Ko yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka za ta ɗore?

The remains of a damaged building in Tehran following an airstrike.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
  • Lokacin karatu: Minti 4

Cikin kwana ɗaya, Donald Trump ya tashi daga barazanar "shafe" tarihin Iran zuwa sanar da cewa sharuɗɗa 10 da Iran ta gabatar ''abubuwa ne da za a iya dubawa'' a sasancin da Pakistan ke shiga tsakani.

Da farko dai za a iya cewa tsagaita wutar wani muhimmin sassauci ne ga fararen hula a yankin Gabas ta Tsakiya waɗanda suka tsinci kansu a tsakiyar yaƙi tun bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran a ranar 28 ga watan Fabarairu.

Sai dai mutanen Lebanon ba su samu hakan ba. Bayan dagewa kan cewa yarjejeniyar ba ta shafi Lebanon ba, Isra'ila ta ƙaddamar da munanan hare-hare ta sama kan ƙasar.

To amma sauƙin da aka samu zai iya zama na wucin-gadi. Dukkanin ɓangarorin biyu - Iran da Amurka - na da ƙwararan dalilan kawo ƙarshen yaƙin.

To amma ra'ayoyinsu da suka bayyana ƙarara, sun yi hannun riga da juna.

Yanzu akwai tsawon mako biyu da waɗannan ɓangarori da ba su amince da juna ba, za su iya amfani da shi domin cimma matsaya.

Mataimakin shugaban Amurka J.D Vance ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mai "santsi". Wannan ne gaskiyar maganar.

Dukkanin ɓangarorin biyu na gindaya sharuɗɗan da ɗayan ɓangaren ba zai amince da shi ba, sannan dukkanin ɓangarorin na iƙirarin yin nasara.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya shaida wa manema labarai cewa "babbar nasara ce" Amurka ta samu kuma "mai cike da tarihi".

Ya ce "ƙasar da ke gaba wajen ɗaukar nauyin ta'addanci ta nuna gazawa wajen kare kanta da mutanenta da kuma faɗin ƙasarta".

Haka kuma ana samun saƙonnin samun nasara masu ƙarfi da ke fitowa daga Iran.

Mataimakin shugaban Iran Mohammed Reza Aref ya wallafa a shafin sada zumunta cewa "duniya ta samu wata babbar ƙasa mai ƙarfi a duniya, zamanin Iran ya fara."

Masu goyon bayan Shugaba Trump sun ce mummunar ɓarnar da Amurka da Isra'ila suka yi wa Iran ne ta tursasa mata amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta. Magoya bayan nasa sun ce kalaman da ya yi sun taka rawa wajen tabbatar da wanzuwar yarjejeniyar.

Barazanar da ya yi, in da ya aiwatar, za su iya haifar da laifukan take haƙƙin bil'adama.

A ɓangare ɗaya Iraniyawa sun yi amannar cewa dagiyar da gwamnatinsu ta nuna wa Isra'ila da Amurka, kasancewar ƙasar na da ƙarfin ci gaba da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da kuma toshe mashigar Hormuz, ya tursasa Amurka ta amince da yin sasanci bisa dogaro da sharuɗɗa 10 da ƙasar ta gabatar.

Sharuɗɗan sun ƙunshi abubuwa da yawa waɗanda zai yi matuƙar wahala Amurka ta amince da su, kamar yadda zai yi wahala ga Iran ta amince da wasu daga cikin sharuɗɗan Amurka.

Cikin sharuɗɗan akwai amincewa da ƙarfinta na yin iko da mashigar Hormuz, da neman a biya ta diyyar ɓarnar da aka mata sanadiyyar yaƙi, da ɗage mata duk wani takunkumi da kuma sakar mata duk wasu kadarorinta da aka riƙe.

The provisional truce comes more than a month after the US and Israel launched coordinated attacks on Iran

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Ko da Pakistan ta samu nasarar tabbatar da yarjejeniya mai ɗorewa tsakanin ɓangarorin biyu yayin da suka je Islamabad, ko kuma a'a, illar da yaƙin yake haifarwa na sauya tsarin Gabas ta Tsakiya.

A lokacin da suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran, Donald Trump da Firaiminista Benjamin Netanyahu sun ce za a sauya gwamnatin Iran.

Hakan bai faru ba, duk da ƙoƙarin da Shugaba Trump yake ta yi na ganin ya nuna cewa kisan jagororin Iran daidai yake da sauyin gwamnati.

Gwamnatin da Amurka da Isra'ila suka ce za ta rushe, a yanzu za ta zama ɗaya daga cikin ɓangarori biyu da za a yi tattaunawa da su.

Iran za ta yi ƙoƙarin ganin ta ƙara samun tasiri.

A ƴan makonnin da suka gabata an ji Trump na buƙatar Iran ta miƙa wuya ba tare da ta gindaya wani sharaɗi ba.

Babu cikakken bayani kan yadda tattaunawar da za a yi a Islamabad za ta sha bamban da ta Geneva wadda ke gudana a lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran.

A Geneva, an fara tattaunawa ne kan sabuwar yarjejeniyar nukiliya, ciki har da makomar tarin makamashin ureniyum (uranium) da Iran ta inganta wanda za a iya amfani da shi wajen haɗa makamin nukiliya.

Wani muhimmin abu da za a tattauna kansa a birnin Islamabad - shi ne Mashigar Hormuz. Mashigar ta zamo wani sabon makami ga Iran.

Idan Amurka da Isra'ila suka yanke shawarar ci gaba da kai wa Iran hare-hare, ƙasar ta riga ta nuna cewa za ta iya sake toshe ta cikin sauƙi, inda za ta yi wa tattalin arziƙin duniya illa.

Gabanin ranar 28 ga watan Fabarairu, jiragen ruwa na fadin duniya na bin hanyar ba tare da wani cikas ba.

Yanzu Iran ta ce za ta buɗe mashigar ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta, matuƙar dakarunta ne za su tsara yadda jiragen ruwan za su riƙa wucewa.

Za ta so a ci gaba da wannan tsari, kuma za ta so a ce ta riƙa karɓar kuɗi daga masu safara ta mashigar, irin yadda ake biya domin ratsawa ta mashigar Suez Canal.

Isra'ila ba ta cikin tattaunawar da aka yi ta tsagaita wuta. Netanyahu ya so ya ƙara yi wa ƙasar Iran ɓarna.

Yayin da ake shirin zaɓe a Isra'ila, masu adawa da shi a siyasance, ciki har da jagoran ƴan adawa Yair Lapid, sun zarge shi da yin zagon ƙasa ga tsaron Isra'ila.

China ta taka rawa gabanin cimma yarjejeniyar, wanda hakan ke nuna cewa za ta yi tasiri a tattaunawar da za a yi a birnin Islamabad. Wannan zai ƙara irin tasiri da take da shi a Gabas ta Tsakiya.

Kalaman Trump na na da tasu illar. Kalaman nasa sun dagula alaƙar Amurka da ƙawayenta, musamman ƙungiyar NATO.

Za a daɗe jagororin Birtaniya ba su manta cin fuskar da Trump ya yi wa Firaiministan ƙasar Keir Starmer ba, da kuma yadda ya ci fuskar dakarun ruwa na ƙasar.

Ƙasashen Gulf ba za su yanke alaƙarsu da Amurka ba amma za su sake nazari a kan alaƙar tsaro da ke tsakaninsu da ita.

Sannan kalaman da aka ji daga shugaban Amurka - wadanda za su iya zama laifukan yaƙi - ciki har da yiwuwar aikata kisan kiyashi kan wata al'umma - sun ƙara ruruta tantamar da ake da ita game da girmama dokokin duniya da na zamantakewa na shugaba Donald Trump.