Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Mourinho zai iya mayar da Real Madrid kan ƙadamin nasara?
José Mourinho ya bar Real Madrid a shekarar 2013 a matsayin ɗaya daga cikin fitattun masu horar da ƙwallon ƙafa a duniya.
Yanzu, bayan shekaru 13, mutumin da ya yi wa kansa laƙabi da "The Special One" ya dawo Santiago Bernabéu, inda aka ɗora masa alhakin dawo da martabar ƙungiyar bayan kakar wasanni biyu a jere ba tare da lashe kofi ba.
Sai dai dawowar Mourinho ta haifar da wata tambaya mai ban sha'awa.
Shin kocin mai shekaru 63 har yanzu yana da ikon kai wa matakin nasarorin da ya taba samu a baya?
Ko kuma gwara shugaban Real Madrid, Florentino Pérez, ya koma ga wani koci ɗan zamani wanda ke kan ganinyarsa mai makon Jose da lokacinsa ya wuce?
A cikin shirin More Than The Score podcast, BBC Sport ta tattauna da mutanen da suka fi sanin Mourinho domin tantance ko zai iya samun nasara a wa'adinsa na biyu tare da Los Blancos.
Komawa wa'adi na biyu
Mourinho ya lashe kofi guda ɗaya kacal tun bayan da ya bar Real Madrid, wato gasar Firimiya da ya ci a wa'adinsa na biyu da Chelsea a shekarar 2015. Zaman da ya yi daga baya a Manchester United, Tottenham, Roma, Fenerbahce da Benfica ya samar da wasu nasarori a gasar kofuna, amma kuma ya kasance cike da rikice-rikice da cece-kuce.
Masanin ƙwallon ƙafar Spain, Eduardo Alvarez, na ganin cewa naɗin Mourinho ya samu ne saboda shugaban kulob din, Florentino Pérez, ya yi koyi da nasarar da Carlo Ancelotti ya samu a wa'adinsa na biyu a Real Madrid.
"Ina ganin ya zaɓi Mourinho a karo na biyu ne saboda Ancelotti ya yi nasara a wa'adinsa na biyu kuma lamarin kusan iri ɗaya ne," in ji Alvarez ga BBC Sport.
"Ancelotti yana horar da Everton, wataƙila ba ya cikin mafi kyawun lokacinsa, yana da shekaru 60 a lokacin, amma da ya koma Real Madrid, komai ya yi kyau kuma ya lashe Champions League.
"Mourinho ya dace da tsarin Real Madrid saboda wannan kulob ba kulob ne na koci ba, kulob ne na 'yan wasa. Duk da cewa Mourinho babban koci ne da ya yi shuhura, salon jagorancinsa bai fi karkata ga dabaru ba, sai dai ga sarrafa da ƙarfafa 'yan wasa, kuma wannan ne nake ganin Florentino yake buƙata."
'Zai buƙaci ya sauya ɗabi'u da halayen 'yan wasa'
Sai dai akwai wani tsohon shugaban Real Madrid da ke ganin Mourinho shi ma dole ne ya canja salon jagorancinsa idan yana son samun nasara.
Ramon Calderon, wanda ya jagoranci kulob ɗin daga shekarar 2006 zuwa 2009, ya yi maraba da naɗin Mourinho, amma ya yi gargadin cewa dan Portugal din ba zai iya dawowa da irin salon da ya yi amfani da shi a wa'adinsa na farko ba.
"Zai buƙaci ya sauya ɗabi'a da halayen 'yan wasan," kamar yadda ya shaida wa BBC Sport.
"Lokacin da yake Real Madrid shekaru 13 da suka gabata, ya kasance yana son fitowa fili sosai. Ya samu matsaloli da dama da kulob-kulob, abokan hamayya da alkalai, kuma a ko da yaushe yana ɗora laifin rashin nasara kan wasu maimakon ya ɗauki alhakin kansa."
"Ina ganin dole ne ya samu girmamawa da amincewar 'yan wasa ta hanyar lallashi da gamsarwa, ba ta hanyar tilastawa ba. Ya kamata ya nuna musu cewa hanyoyin aikinsa su ne mafi alheri ga ƙungiyar gaba ɗaya, ba tare da neman fitattun taurari ba."
Bayan ya jagoranci Inter Milan zuwa lashe kofuna uku a kakar wasa ta 2010, wato Serie A, Coppa Italia da Champions League, Mourinho ya koma Real Madrid inda ya lashe La Liga, Copa del Rey, sannan ya kai ƙungiyar zuwa wasan kusa da na ƙarshe na Champions League sau uku a jere.
Sai dai wa'adinsa na farko a Madrid ya kasance mai cike da rigingimu da abokan hamayya, saɓani a ɗakin canza kayan 'yan wasa, da kuma dangantaka mai cike da tashin hankali da kafafen yaɗa labarai na Spain.
"Ina fatan zai canja," in ji Calderon.
"Idan ya dage kan maimaita kuskuren da ya yi a baya, hakan zai zama matsala."
'Ba kowane dan wasa ba ne ya goyi bayan shi a Benfica'
Tambayar ko Mourinho ya canja kuwa ita ma an yi ta a Portugal, inda ya shafe kakar wasan da ta gabata yana horar da Benfica.
Dan jaridar ƙwallon ƙafa na Portugal, Duarte Monteiro, na ganin cewa amsar ita ce a'a.Ya ce:"Mourinho bai canja ba. Halayensa da ɗabi'unsa ba su canja ba. Matsalar, a ganina, ita ce duniya ce ta canja.
Matasan 'yan wasa na yau, 'yan jarida da kuma yanayin da ake ciki sun bambanta, kuma ina ganin mutane ba sa rungumar sa kamar yadda suke yi shekaru 20 ko 25 da suka gabata, lokacin da halayensa suke sabo kuma abin sha'awa."
Monteiro ya bayyana wasan Benfica a kakar da ta gabata a matsayin wanda "ba ya da armashi sosai", inda ya ce Mourinho ya yi amfani da salon wasa mai tsantsan da taka-tsantsan, kuma ya nuna kamar yana da fifiko daban-daban tsakanin gasannin cikin gida da na Turai.
Duk da haka, akwai wasu lokutan da suka yi fice, musamman nasarar da Benfica ta samu da ci 4-2 a kan Real Madrid a matakin rukuni na Champions League, kafin daga baya ta sha kashi a wasan neman gurbin ci gaba.
Sai dai Monteiro ya ce tsoffin halayen Mourinho sun ci gaba da bayyana, yana mai cewa:"Akwai lokuta biyu ko uku a cikin kakar wasan da ya fito fili yana sukar wasu rukunin 'yan wasa cikin tsananin harshe a bainar jama'a. Ba kowane ɗan wasa a Benfica ne yake tare da shi a kakar wasan da ta gabata ba."
Bellingham zai farfaɗo a ƙarƙashin Mourinho?
Wataƙila wannan ita ce babbar tambayar da Mourinho zai fuskanta, domin ɗakin canza kaya na Real Madrid na ɗauke da manyan taurari irin su Kylian Mbappe, Vinicius Jr da Jude Bellingham, tare da wasu fitattun 'yan wasa na duniya.
A al'adance, dabarun Mourinho wajen jagoranci sun ta'allaka ne kan ƙulla ƙaƙƙarfan dangantaka da manyan 'yan wasa da kuma neman cikakken sadaukarwa daga gare su. Tsohon ɗan wasansa, Robert Huth, ya ce: "Ina ganin Bellingham zai matuƙar so yin aiki da Jose. Zai bunƙasa sosai a ƙarƙashinsa."
Sai dai yana da damuwa game da Mbappe da Vinicius, inda ya ƙara da cewa: "Lokacin da abubuwa ba su tafiya yadda suke so, sai labarai su fito a kafafen yaɗa labarai. Ni ba na son irin wannan abu. Bellingham irin ɗan wasan nan ne da yake bayar da komai a kowane wasa. Jose yana son irin wannan hali."
Calderon ma ya ce sarrafa irin waɗannan taurari zai zama babban ƙalubale ga Mourinho. Ya ce "Ɗakin canza kaya cike yake da taurari, kuma yana da ƙungiya mai ban mamaki. Amma hakan ma na iya zama matsala idan ba a tafiyar da lamarin yadda ya kamata ba."
A aikinsa na farko a matsayin koci a Porto, Mourinho ya kasance mai ɗokin tabbatar wa duniya ƙwarewarsa a matakin koli.
Ya karɓi ragamar ƙungiyar a tsakiyar kakar wasan 2001-02, sannan ya yi fice da furucinsa cewa zai mai da Porto zakaran liga a kakar wasa ta gaba.
Ya cika alkawarinsa, inda ya gina ƙungiya da ba ta ƙunshi manyan sunaye ba amma cike da yunƙurin samun nasara. Ya lashe gasar Portugal da UEFA Cup a shekarar 2003, sannan ya kare kofin liga tare da lashe Champions League a kakar wasa ta gaba.
Sai dai ɗan jarida Duarte Monteiro ya amince cewa ba zai yiwu a sake samun irin wannan Mourinho na Porto ba. "Abin da Mourinho ya yi a Porto aiki ne da ake samu sau ɗaya kacal a rayuwa. Babban bambanci shi ne cewa a wancan lokacin yana da abin da yake son tabbatarwa. Yanzu ina ganin abin da ya rage masa shi ne ya tabbatar wa kansa wani abu, kuma wani lokaci hakan ba ya yi masa amfani."
Yanzu da yake da shekaru 63, Mourinho ba shi da abin da zai sake tabbatarwa dangane da sunansa da tarihin nasarorinsa, amma Real Madrid na iya buƙatar wani abu daban daga gare shi.
Ba wai karfin hali da basirar dabarun wasa kaɗai ba ne suka sa ya zama ɗaya daga cikin fitattun masu horar da ƙwallon ƙafa a duniya, har ma da ƙwarewarsa wajen daidaitawa da canje-canje.
Huth ya ce Mourinho har yanzu yana da: "Ilimi mai ban mamaki game da wasan ƙwallon ƙafa," amma yanzu yana buƙatar ya sa 'yan wasan Real Madrid na yanzu su yi cikakken imani da shi kamar yadda 'yan wasan Porto, Chelsea da Inter Milan suka yi a baya lokacin da suke neman ƙarin ɗaukaka da kofuna.