Wace rawa fitattun ƴan Najeriya za su iya takawa a siyasar ƙasar?

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A duk lokacin da zaɓe ya gabato a Najeriya, fitattun mutane, musamman mawaƙa da jaruman fina-finai, kan bayyana goyon bayansu ga ƴan takarar da suke so, tare da amfani da shahararsu wajen tallata su ga magoya bayansu.

A baya-bayan nan, an ga yadda fitaccen mawaƙin kudancin Najeriya Davido ya taka rawa wajen yaƙin neman zaɓen kawunsa, wanda ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Osun.

Davido ya riƙa amfani da shafukansa na sada zumunta wajen yaɗa manufofin kawun nasa tare da bibiyar yadda zaɓen ke gudana. A wani saƙo da wallafa a X, mawaƙin ya yi barazanar kai ƙara ga Shugaban Amurka Donald Trump idan aka samu wata matsala da zaɓen.

A arewacin Najeriya ma, an dade ana ganin yadda mawaƙa da jaruman fina-finai ke bayyana goyon bayansu ga wasu ƴan siyasa, musamman a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Daga cikinsu akwai fitaccen mawaƙin Hausa Dauda Kahutu Rarara, wanda ya shahara wajen yi wa ƴan takarar jam'iyyar APC waƙoƙin yaƙin neman zaɓe da kuma tallata manufofinsu.

Sai dai tambayar ita ce shin goyon bayan fitaccen mawaƙi ko jarumin fim na iya sa magoya bayansa su sauya ra'ayinsu su zaɓi ɗan takarar da yake goyon baya?

Wane tasiri jarumai ke yi a zaɓuka?

Masana siyasa na ganin cewa fitattun mutane na iya taka muhimmiyar rawa a lokacin zaɓe, musamman saboda yawan masoya da mabiya da suke da su a kafafen sada zumunta da sauran wurare.

Dakta Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Jihar Kano (CAS), ya shaida wa BBC cewa irin waɗannan fitattun mutane kan yi amfani da shahararsu wajen tallafa wa 'yan siyasar da suke goyon baya.

Ya kawo misalin fitaccen mawaƙin Najeriya Davido, wanda ya taka rawa sosai a yaƙin neman zaɓen kawunsa, Ademola Adeleke, a jihar Osun. A zaɓen 2026 ma, Davido ya jagoranci wani kwamiti na matasa da aka kafa domin yaƙin neman zaɓen kawun nasa.

Dakta Sufi ya ce amfani da shafin X da Davido ya yi wajen bayyana matsayarsa da kuma matsa lamba kan batutuwan da suka shafi zaɓen, "ya taka rawa wajen ƙoƙarin da gwamnatin ta yi na rage matsin lamba ga gwamnatin jihar Osun."

Sai dai masanin ya ce tasirin fitattun mutane ba koyaushe yake kasancewa bisa kyakkyawan dalili ba. A wasu lokutan, wasu daga cikinsu kan tallafa wa ɗan siyasa ne saboda kuɗi ko wata moriya, ba wai saboda cancantar ɗan takarar ba.

"Su ma 'yan siyasa har yanzu sun amince da tasirinsu, kuma suna shigo da su cikin harkokinsu," in ji Dr Sufi.

A cewarsa, hakan na nuna cewa 'yan siyasa na kallon shahararrun mutane a matsayin wata hanya ta kai saƙonsu ga ɗimbin jama'a, musamman matasa da waɗanda suke bibiyar waɗannan jarumai da mawaƙa a kafafen sada zumunta.

Hanyoyin da jarumai ke amfani da shi

A yanzu da kafafen sada zumunta ke da matuƙar muhimmanci, fitattun mutane na da hanyoyi daban-daban da suke amfani da su wajen isar da sakon siyasa ga ɗimbin magoya bayansu.

Dakta Kabiru Sufi ya ce waɗanda suka iya amfani da kafafen sada zumunta, musamman X, na iya samun tasiri sosai saboda saƙonninsu na iya isa ga manyan mutane da kuma jama'a a fadin duniya.

Ya ce wasu kuma kan yi amfani da wakokinsu kai tsaye wajen tallata 'yan siyasar da suke goyon baya, musamman a arewacin Najeriya.

"Kamar su mawaƙan arewacin Najeriya, ana ganin waƙoƙinsu na zagaya ƙauyuka, shi ya sa suke tasiri," in ji Dr Sufi.

Sai dai ya ce ba lallai ne dukkan mawaƙa su ambaci sunan ɗan siyasar da suke goyon baya kai tsaye ba musamman na kudancin ƙasar, kamar yadda ake gani a wasu daga cikin waƙoƙin siyasa a arewacin Najeriya.

A cewarsa, wasu fitattun mutane kuma kan yi amfani da shahararsu wajen bayyana ayyukan 'yan siyasa da manufofinsu, ba tare da sun yi cikakken bincike ko tantance sahihancin bayanan ba.

Ya ce hakan na iya sa magoya bayansu su ɗauki abin da suka faɗa a matsayin gaskiya, musamman idan sun riga sun amince da jarumin ko mawaƙin.

A ganinsa, wasu mutane kan bi ra'ayin fitaccen mutumin da suke so ne kawai, ko da kuwa abin da ya faɗa game da wani ɗan siyasa gaskiya ne ko ba haka ba.

Ko suna iya sauya ra'ayin masu zaɓe?

Dr Sufi ya ce fitattun mutane na iya yin tasiri wajen sauya ra'ayin wasu masu zaɓe, musamman saboda akwai mutanen da ba sa yawan tantance ayyukan ɗan siyasa ko gazawarsa kafin su yanke hukunci.

Ya ce wasu daga cikin masu zaɓe kan bi abin da fitaccen mutum ya faɗa kawai, musamman idan suna matuƙar son sa ko kuma sun amince da ra'ayinsa.

Sai dai ya ce akwai wasu da ke yin bincike da kansu, su tantance abin da aka faɗa game da ɗan siyasa kafin su sauya matsayarsu. Haka kuma akwai waɗanda tuni suke da ƙayyadaddiyar alƙibla ta siyasa, don haka ba abu ne mai sauƙi a sauya musu ra'ayi ba.

Sai dai Dr Sufi ya ce yawan ambaton sunan ɗan siyasa da fitattun mutane ke yi, ko da kuwa ba su kai ga sauya ra'ayin masu zaɓe ba, na iya sa sunan ɗan siyasar ya zauna a zukatan jama'a.

A cewarsa, idan aka riƙa jin sunan mutum da kuma abubuwan da ake dangantawa da shi akai-akai, hakan na iya sa wasu su fara ganin ɗan siyasar a matsayin wanda suka fi kusanci ko goyon baya.

"Ko ba komai, irin wannan na iya ƙara wa mutum tagomashi da farin jini," in ji Dr Sufi.

Me ya sa al'umma ke fusata idan aka tallata musu wani ɗantakara?

A baya-bayan nan an ga yadda wasu fitattun mutane, musamman mawaƙa da jaruman fina-finai a arewacin Najeriya, ke fuskantar suka daga jama'a bayan bayyana goyon bayansu ga wasu 'yan siyasa.

Masana na ganin cewa irin wannan martani na iya faruwa ne idan jama'a suka gano cewa bayanan da fitaccen mutumin ke yaɗawa ba su dace da gaskiya ba, ko kuma suka yi imanin cewa yana tallata ɗan takarar ne saboda wata fa'ida da yake samu.

A cewar masana, saboda yawan amincewar da jama'a ke yi da fitattun mutane, ana sa ran su kasance masu faɗin gaskiya. Don haka idan aka gano cewa suna kare ɗan siyasa duk da gazawarsa, hakan na iya sa magoya bayansu su ji an yaudare su.

Haka kuma, wasu masu zaɓe ba sa son a yi amfani da shahararren mutum wajen tura musu wani ɗan takara ba tare da bayyana dalilin da ya sa ya cancanta ba. Wasu na kallon hakan a matsayin ƙoƙarin amfani da shaharar mutum wajen rinjayar ra'ayinsu.

Wannan ne ya sa a wasu lokutan tallan ɗan takara daga bakin fitaccen mutum kan haifar da akasin abin da ake tsammani, inda maimakon ya samu ƙarin magoya baya, sai mutanen da ba su goyon bayansa su fara sukar shi da kuma wanda yake tallatawa.