyoyi suka nuna sha'awar ɗaukar fitattun ƴan wasan ƙungiyar. (Sky Sports)

Mai tsaron ragar Brentford dan ƙasar Iceland, Hakon Rafn Valdimarsson mai shekara 24, na iya duba yiwuwar barin ƙungiyar a nan gaba idan har ya gaza samun damar buga wasa a babban tawagar ƙungiyar. (RUV)

Roma na son ɗaukar ɗan wasan gaba na Brazil, Endrick, a matsayin aro daga Real Madrid a watan Janairu, inda shi kuma ɗan wasan mai shekara 20 ke matuƙar son komawa ƙungiyar ta Serie A domin samun ƙarin damar buga wasa. (Corriere dello Sport)

Ana shirin sabunta kwantiragin ƴan wasan Barcelona da suka haɗa da ɗan wasan gaba na Brazil Raphinha (mai shekara 29), da ɗan wasan baya ɗan ƙasar Spain Xavi Espart, da kuma ɗan wasan tsakiya Marc Bernal. (Fabrizio Romano)