Galatasaray ta taya Martinelli, ina Zubimendi zai tafi?

Asalin hoton, Getty Images
Galatasaray ta taya ɗanwasan Arsenal da Brazil Gabriel Martinelli kan fam miliyan 38.4. (Florian Plettenberg)
Arsenal na son sayar da ɗanwasan tsakiya na Spain Martin Zubimendi kan kudi aƙalla fam miliyan 77, yayin da ke kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan mai shekara 27-year-old. (Teamtalk)
Aston Villa na tattaunawa da West Ham domin ɗauko ɗanwasan baya Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 28, yayin da darajar ɗanwasan na DR Congo ta kai fam miliyan 25. (Athletic - subscription required)
Ipswich na dab da kammala cinikin ɗanwasan Ivory Coast mai shekara 20 Abdoul Ouattara daga Strasbourg. (Sky Sports)
Aston Villa ta yi wa Bayern Munich tayin aro na ɗanwasan tsakiyarta na Portugal Joao Palhinha, mai shekara 31, amma Bayern ta fi son sayen ɗanwasan. (Florian Plettenberg)
Newcastle ta ƙarfafa tattaunawa domin ɗauko ɗanwasan baya na Benfica Amar Dedic from Benfica, inda aka bayyana darajar ɗanwasan na Bosnia Herzegovina kan fam miliyan 25. (Mail)
Hull City na fatan cimma yarjejeniya domin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Augsburg Mert Komur duk da watsi da tayin farko na fam miliyan 10.2 da aka yi kan ɗanwasan na Jamus mai shekara 21. (Teamtalk)
Ɗanwasan tsakiya na Newcastle Joe Willock na Ingila na tattaunawa domin zuwa Besiktas, kuma ana iya sayensa kan fam miliyan 17. (Foot Mercato - in French)
Ɗanwasan tsakiya na Brighton da Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 22, na cikin ƴanwasan da Newcastle ke farauta domin maye gurbin Bruno Guimaraes, mai shekara 28 da kuma ɗanwasan Italiya Sandro Tonali. (Mail)











