Abin da ya sa na daina amfani da man bilicin

    • Marubuci, Aisha Aliyu Jaafar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Akalla kashi 77 na mata a Najeriya ke amfani da mayukan bilicin, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, kuma kasar ce ta fi yawan masu amfani da su a Nahiyar Afirka.

A shekarar 2023, Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ayyana dokar ta-ɓaci kan amfani da waɗannan mayuka, sakamakon kara yawaitar amfani da su da kuma illolin da suke da shi ga lafiya.

To sai dai jami’an kiwon lafiya da masu wayar da kai na ci gaba da jan hankali game da illolin yin shafe-shafe, da ake ganin ƙamarin shi ya sa har yara ake shafa mawa, kamar yadda wani rahitin BBC ya gano.

Halima Shehu, wata ma'aikaciyar jinya ce kuma a yanzu kwararriyar mai gyaran fuska, wadda ke wayar da kan mata game da yadda za su gyara fatar su ba tare da amfani da mayukan bilicin ba, bayan ita ya yi hakan, kuma ta ji a jikin ta.

“Na fara wayar da kan mata game da bilicin ne bayan na bayar da labarina da ban yi tunanin zai ja hankali ba. Bayan na bayar da labarin na samu mutane da dama da ke ta yi min magana cewa suna so su daina, sannan suna faɗa min matsalolin da suke da shi, kuma haka ne ya ƙara min ƙwarin gwiwar ci gaba da magana kan amfani da mayukan shafe-shafe a shafukan sada zumunta,” in ji Halima.

Abin da ya sa na fara amfani da man bilicin

Halima ta bayyana cewa tun farko ba wai sauya launin fatar ta ne ta so yi ba.

Ta ce tun da fari ƙurajen fuska ne suka fito mata suka yi mata yawa, har ya sa ta fara neman maganin kawar da su.

''Yawanci duk irin maganin da zan yi amfani da su, magunguna ne da ke sanya fuska haske.''

A cewar ta a lokacin ma ta yi tunanin duk wani magani da zai cire maka kurajen fuska dole ne ya saka ka haske.

“Abin da ya sa na fara bilicin gaba ɗaya kuma shi ne saboda idan na daina amfani da mayukan sai kurajen su dawo. Bayan na ci gaba da shafawa kuma sai na ga to ta yaya jikina da fuska ta za su yi daban-daban, sai na fara shafawa a jikina,” a cewar ta.

Illolin da shafa mayukan suka janyo min

Halima ta ce duk da mayukan suna kashe mata kurajen a lokacin, amma sun janyo mata matsaloli da dama.

Kamar ƙonewar fuska sakamakon zafin rana, da fitowar nankarwa a jiki, sannan fatar ta yi launi daban-daban, yatsunta suka yi baƙi, saboda ba sa ɗaukar man, “jikina dai kawai ya kasance ba kala daya ba” in ji Halima.

Yadda za ki daina amfani da man bilicin

'Man bilicin ya janyo min illoli da dama, wanda ya sa har na kasance ba ni da karfin gwiwar shiga cikin jama'a. Gashi dai ina so in daina amma ba na so ƙurajen su dawo min,” in ji Halima.

Halima Shehu ta ce a lokuta da dama ta sha daina amfani da su, amma kuma sai daga baya ta ci gaba, kafin daga baya ta samu ƙwarin gwiwar dainawa gaba ɗaya.

Daina sauraron mutane:

Hanyar farko da ta ce ta bi ita ce daina sauraron maganganun mutane, saboda a cewar ta waɗannan maganganu su ne manyan abubuwan da ke hana mutane dainawa.

'An san ki kina da haske, da kin daina kin fara duhu, sai a fara tambayar mene ya same ki, ba ki da lafiya ne?‘

Sauya wurin zama:

Halima ta ce damar da ta samu na barin jihar Kano inda ta yi karatu, zuwa Abuja ya sa ta yanke shawarar daina wa a wannan lokaci.

Sauya man gyaran fuska:

'Na fara amfani da Skin care products da za su iya cire kurajen fuska ba tare da sun haskaka fatar ka ba, ko lalata maka fuska,’ kamar yadda ta shaida wa BBC.

Gangamin wayar wa mata kai game da daina shafe shafe

Halima ta ce tun bayan da ta fara wayar wa mata kai game da illolin shafe-shafe a shafukan sada zumunta, da kuma koyar da su hanyoyi marasa illa na gyara fata, mata da yawa sun karɓi wannan kira.

Ta ce tun bayan da ta fito ta bayar da labarinta, ta samu mata da yawa da ke zuwa suna ce mata a dalilinta suka daina bleaching, ta hanyar bin shawarwarinta kuma suna ganin fatarsu na yin kyau.

Ta kuma ce hakan na yi mata daɗi matuka, saboda tana ganin hakan ya nuna abin da take yi mai kyau ne, kuma ya na kara mata ƙwarin gwiwa.

Abin da ke sa wasu matan yin bilicin

Halima ta ce daga mutanen da take tattaunawa da su, wasu sun shaida mata cewa su ma kashe kuraje ne ya sa su fara shafe shafe.

Wasu kuma sukan fara ne kafin gab da lokacin auren su, bayan an ba su wasu mayuka da za su kara musu kyau kafin lokacin bikin.

Ta ce wasu matan kuma samarin su ne ke son farar mace, su kuwa bakake ne, sai hakan ya sa su fara bilicin.

Halima ta ce bayan da ta sauya yadda take gyara fuskarta, sai ta gane cewa wasu abubuwan da ake yi na gyaran fuska a zamanance na bukatar kwarewa, kuma a matsayinta ta ma’aikaciyar jinya, tana ganin su ya kamata su rika yin irin wadannan ayyuka.

A cewar ta hakan ne ya sa ta je wurin koyon gyaran fuska, kuma a yanzu ta kammala.

”Yanzu ina iya zuwa gidajen mutane, ko muyi magana ta intanet, in duba fatar su, in ba su shawarwari, ko in dan yi musu wasu ayyukan gyaran fuskar a gida.

Kwararriyar mai gyara fatar ta kuma bai wa mata shawarwari game da rungumar ainihin launin fatar su, da guje wa shafe-shafe.

”Idan kin fara kina ganin a yanzu fatar ki na yin kyau, to daga baya fatar za ta zo ta lalace. Kuma zai sa ki rage kwarin gwiwar shiga mutane, har ma ya iya shafar lafiyar kwakwalwa“