Yadda jam'iyyun adawar Najeriya ke neman haɗa kai don barazanar da ke gabansu ta 2027

Obi da Atiku da Kwankwaso

Asalin hoton, BBC COLLAGE

Lokacin karatu: Minti 3

Manyan jam'iyyun hamayya a Najeriya, sun ce suna duba yadda za su hada kai don tunkarar kalubalen da ke gabansu kafin zaben 2027, a daidai lokacin da wasunsu ke zargin ana kokarin murkushe su.

Manyan Jam'iyyun adawar a Najeriya sun ce sun fara daukar matakai daban-daban domin ganin sun ja hankalin duniya da hukumomin da suka kamata, kan ikirarin nasu na cewa dumukuradiyyar Najeriya na cikin barazana.

Galibin jam'iyyun hamayya fitattu a kasar na fama da rikice-rikice na shugabanci, lamarin da ya sa ake hasashen ba lallai su iya wani katabus ba a zaben 2027.

Jam'iyyar hamayya ta ADC da PDP reshen shugabancin Tanimu Turaki sun ce babu wata barazana da za ta sa su kaurace wa zaben 2027 da ke tafe a kasar duk da bangarorin biyu na fuskantar shari'a a kotu.

A tattaunawarsa da BBC Dr Yunusa Tanko, wanda shi ne jagoran yakin neman zaben Peter Obi dan takarar jam'iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, kuma jigo a jam'iyar ADC a yanzu, ya ce sun shirya fuskantar yanayin da ke tunkarar su: ''Gaskiya za mu fito - mutane suna so su fito su yi gangami su ce ba su yard ba da wannan taku da ake neman yi a dakushe 'yan adawa.''

''Na biyu za mu yi kokari kuma mu karasa kotu kuma mu je mu nemi 'yancinmu a kotu.

''Na uku za mu kara danganawa da kasar waje da ko'ina mu fada musu abin da ake ciki.

''Na hudu za mu yi kokarin mu tabbatar cewa ita wannan jam'iyya ta samu tsayawa zabe ta yanda ya kamata. Kuma duk wata hanya da za mu bi mu tabbatar cewa mun kwato wa kanmu 'yanci za mu bi ta, domin irin wannan bi-ta-da-kullin da ake yi ba zai taimaka wa dumukuradiyya ba. Gurgunta ta yake so ya yi. Ana so a tabbatar ba mu da murya gabadaya.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jam'iyar PDP ma da ake ganin tana fama da rikicin shugabanci, tana ganin wannan shi ne lokacin da ya fi dacewa jam'iyyun adawar su hada kai waje guda idan har suna son kalubalantar gwamnatin kasar da kuma samun damar fidda 'yan takararsu a dukkan matakai.

Farida Abdullahi, ita ce mai magana da yawun PDPn bangaren Kabiru Tanimu Turaki, inda ta yi wa BBC bayani : ''Ya kamata jam'iyyun adawa gabadaya mu fito kanmu tsaye mu dumfari INEC, don muna ganin kamar INEC ya kamata tana zaman kanta ne, amma abin da muke ganin tana yi kamar ba mai zaman kanta ba ce.''

''Idan ba mu fita, jam'iyyun adawa gabadaya mun hada kanmu ba, mun dumfari INEC ba suna so su yi mana wani abu da bai dace ba. Kuma na san muna da yakinin za mu zauna mu yi magana mu dumfari INEC saboda su tsaya su yi abin da ya dace.''

Dr Yunusa Tanko ya ce hadin kai a tsakaninsu a wannan yanayin da suke ciki, abu ne da ya zama wajibi:

''Kowace jam'iyyar adawa ta sani abin da ya faru da mu su ma zai iya samunsu, abin da ya faru da su mu ma zai iya samunmu. Amma idan aka samu sahihin zabe, dumukuradiyya kowa zai ji dadinta. To kuma mu sai mu zauna haka kawai muna kallo, mu bayi ne?''

Rikicin jam'iyyun adawa a Najeriya ya kara daukar hankali ne bayan wani mataki da hukumar zaben kasar, INEC ta dauka na cire shugabancin jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark, lamarin da 'yan adawar suka yi watsi da shi, tare da shan alwashin ci gaba da gudanar da babban taronsu da sauran al'amuransu yanda suka tsara.