Matakan da ake bi wajen wanke cikin ɗakin Ka'aba

Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman a lokacin wankin ɗakin Ka'aba a shekarar 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman a lokacin wankin ɗakin Ka'aba a shekarar 2022
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

A kowace shekara akan gudanar da al'adar wankin cikin ɗakin Ka'aba, kuma an gudanar da na wannan shekara a ranar Talata 15 ga watan Muharram, wadda ta zo daidai da 30 ga watan Yuni 2026.

A wannan shekara mataimakin gwamnan birnin Makka, Yarima Saud bin Mishal bin Abdulaziz ne ya jagoranci wankin ɗakin a madadin sarkin ƙasar Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al-Saud.

Wanke ɗakin na daga cikin ayyuka masu muhimmanci da ake gudanarwa a wuri mafi tsarki ga mabiya addinin Musulunci.

Shi ne ɗakin da dukkanin Musulmi ke fuskanta a lokacin sallah daga kowane ɓangare na duniya.

Wankin na alamta irin kula da hidima babu ƙaƙƙautawa da Musulmai suke yi wa ɗakin na Ka'aba.

A kowace shekara akan buɗe ɗakin inda ake gudanar da wankin, wanda hakan wani mataki ne na kula da kuma kare gini da tarihin ɗakin.

Kayan da ake amfani da su wajen wanke Ka'aba

  • Ruwan Zamzam da wani ruwan sinadaran wanke Ka'aba
  • Na'uka daban-daban na turare masu alfarma da ake cakuɗawa da ruwan Zamzam
  • Tsintsiya mai mariƙin azurfa wadda ake amfani da ita wajen cire datti
  • Abin goge bango mai mariƙi domin goge wurare masu tsayi na cikin Ka'aba
  • Ƙyallen goge ƙasan ɗakin Ka'aba wanda aka yi wa mariƙi, domin gogewa da busar da ɗakin Ka'aba

Ta yaya ake wanke Ka'aba?

Lokacin wanke ɗakin Ka'aba ranar Talata

Asalin hoton, FB/Insideharamain

Bayanan hoto, Lokacin wanke ɗakin Ka'aba ranar Talata

Ana yin koyi ne da matakan da Annabi Muhammad ya bi wajen wanke cikin ɗakin na Ka'aba.

A lokacin wankin Ka'aba akan yi amfani da farin ƙyalle na musamman wajen goge bangon cikin ɗakin.

Kuma ana amfani ne da ruwan Zamzam, inda ake haɗa shi da ruwan tsimin furen 'rose' mai ƙamshi.

Za a riƙa tsoma farin ƙyallen a cikin ruwan fure mai ƙamshi da kuma turaren Almiski.

Daga nan sai a riƙa zuba ruwan Zamzam wanda aka yamutsa shi tare da ruwan fure a dandamalin ƙasan ɗakin ana gogewa da hannu da kuma ganyen itacen kwakwa.

Daga ƙarshe akan goga nau'ukan turare masu ƙamshi da daraja a cikin ɗakin, inda bayan haka sai a sake rufe ƙofar ɗakin.

Tsarin matakan da ake bi su ne:

  • Haɗa ruwan wanke Ka'aba da jingina tsanin shiga
  • Ɗaga labulen ɗakin Ka'aba domin kare rigar
  • Wanke ɗakin da ruwan Zamzam da turare
  • Shafa turare a ƙusurwa huɗu na ɗakin