Najeriya za ta kara da Madagascar da Tanzania a neman gurbin Afcon

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rob Stevens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Ghana an haɗa ta da ƙasashen Ivory Coast a wani was da zai ɗauki hankali na neman zuwa gasar cin kofin Afirka ta 2027 (Africa Cup of Nation).
Ba a sanya Gaha a acikin ƙasashen farko ba a tukwane rukuni-rukuni, bayan ƙasar ta faɗo a jerin ƙasahen duniya da suka fi ƙwarewa wajen taka leda, bayan gaza zuwa gasar da ta gabata a Moroko, wadda aka yi a watan Disamba da Janairu.
Gahanar za ta kece raini ne a rukunin C, inda za su fuskanci Gambia, wadda ta kai matakin kwata-fainal a gasar ta 2021.
"Me ya sa kullum abin ke ƙarewa kan mu? Wannan rukuni na da wahala," in ji tsohon ɗan wasan Ivory Coast Maz-Alain Gradel, wanda ya taɓa lashe kofin Afirka a tawagar Elephants a gida a gasar 2020, kuma yana daga cikin wadanda ya taimaka wajen raba ƙasashen a birnin Alƙahira.
"Amma za mu yi duk abin da ya kamata domin mu fito. Ina ganin muna da ƴanwasan, ba mu da matsala."
Kenya da Tanzani da Uganda ne za su ɗauki baƙuncin gasar kofin Afirka mai zuwa, wanda za a gudanar daga ranar 19 ga watan Yunin zuwa 17 ga watan Yulin 2027.
An raba ƙasashe 48 zuwa hurhuɗu a cikin rukuni 12, inda ƙasashe biyu na saman kowane rukuni za su yi nasarar buga gasar cin kofin.
Sai dai ƙasashe uku da za su karɓi baƙuncin dukkaninsu an ba su gurbi, saboda haka ƙasa ɗaya ce a cikin rukuninsu za su samu nasraar zuwa gasar.
Najeriya da Afirka ta Kudu da kuma Tunisia duk suna cikin wannan siradi kasancewar suna cikin rukuni ɗaya da ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar.
Kenya da za ta kara da Eritria, waɗanda wannan ne karon farko da suka dawo buga wasannin neman shiga gasa karon farko a tun daga shekara ta 2008, inda za su hadu da Guinea da Afirka ta Kudu a rukunin A.
Ita kuwa Masar wadda ta taɓa lashe kofin sau 7 za ta fafata ne da Angola da Malawi da Sudan ta Kudu.
Za a buga wasanni hurhuɗu ne na neman zuwa gasar a cikin watan Satumba da Oktoba da kuma Nuwamban wannan shekara, inda za a buda wasanni biyu na ƙarshe a watan Maris na shekara mai zuwa.
Har yanzu ana jiran hukunci kan ƙasar da ta lashe gasar Afcon ta 2025

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu bai a kammala sanin wace ƙasa ce ta lashe kofin Afcon din na 2025 ba bayan Senegal sun lallasa mai amasauki baƙi Moroko 1-0 a ƙarin lokaci, a wani wasan ƙarshe da ya zama mai cike da taƙaddama a ranar 18 ga watan Janairu.
Ƴan wasan Senegal da dama sun fice daga filia lokacin da alƙalin wasa ya bai wa Moroko bugun fenariti a kusa da ƙarshen lokaci, inda aka dakatar da wasan na tsawon minti 17 kafin dsaga baya Brahim Diaz ya gaza cin bugun fenaritin.
Amma a ranar 17 ga watan Maris, kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafe ta hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Afirka CAF ta bai wa Senegal rashin nasara inda ta ce Senegal ta yi watsi da nasarar da ta samu, sannan ta bai wa Moroco kofin.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta yi watsi da matakin inda ta daukaka ƙara zuwa ga kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen wasanni (Cas) wanda har yanzu bai yanke hukunci kan batun ba.
Jadawalin yadda za a kara a wasannin neman gurbin Afcon 2027
Rukunin A: Morocco, Gabon, Nijar, Lesotho
Rukunin B: Masar, Angola, Malawi, Sudan ta Kudu
Rukunin C: Ivory Coast, Ghana, The Gambia, Somalia
Rukunin D: Afirka ta Kudu, Guinea, Kenya, Eritrea
Rukunin E: DR Congo, Equatorial Guinea, Saliyo, Zimbabwe
Rukunin F: Burkina Faso, Benin, Mauritania, Central African Republic
Rukunin G: Kamaru, Comoros, Namibia, Congo-Brazzaville
Rukunin H: Tunisia, Uganda, Libya, Botswana
Rukunin I: Algeria, Zambia, Togo, Burundi
Rukunin J: Senegal, Mozambique, Sudan, Ethiopia
Rukunin K: Mali, Cape Verde, Rwanda, Laberiya
Rukunin L: Najeriya, Madagascar, Tanzania, Guinea-Bissau
Ranakun wasa ta ɗaya da ta biyu: 21 Satumba zuwa zuwa 6 Oktoba 2026
Ranakun wsa na uku da huɗu: 9-17 Nuwamba 2026
Ranakun wasa na biyar da shida: 22-30 Maris 2027











