Za a gudanar da zanga-zanga a Spain saboda tsadar gidaje
Ana shirin gudanar da manyan zanga-zanga a biranen ƙasar Spain domin neman a ɗauki mataki kan matsalar ƙarancin gidaje a ƙasar.
Ana sa ran za a yi mafi girman zanga-zangar a birnin Madrid, inda masu zanga-zangar ke ci gaba da zama a wani babban dandali da tsakiyar birnin.
Ana ci gaba da samun tashin hankali tun bayan da aka kori wata tsohuwa mai shekara tamanin da bakwai daga gidanta da ke babban birnin ƙasar, bayan da aka ninka mata kuɗin haya.
A jiya Juma'a, majalisar dokokin kasar ta yi watsi da shirin gwamnatin na dakatar da karin kudin haya da kuma hana korar masu haya da ke cikin mawuyacin hali.





















