Ko Iran ta yi wa Amurka da Isra'ila ba-zata?

Malami.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani malamin addini a Iran ya ziyarci gidan adana kayan tarihi na dakarun juyin juya-hali a Tehran ranar 12 ga Nuwambar, 2025.
    • Marubuci, Prabhat Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 6

Lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan Iran ranar 28 ga Fabrairun 2026, tambayar ita ce tsawon wani lokaci yaƙin zai ɗauka?

Yanzu lamarin ya wuce kwanaki, makonni zuwa watanni kuma babu alamar kawo karshensa nan kusa.

A ranar 31 ga Maris (Talata), wata guda da kwana uku da soma yaƙin, Donald Trump ya ce Amurka za ta fice daga Iran cikin "makonni biyu zuwa uku".

Abin da haka ke nufi shi ne, yaƙin ba zai kare nan take ba.

Tun da aka soma yaƙin, duk abubuwan da Trump ya yi fata ba su faru ba.

  • Duk da irin asara da ta samu, har yanzu Iran na ci gaba da yaƙi.
  • An ga yanda bambanci tsakanin Amurka da ƙawayenta na NATO ya fito fili dangane da yaƙin.
  • Iran ta yi wa Amurka illa sosai ta hanyar kai wa sansanonin sojinta hari a ƙasashen Gulf - kuma abin da ya fito fili shi ne ƙasashen ba su da kariya.
  • A cewar masana, dogaro da ƙasashen Gulf suka yi da Amurka na ba su tsaro ya ragu.
  • Rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi, ya janyo matsalar ƙarancin mai a faɗin duniya. A kan haka, ƙasashe da dama na matsa wa Amurka da Isra'ila lamba su kawo karshen yaƙin nan take.
  • A lokaci guda, Amurka ta zargi ƙawayenta irinsu Birtaniya, Faransa, Italiya, Sifaniya da kuma Canada da kin taimaka mata a yaƙin Iran.

Shin Amurka da Isra'ila na cikin matsin lamba?

Trump da Netanyahu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ƙasashen duniya da dama na sukar Amurka da Isra'ila. Nan lokaci ne da Trump da Netanyahu ke isa gidan shugaban na Amurka a Mar-a-Lago da ke Florida a watan Disambar, 2025.

Ƙari kuma shi ne, an kashe ƴanmata da dama a wani hari da aka kai wata makaranta a birnin Minab da ke Iran. Ƙasashe da dama, ciki har da Faransa, Jamus, Birtaniya, Italiya da kuma China sun yi alawadai da harin.

Wasu ƙasashe da dama su ma sun yi tir da Amurka da Isra'ila saboda kai harin, duk da cewa Amurka da Isra'ila ba su fito sun ɗauki alhakin kai harin ba.

Yanzu dai, sama da makonni huɗu sun wuce tun soma yaƙi, kuma yakin bai kare ba, an rufe mashigar Hormuz, sannan duniya na fuskantar matsalar ƙarancin mai. Duk da kashe mata shugaban addini, Iran na ci gaba da gwabza yaƙi kuma ta bayar da sharuɗan kawo karshen yaƙin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amurka da Isra'ila sun zama waɗanda ƙasashen waje ke suka a yanzu. Ana gudanar da zanga-zanga a cikin Amurka kanta don adawa da rikicin, sannan goyon baya ga Iran na karuwa a kasashe da dama.

Hakan na nuna cewa Iran ta yi nasara wajen jefa Amurka da Isra'ila cikin wani yanayi mara kyau, ta hanyar dabarun yaƙi da kuma diflomasiyya.

A cewar Happymon Jacob, wani ƙwararre kan harkokin ƙasashen waje, ya ce duka abubuwan da Amurka da Isra'ila suka shirya yi a farkon yaƙin, ba a yi duba a kansu yadda ya kamata ba.

Happymon ya faɗa wa sashen Indiya na BBC cewa, "Da farko, salon Trump da kuma kimarsa ita ce babbar matsala. Amfani da diflomasiyya a matsayin hanyar yaudara, cin zarafin shugaban kasa mai ci a bainar jama'a, tunanin cewa ƙawayen Amurka za su shiga yaƙin da ya fara, da kuma amfani da tattaunawar Geneva a matsayin uzurin far wa Iran, abubuwa ne da masu sharhi da dama suka yi biris da shi."

A cewar Jacob, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi imanin cewa yaƙin zai yi masa alfani a siyasar cikin gida, kuma idan shugaba ya ji irin haka, to ba ya ɗaukar matakai kamar sauran shugabanni idan suna cikin yaƙi.

Iran ta rufe mashigar Hormuz, wanda ya kawo nakasu sosai ga samar da mai a kasashen duniya da dama.

Zuwa yanzu dai Iran ɗin ta bar jiragen ruwa kalilan wucewa ta mashigar Hormuz daga wasu ƙasashen da ta zaɓa, ciki har da Indiya, China da kuma Pakistan. Wannan ya janyo ƙasashen nuna tausayawa Iran. Hakan kuma ya tayar da hankalin Amurka da Isra'ila.

Happymon Jacob ya ce, "Da farko an yi tunanin cewa Iran ba za ta yi barazana har ta rufe mashigar Hormuz ba saboda hakan zai shafi yanayin kasuwancinta ita ma. Sai ga shi ta rufe mashigar. Wannan mataki ba abin mamaki bane ga ƙasa irin Iran, wadda ke faɗa don ceto kanta da kuma ke kan wani aƙida na musamman."

Duk da rasa manyan jagororinta da kuma jami'ai, Iran na ci gaba da yaƙi kuma dabarunta sun kaɗa mutane, jawo rashin kwanciyar hankali da kuma damuwa ga ƙasashe da dama, a cewar masanin.

Shin Trump ya yi amai ya lashe?

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a shafinsa na Truth Social ranar 22 ga Maris cewa tattaunawa mai ma'ana na gudana tsakanin Amurka da Iran don kawo karshen yaƙi.

Masani kan tsare-tsare Brahma Chellaney ya rubuta a shafin X cewa, "Trump ya soma wannan yaƙi da burin tumɓuke gwamnatin Iran, sai dai bayan gaza yin haka, shi Trump da kansa yanzu yana tattaunawa da gwamnatin da ya ce zai kifar. Sannan yakinsa na ci gaba da janyo tsaiko ga tattalin arziki a duniya. Bijiro da batun cewa an gama gurgunta Iran sannan Amurka ta yi nasara a yaƙin zuwa ga cewa ana tattaunawa mai ma'ana da Iran yana a matsayin tamkar yin amai da kuma lashewa."

A ɗaya gefen, an buɗe wani sabon babi ranar Asabar, 28 ga Maris, wata ɗaya bayan fara kaddamar da yaƙi da Amurka da Isra'ila suka yi kan Iran.

A ranar Asabar, an harba makaman linzami daga Yemen zuwa cikin Isra'ila.

Hezbollah da ke Lebanon na ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila, abin da ya tilastawa Isra'ilar yin ramuwa. Isra'ila, ta yi ɓarna sosai a Lebanon ta hanyar amfani da ƙarfinta na soji, amma ta kashe kudaɗe sosai a ɓangaren soji.

Hamidreza Azizi, malami ne a cibiyar nazarin harkokin kasashen waje da ke Berlin. Ya rubuta littafi kan rikicin Iran na baya bayan-nan mai taken "Yadda Iran ta sake sauya dabarunta na yaƙi."

Ya yi magana sosai kan dabarin Iran.

Linzami.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani kwararre ya ce "Amurka da Isra'ila ba su taɓa tsammanin cewa Iran za ta kai har yanzu tana yaƙi ba." Nan wasu makaman linzami ne aka girke a gidan tarihi na dakarun juyin juya-halin Iran a Tehran

"Iran ta saka Amurka da Isra'ila sun ƙara yawan kuɗin da suke kashewa a yaƙin ta hanyar kai hari kan kayayyaki masu muhimmanci da makaman linzami da jirage marasa matuki," in ji Hamidreza.

Ya ce, "Dagan-gan Iran ta mayar da wannan yaƙi a matsayin na yanki. Iran ba ta kallon yakin a matsayin na ɓangarori biyu sai dai gagarumin rikici."

"Wannan ya ba ta dama kan Amurka da Isra'ila ganin cewa ana far musu daga wurare da dama irinsu Lebanin, Iraki da kuma yankin Gulf kuma dole ne su kashe kuɗaɗen soji zuwa ɓangarori da dama. Ta haka, Iran ta kuma kirkiro yanayi na rashin tabbas ga Amurka da Isra'ila kuma ba su san ta inda hari na gaba zai zo."

A cewarsa, tun da farko dabarun Iran ba yin nasara a yaƙin ba, illa gajiyar da Amurka da Isra'ila.

Ya ce, "Iran ba ta son a kawo karshen yaƙin nan take sai dai tana son ci gaba da matsin lamba kan ɓangaren soji, siyasa da kuma tattalin arziki na tsawon lokaci, saboda ɓangarorin da suke yaƙi da kasar su kashe ɗimbin kuɗaɗe ba ga su kaɗai ba har ma ga ƙawayensu."

Wani kwararre kan tsaro da tsare-tsare, C Uday Bhaskar, yayin tattaunawa da sashen Indiya na BBC ya ce, "Amurka da Isra'ila su kansu ba su yi tunanin cewa Iran za ta iya jure yaƙin har zuwa wannan lokaci ba. Trump ya ɗauka zai yi irin abin da ya yi a Venezuela a Iran. Sai dai mutuwar Ali Khamenei ta haɗa kan Iraniyawa baki ɗaya."

A cewarsa, Trump yana tunanin cewa ƴan kasar za su fito kan tituna don adawa da gwamnati, sai dai mutuwar Khamenei ta yi tasiri na daban.

Uday Bhaskar ya ce lokacin da Isra'ila ta far wa Iran a bara, Iran ta koyi darasi daga harin.

A cewarsa, "Iran ta rarraba makamanta da kuma jagoranci a faɗin ƙasar. Ta bai wa jami'ai ƴanci. An yi wani tsari na musamman na abin da za su yi ko da manyan jagororinsu ba su nan. Babu wani ruɗani a wajen ɗaukar mataki kuma Iran ta kai hare-harenta daga dukkan ɓangarori."

Bambanci tsakanin Amurka da ƙawayenta

Maasu zanga-zangar goyon Iran

Asalin hoton, Amid FARAHI / AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a wani gangamin goyon bayan Iran a Washington ranar 29 ga watan Maris, 2026

A ɗaya gefe, wani hari da Iran ta kai kan tankar mai mallakin Kuwait ranar Talata, 31 ga Maris, ya janyo ƙonewarta ƙurmus.

Wannan ya zo ne bayan gargaɗin Donald Trump cewa 'idan Iran ba ta amince da yarjejeniya ba sannan aka ci gaba da rufe mashigar Hormuz, to fa za a iya kai hari kan makamashin Iran, man ta da kuma cibiyoyin makamashinta.'

A ranar Talata, Trump ya zargi ƙasashe irinsu Birtaniya, Faransa, Sifaniya da kuma ƙungiyar NATO da kin taimakawa a yaƙin Iran, inda ya yi gargaɗin cewa 'Amurka za ta tuna da duka wannan.'

Ya kuma ce idan Birtaniya na son mai, ta tafi mashigar Hormuz ta tsara samun man ta.