Me zai biyo baya a rikicin Amurka da Iran? Abu huɗu da za su iya faruwa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Saeed Jafari
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Political analyst
- Lokacin karatu: Minti 7
Ana ganin cewa Amurka na tattauna batun tsagaita wuta zagaye na biyu da Iran, yayin da wata tawaga daga Pakistan ta isa birnin Tehran.
Ana kuma ci gaba da aiwatar tsagaita wuta na makonni biyu da aka cimma bayan tattaunawa mai tsawo da ta ɗauki fiye da awanni ashirin tsakanin Amurka da Iran, wadda Pakistan ta jagoranta, amma ta ƙare ba tare da an cimma matsaya ba a ranar Lahadi.
Kwanaki kaɗan bayan kasa cimma matsaya a tattaunawar tsagaita wutar, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana sabuwar manufarsa kan Iran, inda ya yi magana kan yiwuwar toshe mashigar Hormuz, wacce ke da matuƙar muhimmanci ga harkar kasuwancin man fetur a duniya.
Wannan ya haifar da tambayoyi kan yadda ya kamata a fahimci gazawar tattaunawar farko wajen cimma yarjejeniya, da kuma irin tasirin ci gaba da tattaunawar nan gaba.
Ko shin Amurka da Iran kan hanyar shawo kan rikicin ta hanyar tattaunawa ko kuma rikici na iya faɗaɗa idan tattaunawar ta gaza.?
Ga wasu abubuwa huɗu da za su iya faruwa nan gaba:
1. Tsagaita wuta mara tabbas a matsayin dabarar "daura damara "

Asalin hoton, Getty Images
Bayan tsawon makonni na fada, tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta bayyana kamar wani yunƙuri na dakile rikicin da ya ƙara tsananta. Sai dai tun daga farko, yarjejeniyar ta kasance cike da rashin tabbas, saboda ba a fayyace ta sosai ba, kuma bangarorin biyu sun riƙa fassara ta ta hanyoyi daban-daban.
Babbar matsalar ita ce bambancin fahimta kan abin da tsagaita wutar ta ƙunsa. Wannan ya haɗa da wuraren da ta shafa, irin hare-haren da aka hana, da kuma abin da ake ɗauka a matsayin "karya yarjejeniya tsagaita wutar".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Saboda wannan rudani, wasu masu nazari sun ce ba yarjejeniya mai dorewa ba ce, sai dai wata dabarar "daura damara" na wucin gadi.
Wani babban mai bincike, Behnam Ben Taleblu Behnam a Gidauniyar Kare Dimokuraɗiyya da ke Washington, ya bayyana matsalar da ke cikin yiwuwar cimma yarjejeniya tun farko. Ya ce: "Damar cimma cikakkiyar yarjejeniya ta yi kasa sosai tun tun da farko tunda har an shiga yaki."
Ya ce batutuwan da ke tsakanin Amurka da Iran sun dade suna haifar da sabani, kuma yakin da aka shiga bai rage wannan bambanci ba, sai dai ya ƙara tsananta shi.
Wata babbar matsala ita ce bambancin bayanai daga jami'an bangarorin biyu. Iran na cewa an karya yarjejeniyar sau da dama, yayin da Amurka da Isra'ila ke fassara ta ta hanya daban. Wannan sabanin fahimta ya kara rura rashin yarda tsakanin bangarorin, yana sa kowane bangare ya rika zargin ɗayan da rashin gaskiya.
Idan tattaunawar zaman lafiya ta kasa kawo sakamako, ana ganin wannan tsagaita wutar za ta iya zama kawai hanya ta sayen lokaci ne kawai wanda kowanne bangare na iya amfani da lokacin wajen sake shiri da tattara ƙarfi, da kuma tsara mataki na gaba maimakon neman sulhu na dindindin.
A gefe guda, akwai yiwuwar Amurka ta ƙara matsa lamba ta hanyar kai hari kan muhimman abubuwa kamar tashoshin wutar lantarki da gadoji ko wuraren makamashi. Irin wannan mataki na iya haifar da matsin tattalin arziki da jinƙai ga fararen hula, sannan kuma zai iya sa Iran ta mayar da martani mai ƙarfi, abin da zai iya ƙara dagula rikici.
Haka kuma, Isra'ila tana taka muhimmiyar rawa a wannan yanayi, domin tana da shakku sosai kan tattaunawar. Ana ganin za ta iya ɗaukar matakai kamar kai hari kan wasu mutane masu alaƙa da tattaunawar.
Yaƙin sari ka-noke

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Wani abun da ake ganin zai iya faruwa a rikicin Amurka da Iran ita ce abin da masana ke kira "Yaƙin sari ka-noke". Wannan yana nufin cewa ba za a shiga cikakken yaƙi ba, amma kuma ba za a samu cikakkiyar zaman lafiya ba. A maimakon haka, za a ci gaba da kai wasu ƙananan hare-hare lokaci zuwa lokaci.
A irin wannan yanayi, za a iya ganin ci gaba da kai hare-hare kan muhimman wurare kamar gine-ginen tattalin arziki da sansanonin soja, ko hanyoyin jigilar kaya da makamashi.
Wadannan hare-hare ba za su kai girman yaƙi na ƙasa baki ɗaya ba, amma za su ci gaba da haifar da tashin hankali da rashin kwanciyar hankali tsakanin bangarorin biyu.
Rahotanni na nuna cewa ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran a ƙasashe kamar Iraq da yankin Tekun Fasha za su iya ƙara taka rawa. Haka kuma, Amurka na iya ƙara matsin lamba kan irin waɗannan ƙasashe
Wannan zai iya faɗaɗa fagen rikici zuwa wasu yankuna, ba tare da kai wa ga yaƙi kai tsaye tsakanin Amurka da Iran ba.
Wani masani, Hamidreza Azizi, ya bayyana cewa ɓangarorin biyu na ƙoƙarin amfani da ƙarfin su da dabarunsu domin matsa wa juna lamba, ba tare da shiga cikakken yaƙi ba. Ya kuma ce idan aka karya yarjejeniyar tsagaita wuta, akwai yiwuwar Iran ta ƙara amfani da ƙawayenta, musamman a Yemen, wajen mayar da martani.
Sai dai wannan yanayi na ɗauke da babban haɗari. Duk da cewa ba a nufin faɗaɗa rikici ba, kuskuren lissafi ko rashin fahimta daga ɗaya daga cikin bangarorin na iya jawo faɗaɗa rikicin fiye da yadda ake zato. A irin wannan hali, abin da aka fara a matsayin ƙananan hare-hare na iya rikidewa zuwa rikici mai girma.
3. Ci gaba da tattaunawar diflomasiyya

Asalin hoton, Pool/Getty Images
Duk da cewa tattaunawar da aka yi a Pakistan ta kasa haifar da sakamako mai gamsarwa, hakan ba yana nufin cewa hanyoyin diflomasiyya sun kare ba, ko kuma an rufe kofar tattaunawa gaba ɗaya. Har yanzu ana ganin akwai damar ci gaba da ƙoƙarin sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya maimakon faɗa.
Pakistan, wadda ta karbi bakuncin wannan tattaunawa, ana sa ran za ta ci gaba da taka rawa a kwanaki masu zuwa. Ana iya ganin ta na aika saƙonni tsakanin Amurka da Iran domin ƙoƙarin kusantar da su da kuma taimaka musu su cimma matsaya ɗaya, ko da kuwa a hankali ake tafiya.
A lokaci guda, wasu ƙasashe masu shiga tsakani kamar Qatar, Oman, har ma da Saudiyya da Masar, na iya ƙara shiga lamarin. Wannan na faruwa ne saboda fargabar cewa rikicin na iya ƙara faɗaɗa.
Irin waɗannan ƙasashe na iya zama hanyoyin sadarwa tsakanin bangarorin biyu, tare da ƙoƙarin hana rikici.
Sai dai babbar matsalar ita ce bambancin matsayi da ra'ayi tsakanin Amurka da Iran yana da zurfi sosai. Duk wani ci gaba a tattaunawar zai dogara ne kan yadda za a rage wannan bambance-bambacen ra'ayoyi da bukatu, wato a samu matsaya ta tsaka-tsaki maimakon kowane bangare ya dage kan nasa tsarin gaba ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta gabatar da shawara mai maki 15, yayin da Iran ta mayar da martani da nata shawara mai maki 10. Wannan yana nuna cewa har yanzu kowanne bangare yana ƙoƙarin ganin an karɓi tsarin sa fiye da neman hadin kai a tsakani.
Saboda haka, duk da yiwuwar komawa teburin tattaunawa, masana na ganin cewa samun cikakkiyar yarjejeniya cikin gaggawa ba abu ne mai sauƙi ba.
4. Toshe hanyoyin jiragen ruwa

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
Shugaban Amurka ya bayyana cewa sojojin ruwan ƙasar na shirin ƙaƙƙaba takunkumin teku a kan Iran, ta hanyar hana jiragen ruwa da tankunan mai wucewa ta mashigin Hormuz. Wannan mashigi yana daga cikin muhimman hanyoyin da ake jigilar mai a duniya.
Ya kuma yi barazanar cewa za a iya dakatar ko kama duk wani jirgi da ya biya kuɗin wucewa ga Iran domin wucewa ta mashigar Hormuz. Wannan mataki, a cewarsa, na da nufin hana Iran samun kuɗaɗen shigar mai, da matsa mata tattalin arziki, tare da rage ƙarfin China, wadda ita ce babbar mai sayen man Iran.
Behnam Ben Taleblu, ya ce irin wannan takunkumi na teku zai iya yin tasiri sosai kan Iran. Ya bayyana cewa bakin tekun Iran yana da tsawo, amma idan an rufe shi, hakan zai iya hana gwamnatin Iran damar fitar da muhimmin abin da take sayarwa, wato mai.
Sai dai wasu masana sun yi gargadi cewa wannan shiri na iya jawo wa Amurka manyan matsaloli. Suna cewa hakan zai sa sojojin Amurka su kusanci Iran sosai, inda za su iya zama cikin haɗarin kai farmaki. Haka kuma, za a buƙaci a ci gaba da tura sojojin ruwa na tsawon lokaci, abin da zai haifar da tsadar aiki sosai.
Bugu da ƙari, irin wannan mataki na iya jawo tashin farashin mai a duniya baki ɗaya. Haka kuma yana iya ƙara yiwuwar ƙungiyar Houthi ta Yemen ta tsoma baki ta hanyar kawo cikas a mashigar Bab al-Mandab, wanda shi ma yana da muhimmanci wajen jigilar mai. Idan hakan ta faru, zai iya ƙara dagula kasuwar makamashi ta duniya da kuma ƙara hauhawar farashin mai.
Rashin tsayayyen tsari: Sabuwar yanayin yankin

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Masana suna bayyana cewa yankin ya shiga wani sabon hali da ke da ruɗani, inda bambanci tsakanin zaman lafiya da yaƙi ya zama abun da ba a fayyace ba sosai. Wannan yana nufin cewa ba a cikin cikakken yaƙi ake ba, amma kuma ba a cikin cikakkiyar zaman lafiya.
Duk da gazawar tattaunawar da aka yi a Pakistan, hakan ba ya nufin cewa diflomasiyya ta ƙare. Haka kuma, ba ya tabbatar da cewa yaƙin zai fadada.
A irin wannan lokaci, ƙananan matakai ko sauye-sauye na iya haifar da manyan sakamako da zai iya canza yadda rikicin ke tafiya gaba ɗaya.
Saboda haka, masana suna kiran wannan yanayi da "rashin tsayayyen tsari", wato babu tabbatattun ka'idoji ko hanya ɗaya da ake bi, kuma sakamakon abin da zai biyo baya ba abin da za a iya hasashensa bane.











