Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ademola Adeleke ya sake lashe zaben gwamnan jihar Osun - INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar 15 ga watan Agustan 2026.
Adeleke ya fafata ne a zaben da sauran ‘yan takara 14, ciki har da dan takarar jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Oyebamiji, wanda shi ne fafatawar ta fi zafi a tsakaninsu.
Babban jami’in zabe na hukumar Inec a zaben wanda ya sanar da sakamakon da asubahin ranar Lahadi, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe ya ce Adeleke ya samu jimillar kuri’u 511,067 yayin da Oyebamiji na jam’iyyar APC wanda ya zo a matsayi na biyu ya samu jimillar kuri’u 444,815.
Abubuwa da dama ne suka faru gabanin zaben, daya daga ciki wanda ya ja hankalin al’ummar Najeriya shi ne garkame asusun kudin gwamnatin jihar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta yi.
Hukumar ta ce dama tana gudanar da bincike kan asusun saboda tana zargin cewa ana gudanar da wata almundahana.
Sai dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa EFCC umarnin sake bude asusun ajiyar gwamnatin sanadiyyar Allah-wadai da tofin Allah-tsine da matakin ya janyo daga al’umma.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Shugaba Tinubu ya ce “ya ji matukar kunya ba domin cewa EFCC ta gudanar da aikin da doka ta amince mata ba, sai dai saboda yadda ta dauki matakin a daidai wannan lokaci”.
Ya bai wa hukumar umarnin ta dakatar da duk wani mataki da take son dauka kan gwamnatin jihar a wannan lokacin.
Shugaban na Najeriya ya ce tun bayan hawansa mulki ya sha nanata cewa za a bar hukumomin yaki da rashawa su gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ko sanya siyasa a ciki ba.
Wane ne Ademola Adeleke?
Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, wanda shi ne gwamnan jihar Osun a halin yanzu, an haife shi ne a ranar 13 ga Mayun 1960 a garin Ede, jihar Osun.
Ya fito daga cikin iyali mai tasiri a siyasa - Mahaifinsa shi ne Sanata Raji Ayoola Adeleke, yayin da mahaifiyarsa, Nnenna Esther Adeleke, ta fito daga yankin Akwete da ke ƙaramar hukumar Ukwa West a jihar Abia.
Ademola Adeleke ya shiga harkar siyasa a shekarar 2001 tare da ɗan'uwansa, Sanata Isiaka Adeleke, wanda ya rasu a watan Afrilun 2017.
Bayan rasuwar ɗan'uwansa, Ademola Adeleke ya tsaya takarar kujerar Sanatan Osun ta Yamma , inda ya samu nasara a zaɓen cike gurbi na shekarar 2017 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.
Kafin komawarsa PDP a watan Afrilun 2017, Adeleke ya kasance mamba a jam'iyyar APC.
Daga baya, ya shiga takarar gwamnan jihar Osun, inda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyarsa bayan ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Akin Ogunbiyi, da ƙuri'u bakwai kacal. Bayan haka ya tsaya takarar gwamna a zaɓen da aka gudanar a ranar 23 ga Yulin 2018.
A watan Disamban 2025, Adeleke ya koma jam'iyyar Accord, inda ya samu tikitin takarar gwamna domin neman wa'adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar Osun.
A ranar 22 ga Maris, 2019, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da hukumar zaɓe ta ƙasar ta ce bai kammala ba. Amma daga bisani, a ranar 5 ga Yulin 2019, Kotun Ƙolin Najeriya ta soke wannan hukunci tare da tabbatar da Gboyega Oyetola a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Osun na 2018.
A zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga Yulin 2022, Adeleke ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, inda ya samu nasara kan gwamna mai ci a wancan lokaci, Gboyega Oyetola.
Adeleke ya samu ƙuri'u 402,979, yayin da Oyetola ya samu 375,027, abin da ya ba shi damar lashe zaɓen.
Ademola ya yi karatun Kimiyyar Siyasa (Political Science) a Jami'ar Jacksonville State University da ke jihar Alabama, Amurka.
Ademola Adeleke fitaccen ɗan kasuwa ne kuma ƙwararren mai gudanarwa.
A cewar bayanan da aka bayar, ya riƙe mukamin Babban Darakta na kamfanin Guinness Nigeria Plc tsakanin shekarun 1992 zuwa 1999.
Haka kuma, ya kasance Babban Daraktan kamfanin Pacific Holdings Limited daga shekarar 2001 zuwa 2016. Kafin wannan, ya yi aiki da kamfanin Quicksilver Courier da ke Atlanta, jihar Georgia ta Amurka tsakanin 1985 zuwa 1989.
Adeleke ya kuma yi aiki da kamfanin Origin International LLC da ke Atlanta, Georgia, inda ya riƙe mukamin mataimakin shugaban kamfanin tsakanin 1990 zuwa 1994.