Ko nawa aka taya Bruno ba za mu sayar ba - Man United
Manchester United ta ce ko nawa za a taya kyaftin ɗinta Bruno Fernandes ba za ta siyawar ba, har lokacin d za a rufe kasuwar saye da sayarwar 'yan wasa ta nahiyar Turai a watan gobe.
BBC Sport ta samu labari a makon da ya gabata cewa kulob ɗin Galatasaray na Turkiyya, tare da manyan kulob ɗin Italiya Juventus da AC Milan, suna nazarin yiwuwar United ko za ta ci gaba da riƙe kyaftin ɗinta.
Ana tunanin cewa Galatasaray ta shirya wani tayin da za ta miƙa wa United, wanda zai kai kimanin yuro miliyan 50, kwatankwacin fam miliyan 42.7.
Sai dai manyan majiyoyi daga Old Trafford sun bayyana cewa Galatasaray za ta ɓata lokacinta ne kawai idan ta yi hakan.
Ko da yake a bara United ta gaya wa Fernandes cewa shi ne zai yanke shawara kan ko zai amince da tayin da kulob ɗin Al-Hilal na Saudi Pro League ya yi masa, inda daga baya ɗan wasan na Portugal ya amsa cewa ya ji "raɗaɗi" saboda wannan ba shi zaɓin, amma a wannan karon United ta fito ƙarara ta bayyana matsayinta.
Majiyoyin kulob ɗin sun ce har yanzu babu wani tayin da aka gabatar wa ɗan wasan mai shekaru 31, amma ta jaddada cewa ko nawa za a taya shi ba za ta sayar da shi ba.
Fernandes yana da sauran shekara ɗaya a kwantaraginsa na yanzu, tare da zaɓin ƙara wata shekara ɗaya.
An san cewa shi da kansa ya fi son ci gaba da zama a kulob ɗin.
Kunshin yarjejeniyar ɗan wasan ɗan ƙasar Portugal wanda ya haɗa da sharadin sayensa kan fam miliyan 57 ya riga ya ƙare.
Har zuwa yanzu, ba a cimma wata yarjejeniya ba kan tsawaita kwantaraginsa a ƙungiyar.