Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023
- Marubuci, Uche Akolisa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 12
Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen ƙasa a watan Janairun 2027, ana sa ran miliyoyin 'yan ƙasa za su kaɗa ƙuri'a domin zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni, da kuma 'yan majalisun dokoki na tarayya da na jihohi.
Lokacin da 'yan Najeriya suka je rumfunan zaɓe a shekarar 2023, mutane da dama sun yi imanin cewa sabuwar fasahar gudanar da zaɓe da aka ƙaddamar, yawan matasa da suka fito kaɗa ƙuri'a, da kuma gasa ta musamman tsakanin manyan 'yan takarar shugaban ƙasa guda uku za su taimaka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar.
Sai dai matsalolin fasaha da suka shafi shafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na duba ko sakamakon zaɓe sun yi tasiri wajen rage amincewar jama'a da tsarin.
Daga bisani an ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe ɗaya daga cikin zaɓukan da suka fi zafi a tarihin Najeriya.
Manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP), sun ƙalubalanci sakamakon a kotu. Sai dai a ƙarshe Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Tinubu.
Shekaru huɗu bayan haka, Najeriya na sake komawa rumfunan zaɓe cikin wani yanayi da ya bambanta da na baya, ta fuskar siyasa da tattalin arziki.
An samu sauye-sauye a dokokin zaɓe, jam'iyya mai mulki ta faɗaɗa tasirinta a fagen siyasa, yayin da masu kaɗa ƙuri'a ke fuskantar sabbin ƙalubale da suka haɗa da tsadar rayuwa, matsalolin tsaro da kuma wutar lantarki.
Haka kuma, sabon rukuni na matasa masu jefa ƙuri'a na shirin taka muhimmiyar rawa a zaɓen.
Ga abubuwa shida da suka sauya a Najeriya tun bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
An sauya dokokin zaɓe
Zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ya fuskanci suka daga sassa daban-daban bayan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta kasa ɗora sakamakon rumfunan zaɓe a shafinta na IReV (INEC Result Viewing Portal) kai tsaye kamar yadda aka tsara, duk da cewa an kirkiro tsarin ne domin ƙara fayyace sahihancin zaɓe da kuma tabbatar da gaskiya.
A wasu zaɓukan gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi da aka gudanar a lokuta daban-daban a shekarar 2022, tsarin ya yi aiki yadda ya kamata. Sai dai matsalolin da suka taso a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, waɗanda INEC ta danganta da matsalar fasaha, sun sa 'yan Najeriya da dama suka fara tambayar sahihancin tsarin zaɓen.
A martanin da aka mayar kan waɗannan matsaloli, Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanadi sabbin matakai da suka wajabta wa jami'an da ke kula da rumfunan zaɓe aika sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki zuwa shafin IReV bayan an cike, an sanya hannu a takardar sakamako ta EC8A, kamar yadda Sashe na 60(3) na dokar ya tanada.
Sai dai duk da haka, dokar ta ci gaba da ba da damar aika sakamako ta hannu idan aka fuskanci matsalar sadarwar intanet ko wata tangarda a tsarin. Wannan tanadi na ci gaba da janyo muhawara gabanin zaɓen 2027.
Daraktan Makarantar Abuja ta Nazarin Siyasa da Tunanin Jama'a, Sam Amadi, ya ce wannan keɓancewar na iya raunana amincewar jama'a da sauye-sauyen da aka yi.
Ya ce: "Tanadin da ya ba da damar aika sakamako ko rubuta shi ta hannu idan aka samu matsalar sadarwa ko matsalar tsarin na iya haifar da rudani a harkar siyasa, domin wasu jami'an INEC na iya ƙin ɗora sakamakon suna mai danganta hakan da rashin intanet."
Sai dai INEC ta ce aika sakamako ta lantarki ba ta maye gurbin tsarin tattara sakamako na hannu ba, illa tana ƙara masa ƙarfi ne.
Kwamishinan Zaɓe na Jihar Edo, Obo Effang, ya ce: "Har yanzu tsarin kaɗa ƙuri'a a Najeriya ana gudanar da shi ne da hannu. Ana ƙirga ƙuri'u da hannu, ana rubuta sakamakon a takardar sakamako da hannu, sannan a yi amfani da na'urar BVAS wajen ɗaukar hoton takardar, wanda shi ne ake ɗorawa a shafin IReV."
Ya ƙara da cewa daga nan ne ake ci gaba da tattara sakamakon da hannu daga matakin ƙananan hukumomi zuwa jihohi har zuwa matakin ƙasa.
Dangane da sabon tanadin doka, ya ce: "Ko akwai intanet ko babu, za a yi ƙoƙarin ɗora sakamakon. Amma hakan ba zai canza gaskiyar cewa har yanzu za a ci gaba da tattara sakamakon ne da hannu ."
Masu goyon bayan gyare-gyaren sun ce za su taimaka wajen ƙara bayyana gaskiya a zaɓe, yayin da masu suka ke ganin tanadin da ya ba da damar amfani da tsarin hannu a wasu lokuta na iya haifar da rashin tabbas. Ko waɗannan sauye-sauyen za su dawo da cikakkiyar amincewar jama'a da tsarin zaɓe zai fito fili ne lokacin da 'yan Najeriya za su kaɗa ƙuri'a a 2027.
Hakazalika, dokar ta kuma tanadi gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye a cikin jam'iyyu da samar da rijistar mambobi ta dijital, da damar sauke katin zaɓe ta yanar gizo, tare da amincewa da sabbin jam'iyyun siyasa biyu da aka yi wa rijista.
Wannan ya sa adadin jam'iyyun siyasa a ƙasar ya kai 20, ciki har da Nigeria Democratic Congress (NDC), jam'iyyar da Peter Obi ke takara a ƙarƙashinta.
Jam'iyyar da ke mulki ta ƙara faɗaɗa ikonta a jihohi da dama na ƙasar
Tun bayan zaɓen 2023, an samu manyan sauye-sauye a yanayin siyasar Najeriya.
A shekaru huɗu da suka gabata, zaɓen shugaban ƙasa na ɗaya daga cikin zaɓukan da suka fi zafi tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
A lokacin, jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ta fuskanci ƙalubale mai ƙarfi daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kuma Labour Party (LP), wadda ɗan takararta Peter Obi ya samu goyon bayan matasa da kuma masu kaɗa ƙuri'a karo na farko.
Sai dai gabanin zaɓen 2027, al'amura sun sauya.
Sauya sheƙar gwamnonin jihohi zuwa APC ya sa jam'iyyar mai mulki ke da goyon bayan gwamnoni 30 daga cikin jihohi 36 na Najeriya, lamarin da ya haifar da muhawara kan ko ƙasar na tafiya ne zuwa tsarin jam'iyya ɗaya.
Irin wannan rinjaye na siyasa ya taɓa faruwa a baya. A shekarar 2007, jam'iyyar PDP wadda ke mulki a lokacin, tana iko da jihohi 28 cikin 36 na Najeriya.
Masu sukar wannan yanayi na cewa taruwar ƙarfin siyasa a hannun jam'iyya ɗaya, na iya rage ingancin tsarin dimokuraɗiyya da ɗora masu mulki a kan turbar yin abin da suke so ba tare da cikakken sa ido ba.
Sai dai masu goyon bayansa suna cewa gwamnoni kan fi karkata zuwa jam'iyyar da ke mulki a matakin tarayya ne domin samar da kyakkyawar haɗin gwiwa da kuma sauƙaƙa samun albarkatun gwamnatin tarayya.
Matsalar tsaro na ci gaba da kasancewa babban ƙalubale a ƙasar
Batun tsaro ya mamaye yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, kuma har yanzu yana ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ke jan hankali gabanin zaɓen 2027.
A lokacin da ya kama aiki a ranar 29 ga Mayun 2023, Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin mayar da tsaro a matsayin babban abin da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kai, yana mai cewa ba za a iya samun ci gaba ko adalci ba a yanayin rashin tsaro da tashin hankali. Haka kuma ya yi alkawarin sake fasalin tsarin tsaro na ƙasar.
Tun daga lokacin, gwamnati ta ce ta ɗauki ƙarin jami'an 'yan sanda 20,000 aiki, ta ƙara kuɗaɗen da ake warewa harkokin tsaro, tare da sauya shugabannin hukumomin tsaro.
Sai dai duk da waɗannan matakai, sace mutane domin neman kuɗin fansa, ayyukan masu tayar da ƙayar baya da sauran nau'o'in laifukan tashin hankali sun ci gaba. Har ila yau, hare-haren sun bazu daga yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma zuwa wasu sassan Kudu maso Yamma.
A Jihar Oyo, alal misali, sojoji sun samu nasarar ceto mutum 45 da aka yi garkuwa da su, ciki har da ɗalibai da malamansu, bayan sun shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane.
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka ja hankalin jama'a a lokacin mulkin Tinubu shi ne sace fiye da yara 300 daga Makarantar Katolika ta St Mary's Private Catholic School da ke Jihar Neja. Wannan shi ne mafi girman sace ɗalibai da aka yi a lokaci guda a tarihin ƙasar.
Bayanan ƙungiyar Armed Conflict Location and Event Data (Acled) sun nuna cewa tsakanin shekarun 2015 da 2023, an samu hare-haren sace ɗalibai sau 10 a Najeriya, inda aka yi awon gaba da kimanin ɗalibai da malamai 1,127.
A cikin shekaru uku na farko na gwamnatin Tinubu kuwa, an samu manyan hare-haren sace mutane tara da suka shafi sama da mutum 500.
Masana sun ce bazuwar hare-haren zuwa yankunan da a baya ake kallon suna da zaman lafiya ya ƙara jefa damuwa a zukatan jama'a.
Tasirin matsalar tsaro ya wuce batun kare rayuka da dukiyoyi kaɗai. Hare-hare kan al'ummomin manoma sun kawo cikas ga noman amfanin gona, lamarin da ya ƙara ta'azzara matsalar ƙarancin abinci.
Shirin samar da abinci na duniya,ya kiyasta cewa mutum miliyan 35 a Najeriya na iya fuskantar matsalar rashin wadataccen abinci a shekarar 2026, idan aka kwatanta da mutum miliyan 24.8 a shekarar 2023.
Yayin da 'yan Najeriya ke shirin sake komawa rumfunan zaɓe, ana sa ran batun tsaro zai kasance ɗaya daga cikin manyan ma'aunin da masu kaɗa ƙuri'a za su yi amfani da shi wajen tantance nasarorin gwamnati da kuma alkawuran waɗanda ke neman maye gurbinta.
'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa
Samson Itodo, babban daraktan ƙungiyar Yiaga Africa, ya ce:
"Duk wani ɗan Najeriya da ke damuwa da ingancin rayuwarsa ya kamata ya damu da wanda zai lashe zaɓen 2027, domin shugabannin da za a zaɓa ne za su yanke muhimman shawarwari na siyasa da tattalin arziki da za su shafi makomar 'yan Najeriya."
Tun kafin zaɓen 2023, batutuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum da walwalar jama'a sun kasance muhimman abubuwan da suka mamaye muhawarar siyasa a ƙasar. Bayan shekaru huɗu, matsalar tsadar rayuwa ta ƙara zama babban batu gabanin zaɓen 2027.
A jawabinsa na rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen tallafin man fetur, yana mai cewa kasafin kuɗin da ya gada bai tanadi kuɗin ci gaba da tallafin ba.
Tun daga lokacin, cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin naira bisa ƙarfin kasuwa sun sauya yanayin tattalin arzikin Najeriya, lamarin da ya haifar da ƙarin kuɗin sufuri, tsadar kayan abinci da kuma hauhawar kuɗaɗen gudanar da rayuwar yau da kullum.
Alƙaluman Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 24.7 cikin ɗari a shekarar 2023, kafin ta kai matsayi mafi girma na kashi 37.57 cikin ɗari a watan Agustan 2024.
Sai dai zuwa watan Janairun 2026, adadin ya ragu zuwa kashi 17.18 cikin ɗari, duk da cewa har yanzu 'yan Najeriya da dama na ci gaba da fama da tsadar rayuwa.
Masanin tattalin arziki Boniface Chizea ya ce matsalolin tattalin arzikin ƙasar sun ƙara tsananta idan aka kwatanta da lokacin zaɓen da ya gabata.
Ya ce:
"Najeriya na da duk abin da take buƙata domin ta samu ci gaba, amma cin hanci da rashawa, ƙara talauci, ayyukan ta'addanci da kuma garkuwa da mutane na ci gaba da kawo mata cikas. Nahiyar Afirka ba za ta iya cimma burinta yadda ya kamata ba idan Najeriya ba ta taka rawar da ake sa ran za ta taka ba."
Ya kuma yi nuni da cewa, duk da raguwar adadin hauhawar farashin kayayyaki, "halin da ake ciki a yanzu ya fi tsanani idan aka kwatanta da shekarar 2023."
Ga 'yan Najeriya da dama, babban abin da zai iya rinjayar zaɓen 2027 ba wai bambancin akidun siyasa ba ne, illa tambayar ko rayuwa ta zama mai sauƙi da araha fiye da yadda take shekaru huɗu da suka gabata.
Har yanzu batun wutar lantarki na daga cikin muhimman batutuwan da ake amfani da su wajen auna nasarar gwamnati
Samar da ingantacciyar wutar lantarki na daga cikin manyan alƙawuran da ake auna nasarar shugabannin Najeriya da su, kuma har yanzu batu ne mai muhimmanci gabanin zaɓen 2027.
A lokacin yakin neman zaɓen shekarar 2023, Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa masu kaɗa ƙuri'a cewa: "Idan ban samar muku da tabbatacciyar wutar lantarki ba sannan na dawo neman wa'adi na biyu, kada ku zaɓe ni, sai dai idan na ba ku gamsassun dalilan da suka hana ni cika alƙawarin."
Tun bayan hawansa mulki, gwamnatin Tinubu ta aiwatar da wasu daga cikin manyan sauye-sauyen da aka gani a fannin wutar lantarki cikin shekaru da dama.
Dokar wutar lantarki da kuma gyaran kundin tsarin mulki sun bai wa jihohi damar kafa kasuwannin wutar lantarki na kansu a karon farko, ta hanyar samarwa, jigilarwa da rarraba wutar lantarki ba tare da dogaro kacokan ga tsarin wutar lantarki na ƙasa ba.
Haka kuma gwamnati ta amince da wani shiri na dala biliyan 2.4 domin magance matsalolin basussukan da suka daɗe suna addabar fannin lantarki, da nufin farfaɗo da yanayin kuɗaɗen kamfanonin lantarki da kuma inganta samar da wutar.
Sai dai duk da waɗannan sauye-sauyen, har yanzu 'yan Najeriya da dama na fama da yawan katsewar wutar lantarki, yayin da kuma kuɗin amfani da wutar ya ƙaru.
Bayanan Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) sun nuna cewa ƙasar ta samar da sama da megawatt 4,922 na wutar lantarki a shekarar 2023.
Zuwa watan Janairun 2026 kuwa, kimanin megawatt 4,901 ne a matsakaici ke samuwa don rabawa daga cikin ƙarfin samar da wutar lantarki da ya kai megawatt 13,625.
Yayin da gidaje da 'yan kasuwa ke ci gaba da dogaro da janareto da sauran hanyoyin samar da makamashi, ana sa ran batun wutar lantarki zai kasance ɗaya daga cikin muhimman ma'aunan da masu kaɗa ƙuri'a za su yi amfani da su wajen tantance ayyukan gwamnati a lokacin zaɓen 2027.
Matasa na ci gaba da tasiri a zaɓen Najeriya.
Matasan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen tsara tattaunawar siyasa a zaɓen 2023, kuma ana sa ran za su ci gaba da kasancewa wani muhimmin rukuni da zai iya tasiri kan sakamakon zaɓen 2027.
Bayanan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sun nuna cewa mutanen da shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 35 sun kasance kashi 76 cikin 100 na sabbin masu rajistar zaɓe a babban zaɓen da ya gabata.
Sai dai duk da haka, kashi 30.56 cikin 100 ne kawai daga cikinsu suka fito suka kaɗa ƙuri'arsu a ranar zaɓe.
Adadin matasan da ke yin rajistar zaɓe ya ci gaba da ƙaruwa. A lokacin aikin sabunta rajistar masu kaɗa ƙuri'a na shekarar 2026, INEC ta ƙara sabbin masu rajista 2,782,589 a kan mutum 93,469,008 da suka kasance cikin rijistar zaɓen 2023.
Hakan ya sa jimillar masu rajistar zaɓe a ƙasar ta kai mutum 96,251,597 zuwa watan Janairun 2026.
Daga cikin sabbin masu rajistar, kusan kashi 69 cikin 100 matasa ne.
Sai dai a tarihance, yawan yin rajistar zaɓe ba koyaushe yake nufin yawan fitowar masu kaɗa ƙuri'a ba. Hakan na da nasaba da dalilai da suka haɗa da tashin hankalin da ke tattare da zaɓe, rashin sha'awar shiga harkokin siyasa da kuma rashin amincewa da tsarin gudanar da zaɓe.
Yayin da Najeriya ke shirin sake gudanar da zaɓe a 2027, ana sa ran yadda matasa za su fito domin amfani da haƙƙinsu na zaɓe zai iya taka muhimmiyar rawa wajen ƙayyade makomar siyasar ƙasar.
Dalilin da ya sa duniya ke sanya ido kan zaɓen Najeriya
Zaɓen Najeriya na shekarar 2027 na da muhimmanci ba ga ƙasar kaɗai ba, har ma ga maƙwabtan ta da sauran sassan duniya.
A matsayinta na ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka kuma ɗaya daga cikin manyan tattalin arzikin nahiyar, duk wani rikicin siyasa a Najeriya na iya yin tasiri ga harkokin kasuwanci, ƙaurar jama'a, tsaron yankin da kuma saka hannun jari a Afirka ta Yamma da sauran wurare.
Masanin tattalin arziki, Boniface Chizea, ya ce girman Najeriya da tasirinta na nufin cewa duk wata doguwar matsalar rashin kwanciyar hankali za ta shafi fiye da iyakokin ƙasar.
Ya ce: "Najeriya ƙasa ce mai muhimmanci ta fuskar dabarun siyasa da tattalin arziki. Muna da al'umma sama da miliyan 200. Ba kasafai ake samun ƙasashe masu yawan jama'a ko faɗin ƙasa irin na Najeriya ba. Saboda haka idan aka samu rikicin siyasa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma mutane suna tserewa daga ƙasar a matsayin 'yan gudun hijira, hakan zai girgiza yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya. Haka kuma zai yi tasiri ga sauran sassan duniya, kamar yadda ake gani a halin da ake ciki yanzu a Iran."
Sai dai ga 'yan Najeriya, abin da ke gaban su ya fi kusanci da rayuwarsu ta yau da kullum.
Shekaru huɗu bayan zaɓen da suka yi a 2023, suna komawa rumfunan zaɓe ne a cikin ƙasar da ta samu sauye-sauye ta fuskar siyasa, tattalin arziki da zamantakewa.
Yayin da suke shirin kaɗa ƙuri'arsu a shekarar 2027, akwai wata muhimmiyar tambaya da mutane da dama za su yi wa kansu:
Shin rayuwarsu ta inganta a yau idan aka kwatanta da lokacin da suka kaɗa ƙuri'a a shekarar 2023?