Ƙasashe 10 da suka fi samar da man fetur a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ake ƙara nutsawa a cikin yaƙi tsakanin Amurka da Isra'ila da kuma Iran, ƙasashe masu samar da mai a duniya na ƙara zama wasu 'yan lele a idanun marasa man.
Hakan ya biyo bayan matakin da Iran ta ɗauka na rufe mashigar Hormuz wadda take iko da ita, wata mashiga da ake safarar kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas da ake amfani da shi a duniya, kuma an samu raguwar man da ake bi da shi ta mashigar da kashi 95 cikin ɗari.
Wannan dai ya janyo tashin farashin man fetur da wasu dangoginsa da ake amfani da su kuma suke ratsawa ta mashiga, nauyin man Brent ya ta shi zuwa dala 120 kamar yadda jaridar INN ta wallafa.
Wannan ya sa BBC Hausa ta rubuta wannan maƙala domin nazari kan ƙasahen duniya 10 da suka fi samar da man fetur da sauran nau'o'insa a duniya.
Amurka - ganga miliyan 22
Sama da shekara bakwai a jere Amurka ce ke jan ragamar kasuwar duniya wajen fitar da man fetur, inda tae samar da sama da ganga miliyan 22 a kowacce rana.
Amurka a gefe guda kuma tafi kowacce ƙasa buƙatar man fetur ɗin saboda yawan al'ummar da take da su da waɗanda suke bayuwa zuwa ga yawan buƙatarsa.
Jihar Texas ce ke kan gaba cikin jihohin Amurka wajen samar da man fetur ɗin da kuma tazara mai nisa tskaninta da New Mexico ta biyu, inda take samar da ninki uku na abin da New Mexico ke fitarwa a kullum.
Saudiyya - ganga miliyan 10

Asalin hoton, Reuters
Saudiya ce ƙasar da take samar da kimanin kashi 17 na man fetur da ake ajiyewa a matsayin na ko ta kwana a duniya.
Itace ƙasar da ta fi fitar da man fetur zuwa kasuwa duniya, tana samar da ganga miliyan 10.88 a kowacce ranar.
Wannan ya sa ta zama mai yanke makomar hukunce-hukunce da matakan da ake ɗauka a Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC.
A 2022, sai da ƙawar ta Amurka ta so ta ƙara yawan gas ɗin da take fitarwa kasuwar duniya domin sauƙaƙa farashi a kasuwar.
Rikicin Iran da Amurka da Isara'ila ya tilastawa Saudiyya rage yawan man fetur ɗin da take samarwa daga miliyan 10 zuwa takwas, saboda rufe mashigar Hormuz da ake fitar da man fetur ɗin ta nan.
Rasha - gamga miliyan 10
Rasha ma na samar da ganga sama da miliyan 10 a kowacce rana, kuma tana ɓoye mafi yawan man fetur ɗin da take samarwa ne a West Siberia tsakanin tsaunikan Ural da ke yankin Urals-Volga da kuma har zuwa wajen tekun Caspian domin faɗaɗa iko.
Yanayin kasuwanci ta ya fuskanci koma baya tun lokacin da ta fara yaƙi da Ukraine, Ƙungiyar Tarayyar Turai EU da ta ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziki a duniya G7 da kuma Australia sun sanya wa Rashan takunkumin fitar da man fetur ɗinta.
Gabanin fara yaƙin wajen shekarun 2021, ƙasashen turai ne ke sayan kimanin kashi 20 cikin ɗari na man fetur ɗin da Rasha ke samarwa, amma bayan fara yakin kason ya dawo kasa da 6.
China da India yanzu sune manyan masu sayan man fetur ɗin Rasha, inda suke sayan kashi kusan 92 na man fetur ɗin da Rasha ke fitarwa.
Canada - ganga miliyan 5
A 2024, yawan man da Canada take samarwa ya kusa ganga miliyan 6, inda take samar da ganga miliyan 5.997 a kullum, daga 237,000 da take iya samarwa a 2023.
Kusan duka rumbunan da take ajiye man fetur ɗin da take samarwa suna yankin Alberta.
Mafi yawan man fetur ɗin da Canada ke fitarwa tana fitar da shi ne zuwa Amurka, inda rahotanni suke ce a 2023 kashi 60 cikin 100 na abin da take samarwa ana shigar da shi Amurka ne, dan an kwatanta da 2013 da Amurkan ke bukatar kashi 33 kacal cikin 100.
Ana sa ran Canada za ta ƙara yawan man da take samarwa da ganga 140,000 a wannan watan na Afrilun 2026, a wani mataki na amfani da matatar ta garin Ottawa domin ƙara yawan man da ake samarwa zuwa ganga miliyan 23.6.
China - ganga miliyan 5
China na samar da ganga miliyan 5.33 a kowacce ranar bisa ga alƙaluman da aka fitar a 2024.
An yi ƙiyasin cewa China ce ƙasa ta biyu da ta fi buƙata tare da amfani da man fetur a duniya, a 2014 ta zama ta ɗaya da a wayan sayan man fetur a dunida.
Saboda yawan al'umarta da kuma habbbakar da tattalin arziƙinta yake yi a sannu, shi ya sa ta zama wacce ta fi buƙatar makamashi a duniya.
Ta zama ta ɗaya ne a duniya saboda tana shigar da mai ganaga miliyan 11 a kowacce ranar zuwa cikinta.
Kimanin kashi 70 cikin 100 na man da take saya tana karba ne daga kasashen da ke mambobin OPEC su Rasha Saudiyya da kuma Iraƙi.
Dan haka ba za a yi mamaki ba idan buƙatar makamashin China ta sauya kasuwar duniya, musamman a yanzu da aka rufe mashigar Hormuz.
Iran - ganga miliyan 4.5
Iran ita ce ƙasa ta shida cikin jerin ƙasashen da ke samar da man fetur, a 2024 yawan abin da take fitarwa yakai ganga 4.62 a kowacce rana, wannan wani gagarumin ci gaba ne da ta samu, idan aka kwatanta da ganga miliyan 3.66 da take fitarwa a 2023.
Da wannan ƙarin da ta samu ta zama ta biyu cikin jerin ƙasashen ƙungiyar OPEC da ta fi fitar da man zuwa kasuwar duniya.
A cewar Hukumar bayar da bayanai kan makamashi EIA Iran ce ta uku a duniya da take da majiyin man fetur mai girma, ta biyu kuma wajen rumbun ma'adanin gas da ke ƙasa.
Mafi yawan man da ta fitar da ya kai ganga 1.4 a shekarar 2023 ta sayar da shi ne ga China.
Yaƙin da Iran ke yi da Amurka da Isra'ila ya sa ta rufe mashigar Hormuz mai muhimmanci, wata hanya da ake hada-hadar kashi 20 cikin 100 na man fetur da gas ɗin duniya ta cikinta.
UAE - ganga miliyan 4.5
Cikin sama da shekara 10 UAE ta kasance cikin manyan kasashen da suke samar da mai guda 10 a duniya.
Ƙasar da take cikin mambobin OPEC na samar da man fetur ganga miliyan 4.51 a mafi ƙaranci a kullum a shekarar 2024 kamar yadda rahotanni suka bayyana,
Kasar tana da wurin ajiyar rarar mai da zai ɗauki ganga bilyan 111, kuma mafi wayawan wuraren suna babban birninta Abu Dhabi.
A watan Mayun 2024 ne kamfanin mai na Abu Dhabi ya sanar da ƙarfin samar da ɗanyan man kasar zuwa ganga miliyan 4.85, yana cikin shirinta adadin ya kai miliyan biyar nan da 2027.
A cewar wasu rahotanni, hare-haren jiragen marasa matuƙa da aka riƙa kai wa kan manyan masana'antu da wurare masu mahimmanci da ke da alaƙa da kasuwancin mai da kuma rufe mashigar Hormuz ya ja UAE ta rage yawan man da take samarwa a kullum da kusan rabi.
Iraƙi - ganga miliyan 4.5
Itama wata mamba ce a OPEC, a 2023 tana samar da man da ya kai ganga miliyan 4.44 a kullum amma a 2024 sai aka samu ƙari duk da dai bai kai ya kawo ba.
A 2024 ne Iraƙi ta sauka daga matsayin mambar OPEc ta biyu da ta fi fitar da man fetur zuwa kasuwar duniya, inda Iran ta sha gabanta.
Bayanan da OPEC ta fitar a 2023 sun ce Iraƙi na da wurin ajiyar rarar mai da zai ɗauki ganga biliyan 145.02, wanda hakan ya kai kashi 11 na ma'ajin rarar da ake da shi a duniya.
Rikicin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka ya janyo koma baya ga kasuwar man fetur din Iraƙi a watan Maris da ya gabata.
Brazil - ganga miliyan 4
Kasuwar man feturin Brazil a 2024 tana samar da ganga miliyan 4.28, kusan kowacce shekara ba a wani samun gagagrumin sauyi.
A cewa IEA buƙatar makamashin Brazil ta ninka cikin shekara 10 da suka gabata saboda bunƙasar tattalin arzikinta mai ɗorewa.
Inda ya fi ɗaukar kaso mai yawa na makamashin Brazil shi ne man fetur sai kuma ɗanyen mai da sannan gas da kuma lantarki.
A na sa ran Brazil za ta iya sama ta huɗu a duniya da ta fi fitar da mai kasuwar duniya nan da shekaru masu zuwa.
A 2024 man fetur ɗin ƙasar ya taimaka sosai wajen haɓɓakar safarar mai a duniya baki ɗaya.
Kuwait - ganga miliyan 2.78
Ta ƙarshe a cikin jerin ƙasashen da suke samar da man fetur ita ce Kuwait, wadda take samar da ganga miliyan 2.78 a kullum a 2024.
ƙasar ta yi ta fama wajen ganin ta dawo samar da ganga miliyan 3.5 saboda jan ƙafar da aka samu wajen saboda siyasar cikin gida.
Bangaren man ƙasar ne ke samar da kashi 50 na bunkasar tattalin arzikinta a alƙaluman duniya, kuma da smaar mata kuɗin shhiga da ya kai kashi 90.
Ƙara samun wani man da aka yi a ƙasar ya ƙara baiwa ƙasar kwarin gwiwar habbakar tatalin arzikinta a shekaru masu zuwa.
Wane matsayi Najeriya take?
Najeriya ce a matsayi na 11 cikin jerin ƙasashen duniya mafiya arzikin man fetur a duniya.
Wasu alƙaluma daga Hukumar Makamashi da Duniya, (EIA) ta fitara a 2024 sun nuna cewa ƙasar na da yawan man fetur a ya kai kimanin ganga biliyan 37 a ƙasa.
Ƙasar ce kan gaba a yawan arzikin man fetur da fitar da shia duniya, kodayake tana bayan Libya a wayan man da ke jibge a ƙarƙashin ƙasa.
Man fetur na Najeriya - wadda mamba ce a ƙungiyar Opec, ta ƙasashe masu arzikin man fetur - na daga cikin na gaba-gaba mafiya inganci a duniya, don yake cikin mafiya daraja a kasuwar man fetur.









