Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Talata 7/4/2026
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 7 ga watan Afrilun 2026.
Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi, Abdullahi Bello da Muslim Muhammad Yusuf
Isra'ila ta ce ta kai hare-hare kan layukan dogo da gadoji a Iran
Asalin hoton, RONEN ZVULUN/POOL/EPA/Shutterstock
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce sojojin ƙasarsa sun kai hare-hare kan layukan dogo da gadoji a Iran.
Da fari dai rundunar sojin Isra’ila ta gargaɗi fararen hula a Iran da su guji tashoshin jirgin ƙasa da layukan dogo a yau.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kai hare-hare kan sassan gadoji guda takwas da rundunar sojin Iran ke amfani da su wajen jigilar makamai da kayan yaƙi.
Kafafen watsa labaran Iran sun ce an kai hari kan wata gadar jirgin ƙasa a Kashan, inda aka kashe mutum biyu, sannan an sake kai hari kan wata gada ta daban a kusa da birnin Qom.
Gwamnatin Kuwait ta buƙaci jama'a su zauna a gidajensu a daren yau
Gwamnatin Kuwait ta buƙaci ƴanƙasar da su guji fita daga karfe 12:00 na dare zuwa 06:00 na safiyar gobe.
Ma'aikatar cikin gida ta wallafa wata sanarwa a shafinta na X cewa "ana kira ga 'yan ƙasa da su kasance a cikin gidajensu sai dai idan ya zama dole".
Ya ce "an ɗauki matakin ne domin samar da tsaro, da tabbatar da kwanciyar hankali" a yankunan ƙasar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ya yi barazanar shafe Iran, idan wa'adin da ya ba ta ya cika ba ta buɗe mashigin Hormuz ba.
Firaministan Pakistan ya buƙaci Trump ya ƙara wa'adin da ya ba Iran
Asalin hoton, Reuters
Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya buƙaci shugaban Amurka Donald Trump da ya ƙara wa'adin da ya ba Iran da makonni biyu "domin ba da damar tattaunawar diflomasiyya".
Ya kuma buƙaci Iran ta bude mashigin Hormuz.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, ya ce: "Ana ci gaba da tattaunawar diflomasiyya don sasanta yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya, da yiwuwar samun sakamako mai kyau.
“Domin samun damar diflomasiyya, ina roƙon Shugaba Trump da ya kara wa’adin da makonni biyu.
"Pakistan na bukatar 'yan'uwanmu Iran da su bude mashigin Hormuz na tsawon makwanni biyu."
"Haka kuma, muna kira ga dukkan bangarorin da ke rikici da juna da su tsagaita bude wuta a ko'ina na tsawon makwanni biyu don ba da damar tattaunawar diflomasiyya da za ta kai ga kawo karshen yakin, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin."
Fafaroma ya yi alawadai da barazanar Trump kan Iran
Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Leo ya ce barazanar Trump ga Iran abu ne sam da "bai dace ba".
Trump dai ya yi barazanar "shafe duk wani ci gaba na Iran" idan har wa'adin da ya ba ta ya cika ba ta buɗe mashigin Hormuz ba.
Fafaroman wanda shi ma Ba'Amurke ne, a yayin hira da manema labarai ya yi alawadai da matakin.
Ya buƙaci ƙasashen duniya su sa baki domin dakatar da yaƙin da ake yi.
'Trump kaɗai ya san matakin da yake shirin ɗauka kan Iran idan wa'adi ya cika'
Asalin hoton, Getty Images
Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House, Karoline Leavitt ta ce Donald Trump ne kaɗai ya san abin da zai yi idan wa'adin da ya gindaya wa Iran na bude mashigar ruwan Hormuz ya ƙare.
Bayanin nata na zuwa ne bayan da BBC ta buƙaci ƙarin haske game da kalaman da shugaban Amurka Donald Trump da mataimakinsa JD Vance suka yi.
Kamar yadda muka ruwaito a ɗazu, Vance ya ce sojin Amurka "za su yi amfani da wasu makamai da har yanzu ba su yi amfani da su ba", idan wa'adin da Trump ya ba su ya ƙare.
Shi ma Trump ya yi barazanar "shafe duk wani ci gaba da Iran ta samu"
Hakan ne ya sa wasu ke tunanin ko za a yi amfani da makamin nukiliya ne kan Iran ɗin.
BBC ta tuntuɓi gwamnatin kan matsayinta kan zargin amfani da makaman kare dangi, fadar White House ta bakin Leavitt ta ce: "Gwamnatin Iran tana da har zuwa karfe 8 na yamma agogon Gabashin kasar ta gana da Amurka. Shugaban kasa ne kadai ya san abin da ya ke shirin aikatawa a kai."
Iraniyawa sun fantsama kan tituna da wuraren da Trump ya ce zai kai hari
Asalin hoton, TASNIM
Yayin da wa'adin da shugaban Amurka Donald Trump ya baiwa Iran na sake bude mashigin Hormuz ke gabatowa, rahotannin sun ce magoya bayan gwamnatin Iran sun fantsama kan tituna tare da yin tattaki a wasu tashoshin wutar lantarki.
Gidan talabijin na kasar Iran, ya watsa wasu faifan bidiyo na magoya bayan gwamnati rike da tutar jamhuriyar musulunci ta Iran.
Wasu hotunan kuma na nuna magoya bayan gwamnati a kusa da tashoshin wutar lantarki na Iran.
Asalin hoton, TASNIM
Kafofin yada labarai a Iran sun ce mutanen sun taru a gaban tashoshin wutar lantarki na Neka, Mashhad, da Tabriz da dai sauransu.
Da ma Trump ya ce zai kai hari kan cibiyoyin makamashin Iran tare da shafe tarihinta, idan ƙasar ba ta buɗe mashigin Hormuz ba.
Asalin hoton, FARS
Sojojin Isra'ila sun gargaɗi jiragen ruwa a gabar tekun Lebanon
Dakarun tsaron Isra'ila (IDF) sun aike da gargaɗin gaggawa ga jiragen ruwa a tekun Tire da Ras Naqoura da ke ƙasar Lebanon.
A cikin wata sanarwa da kakakin IDF Avichay Adraee ya fitar a shafin X, ya ce ƴan Hizbullah na jefa jiragen ruwa cikin haɗari, kuma za su ɗauki mataki.
Ya wallafa wasu hotunan taswira, inda ya buƙaci jiragen su sauya akalar tafiyarsu zuwa arewaci.
Amurka ba ta da niyyar amfani da nukiliya kan Iran - Fadar White House
Asalin hoton, EPA
Fadar White House ta yi ƙarin haske kan kalaman da mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya yi game da ɗaukar matakin soji a kan Iran.
Ta ce kalaman na sa ba su nufin ƙasar za ta yi amfani da makamin nukiliya kan Iran ɗin.
Wannan na zuwa ne bayan da Vance ya ce sojin Amurka "za su yi amfani da wasu makamai da har yanzu ba su yi amfani da su ba", idan wa'adin da Trump ya ba su ya ƙare.
Sai dai a wani bayani da fadar White House ɗin ta wallafa shafinta na X, ta ce "kalaman na sa ba abin da suke nufi ba kenan".
Tana mayar da martani ne kan wani mai amfani da shafin X, ya yi zargin cewa kalaman na Vance na zargin yiwuwar amfani da makamin nukiliya kan Iran.
Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata cewa jami'anta na sayen kayan sarki da kuɗinsu
Asalin hoton, AFP
Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata zargin da wani tsohon jami'inta Rotimi Olamilekan, ya yi na cewa sojojin ƙasar da kuɗin aljihunsu su ke sayen kayan sarki da sauran kayan aiki.
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna yadda tsohon soja da aka sallama daga aiki yake nuna damuwa kan halin da ya ce sojin ƙasar ke ciki da rashin samun kulawar da ta kamata.
Sai dai a wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran rundunar sojin ƙasa na Najeriya, Appolonia Anele, ya fitar, ta ce iƙirarin ba gaskiya ba ne, inda ta jaddada cewa ana samar da kayan aiki yadda ya kamata ga jami'an.
Bayanin na zuwa ne bayan da aka sallami jami'in da ake kira da Soja Boi, sakamakon ɓullarsa a wani bidiyo da ya ke kira ga manyan ƴansiyasa a ƙasar su sanya ƴaƴansu aikin soji, da kuma yadda ya koka kan halin ko in kula da ake nuna musu.
A cikin hrar da aka yi da shi ya ce, tun daga kan takalmin da suke sanyawa, da kayan sarki, da hular kwano da rigar kariya daga harsashi, sai dai su saya daga albashinsu.
Game da batun albashi, rundunar sojin ta ce akwai albashi wadatacce da kuma wasu alawus-alawus da ake ba jami'an.
Amma ta ce, wasu jami'an na da damar amfani da kuɗinsu wajen sayen wasu kayayyakin da suke buƙata amma sai idan su ne suka ga damar yin hakan.
Rundunar ta buƙaci jama'a su yi watsi da zarge-zargen da ta ce suna ƙoƙarin rage ƙwarin gwiwa ne kawai da kuma aibu ga tsaron ƙasa.
An kashe ɗan bindiga a harin kusa da jakadancin Isra’ila a Turkiyya
Rahotanni daga Turkiyya sun ce an kashe wani ɗan bindiga, yayin da wasu biyu suka jikkata a wata musayar wuta da ta auku kusa da ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Santanbul.
Ministan harkokin cikin gidan Turkiyya, Mustafa Çiftçi ya ce an gano waɗanda suka kai harin, yana mai kiran su da sunan yan ta’adda. Rahotanni sun ce aƙalla ‘yan sanda biyu sun jikkata.
A sanarwar da wasu hukumomin ƙasar suka fitar, sun ce an ƙaddamar da cikakken bincike kan lamarin.
Babu jami’ai a ofishin jakadancin Isra’ila a lokacin, bayan dakatar da ayyukan su sakamakon harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar bakwai ga watan Oktobar 2023.
Ɗalibai 238 da malamai 49 sun mutu sakamakon hare-hare a Iran
Ma’aikatar Ilimi ta ƙasar Iran ta bayyana a sabon rahotonta cewa, tun bayan fara yaƙin da ke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran, an kashe ɗalibai 238 da malamai 49, tare da wasu sabbin dalibai guda 7 da su ma suka rasa rayukansu.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa, dalibai 178 da malamai 24 ne kuma suka jikkata sakamakon hare-haren.
Rahoton ya nuna cewa, an kai hare-hare kan makarantu 764 a faɗin ƙasar, inda mafi yawansu suke a yankunan Tehran da Kermanshah.
A cewar Ma’aikatar Ilimin, hare-haren da aka kai kan wuraren fararen hula ne suka haddasa mutuwa da jikkatar wannan adadi na dalibai da malamai.
Gwamnatin Najeriya za ta kashe biliyan 135 kan shari’o’in bayan zaɓen 2027
Asalin hoton, @aonanuga1956/X
Gwamnatin Najeriya ta ware naira biliyan 135.22 domin shari’o’in da suka shafi bayan zaɓen 2027.
Wannan buƙatar na daga cikin abubuwan da aka tattauna a zaman majalisar tarayyar ƙasar a ranar 31 ga watan Maris, 2026 a lokacin da aka karɓi rahoton kasafin kuɗin 2026.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, gwamnatin ƙasar ta sanya wannan buƙatar a cikin kasafin kuɗin, inda suke cikin rukunin kuɗaɗen da ake kashewa na ko ta kwana, amma ba a alaƙanta su da ko wace ma'aikata ko hukuma ba.
Masana tattalin arziki da shari’a sun bayyana cewa irin wannan tanadi yana nuna cewa gwamnati na tsammanin matsin lamba daga shari’o’in da suka shafi zaɓe, ciki har da sasanta rikice-rikice da sauran tsarin gudanarwa da ke biyo bayan zaɓuka.
A shekarar 2027 ne za a gudanar da manyan zaɓukan ƙasar na shugaban ƙasa, da ƴanmajalisa da gwamnoni a wasu jihohin ƙasar saboda ƙarewar wa'adin mulkinsu.
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya soki Turai kan yaƙin Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya yi kakkausar suka ga shugabannin yammacin Turai, yana mai cewa sun gaza dakatar da yaƙin Ukraine.
JD Vance ya ce da Trump ya kasance shugaban Amurka shekaru 4 da suka gabata da ba za'a taba kama hanyar shiga yaƙin ba.
Ya kuma zargi shugabannin da tsoma baki a zaɓen da ke tafe a Hungary.
Vance dai na gudanar da ziyara a birnin Budapest, inda ya bayyana tare da Firaministan ƙasar, Viktor Orbán.
An dakatar da sufurin jiragen ƙasa a Khuzestan da ke Iran
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce an dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa a lardin Khuzestan, yayin da ake ƙara fargabar hare-haren soji a ƙasar.
Sa’o’i kaɗan da suka gabata, gwamnan birnin Mashhad ya bayyana cewa, “saboda gargaɗin da Isra’ila ta bayar wanda bai dace ba” na kai hari kan layukan jirgin ƙasa na ƙasar, an soke dukkan tafiye-tafiyen jiragen ƙasa daga tashar Mashhad har sai wani lokaci na gaba, domin kauce wa haɗari.
Tun da farko, rundunar sojin Isra’ila ta gargadi ‘yan ƙasar Iran da su guji amfani da jiragen ƙasa ko kusantar layukan dogo a faɗin ƙasar.
A wasu sassan Iran, musamman a kudancin Tehran, layukan jirgin ƙasa na kusa da gidajen jama’a, lamarin da ke ƙara haddasa fargaba.
Hare-haren soji sun lalata gadar jirgin ƙasa a kudancin Tehran
Rahotanni daga kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa an kai hare-haren soji kan wata gada da jirgin ƙasa ke bi a birnin Rey, da ke kudancin Tehran.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ce wannan gada ita ce kaɗai ke ratsa kogin Sorkheh-e-Hisar a yankin.
Rahotannin sun kuma nuna cewa hare-hare kan wasu gadoji a sassan Iran sun fara ne tun wasu sa’o’i da suka gabata.
A halin yanzu, kafofin yaɗa labaran Iran sun fitar da hoton gadar Hashtrood-Tabriz, wanda ke nuna irin ɓarnar da harin na yau ya janyo.
'Mun kai wa kamfanin sarrafa sinadaran man fetur na Amurka a Saudiyya hari'
Asalin hoton, Getty Images
Dakarun juyin juya hali Iran sun ce sun kai hari kan manyan kamfanonin sarrafa sinadaran man fetur mallakin Amurka da ke Saudiyya, ciki har da cibiyoyi a yankin Jubail da Al-Juaimah, a matsayin martani ga harin da aka kai kan masana’antar Asaluyeh.
Sanarwar ta ce a jerin hare-haren Iran karo na 99”, an kai hare-hare da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki kan sansanonin Amurka da kadarorinta a yankin Tekun Farisa da mashigar Hormuz, da kuma cibiyoyin tsara kai hare-hare a Isra’ila.
Dakarun sun bayyana cewa harin na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya kan abin da suka kira hari kan “ kamfanin sarrafa sinadaran man fetur da ke Asaluyeh”.
Sun ƙara da cewa a matakin farko na harin, sun nufi manyan cibiyoyin sarrafa sinadaran man fetur da suka hada da na kamfanonin Amurka irin su ExxonMobil da Dow Chemical Company da kuma Chevron Phillips Chemical, inda aka ce an kai musu hari da makamai masu linzami.
Dakarun sun kuma yi gargaɗin cewa idan sojojin Amurka suka tsallake iyakar da suka gindaya, martanin da za su mayar zai wuce yankin Gabas ta Tsakiya.
Sanarwar ta ce za su yi aiki kan lalata cibiyoyin samar da mai da iskar gas na Amurka da ƙawayenta domin hana su anfani da albarkatun yankin na tsawon shekaru.
Sun kuma gargadi kawayen Amurka a yankin da cewa a baya sun nuna hakuri saboda kyakkyawar makwabtaka, amma yanzu sun cire duk wani sharadi wajen zabar wuraren da za su kai hari.
Dakarun sun ƙara da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai hare-hare har ma da wuraren fararen hula idan rikicin ya ƙara ƙamari.
Idan Amurka ta wuce gona da iri, martaninmu zai wuce yankin Gabas ta Tsakiya - Iran
Asalin hoton, Tasnim news agency
Rundunar juyin juya halin Iran ta yi gargaɗin cewa idan Amurka ta wuce gona da iri da hare-haren da take kai wa, martanin da za ta mayar zai wuce iya kan yankin Gabas ta Tsakiya kawai.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa ta kafafen yaɗa labaran gwamnati, rundunar ta ce duk da rikicin da ake ciki, ta nuna juriya sosai tare da yin taka-tsantsan wajen zaɓen wuraren da take kai hare-haren ramuwar gayya kan Amurka da ƙawayenta a yankin.
Sai dai ta ƙara da cewa daga wannan lokaci, za ta ajiye irin waɗannan la’akari, tana mai gargadin cewa idan sojojin Amurka suka wuce gona da iri, martanin Iran zai haɗa da kai hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa na Amurka da ƙawayenta, tare da kawo cikas ga samar da mai da iskar gas a yankin na tsawon shekaru.
Isra'ila ta yi barazana wa sufurin jiragen ƙasa na Iran
Sojojin Isra’ila sun yi barazana wa sufurin jiragen ƙasa a Iran, inda suka gargaɗi ‘yan Iran da su guji amfani da jiragen ƙasa ko yin tafiya a fadin ƙasar saboda hatsarin rayuwa.
Wannan gajeriyar sanarwa, wadda sojojin Isra’ila suka wallafa a harshen Farsi a X, ta ce: “Kasancewarku a kan jiragen ƙasa ko kusa da layukan jiragen ƙasa na sanya rayukanku cikin haɗari.”
A wasu sassan Iran, ciki har da Tehran ta Kudu, layukan jiragen ƙasa suna kusa da yankunan da ake zama.
Ranar ƙarshe da Donald Trump ya sanya wa Iran don bude mashigar Hormuz za ta cika cikin ƙasa da awanni 24, kuma ya ce zai kai hari kan kayan more rayuwa, ciki har da gadaje.
Kakakin majalisar dokokin Jihar Kebbi ya rasu
Asalin hoton, Audi Photography
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Right Hon. Muhammad Usman Ankwai.
Ɗan majalisar mai wakiltar yankin Zuru ya rasu ne a ƙasar Masar bayan fama da jinya, kamar yadda akawun majalisar Suleiman Shamaki ya tabbatar.
Cikin saƙon ta'aziyyae da gwamnan jihar ya fitar, ya bayyana kaɗuwarsa kan rasuwar mutumin da ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan gwamnatin jihar.
''Ya kasance jagora mai ƙoƙari, ɗan kishin ƙasa na gaskiya da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimta wa al'umma, haƙiƙa ba za mu manta da ƙwarewarsa ba wajen ciyar da jiharmu gaba'', in ji shi gwamnan.
Hon Ankwai ya rasu ya bar matarsa ɗaya da ƴaƴa biyar.
Amurka ta yi asarar aƙalla jiragen yaƙi tara a yaƙin Iran
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Amurka ta yi asarar aƙalla jiragen yaƙi tara a yaƙin da take yi da Iran zuwa yanzu, bisa binciken hotuna da sanarwar hukumomi, da bayanai daga kafofin watsa labaran Amurka.
CBS News ta ruwaito a ranar 5 ga Afrilu cewa Iran ta lalata jirage guda biyu ƙirar F-15E da aka tura don taimakawa aikin ceto. Hotuna da aka tabbatar sun nuna ɓirɓishin jiragen na hayaƙi a tsakiyar Iran.
A ranar 3 ga Afrilu, Iran ta kakkaɓo tare da harbe jirgin yaƙin Amruka ƙirar F-15E Strike Eagle a saman tsakiyar ƙasar. A wannan rana, New York Times ta ruwaito cewa wani jirgi ƙirar A-10 Warthog ya faɗi a tekun Gulf, matukin sa ya tsere, sannan daga baya aka ceto shi.
Hotuna da aka tabbatar a ranar 29 ga Maris sun nuna jirgin E-3 Sentry ya lalace a sansanin jirgin saman Prince Sultan a Saudiyya, bayan rahotannin harin Iran.
A ranar 12 ga Maris, mutane shida da ke jirgin yaƙin Amurka ƙirar KC-135 sun mutu a yammacin Iraq bayan ya faɗi, in ji babbar cibiyar ayyukan sojin Amurka (Centcom). Ana binciken dalilin faduwar, amma Centcom ta ce ba harin abokan gaba ba ne.
A ranar 2 ga Maris, jiragen Amurka ƙirar F-15E guda uku sun rikito a sararin samaniyar ƙasar Kuwait a abin da Centcom ta bayyana a matsayin “abin da ake zargin kuskure ne daga dakarun ƙawance.” Duk ma’aikatan jiragen guda shida sun kuɓuta lafiya, sashen tantance labarai na BBC Verify ya tabbatar da gaskiyar bidiyon da ke nuna jirgi guda ɗaya na F-15 yana jujjuyawa a lokacin da yake fadi ƙasa a yammacin babban birnin Kuwait.