Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shirin da manyan ƙungiyoyin Premier 6 suka yi don tunkarar sabuwar kaka
Yayin da za a buɗe sabuwar kakar gasar Premeir league a yau, masu nazarin ƙwallon ƙafa na ci gaba da hasahen rawar da ƙungiyoyin gasar za su taka a bana.
Kodayake wasu na ganin lokaci ya yi da za a daina hasashe kai tsaye, ko bugun ƙirji kan wadda za ta lashe gasar ko waɗanda za su ma fice daga gasar.
A kakar da ta gabata, an yi hasashen cikin ƙwarin gwiwa cewa Liverpool ce za ta lashe gasar, amma daga baya ta gaza kai wa ga hasashen da aka yi cikin wani abin mamaki, lamarin da ya kai ga korar mai horar da ita Arne Slot.
A wannan kakar kuwa, akwai sabbin masu horarwa guda tara a gasar ta Premier League, abin da ya sa wannan ya zama ɗaya daga cikin hasashen da suka fi wahala da aka taɓa yi.
A wannan muƙala mun duba irin shirin da manyan ƙungiyoyin gasar shida suka yin don tunkarar kakar ta bana.
Arsenal
Wadda ta lashe Premier bara karon farko cikin shekara 22 na cikin kyakkyawan matsayi na kare kambunta, kuma wasu masana ƙwallon ƙafa na imanin cewa za ta sake lashe gasar.
Tawagar Mikel Arteta na da ƙwararrun ƴan wasa a kowane hannu da ake buga wasa, kuma za ta shiga kakar wasa da ƙwarin gwiwar kasancewa gwarzuwar gasar ta bara.
Ta kuma sayi fitattun ƴanwasa, Bruno Guimaraes da Christos Tzolis da ake ganin za su taka rawa a ƙungiyar, mai fitattun ƴanwasa.
Tuni dai ƴan wasan suka nuna kansu bayan rawar da suka taka lokacin da Arsenal ta lallasa Manchester City a wasan Community Shield.
Manchester City
Man City ce ta zo ta biyu a kakar wasan da ta ƙare.
Wannan shi ne farkon sabon zamani a ƙungiyar, inda Enzo Maresca ya gaji Pep Guardiola, wanda mutane da dama ke ganin shi ne mafi girman kocin ƙwallon ƙafa na wannan zamanin namu.
Manyan ƴan wasa masu tasiri da ƙarfi sun bar ƙungiyar, ciki har da Rodri, Bernardo Silva da John Stones da Tijjani Reinders , wanda ya nuna cewa Manchester City na cikin wani muhimmin matakin sauyi a filin wasa na Etihad.
Rashin nasarar da suka yi a wasan ƙarshe na Community Shield a hannun Arsenal na iya sa wasu magoya baya su shiga damuwa, amma har yanzu ƙungiyar tana da ƙwararrun 'yan wasa masu inganci.
Tuni ta ɗauko Elliot Anderson kan kuɗin fam miliyan 116, sannan ta na sa ran matashin ɗan wasan tsakiya na Morocco mai hazaka, Ayyoub Bouaddi, zai dawo City daga Lille.
Abu mafi muhimmanci kuwa shi ne, duk wata ƙungiya da take da fitaccen mai zura ƙwallaye kamar Erling Haaland a gaba ba za a taɓa cire ta daga masu neman kowane kofi ba.
Ana sa ran Manchester City za ta lashe aƙalla wani babban kofi a wannan kakar.
Manchester United
Ta ƙare kakar da ta gabata a mataki na uku, kuma wannan ce cikakkiyar kakar wasa ta farko ƙarƙashin jagorancin Michael Carrick, wanda ya yi abin yabo sosai wajen dawo da Manchester United gasar Zakarun Turai a kakar da ta gabata bayan korar Ruben Amorim.
Samun gurbin Champions League da kuma lashe aƙalla kofi guda ya kamata su kasance manyan manufofin Manchester United a wannan kakar, kuma ina sa ran ƙungiyar za ta iya cimma waɗannan burikan.
Youri Tielemans ya zo daga Aston Villa a matsayin ƙwararren ɗan wasa mai gogewa da basirar karanta wasa, sai matashin ɗan wasa Andrey Santos daga Chelsea mai cike da fatan samun makoma mai kyau.
Liverpool
A matsayi na biyar ta kammala a bara, mataki mafi muni cikin shekaru.
Sabon koci, Andoni Iraola da ta ɗauka daga Bournemouth ya zo da tsari na daidaito bayan mummunar kakar gasar da Liverpool ta fuskanta a bara.
Wani sabon lokaci ne ga ƙungiyar ba tare da Mohamed Salah ba, ɗan wasan da ya jagoranci ƙungiyar tsawon shekaru.
Salon wasan Iraola mai cike da matsin lamba da ƙarfin gudu zai iya ɗaukar lokaci kafin 'yan wasan su saba da shi, amma har yanzu Liverpool tana da manyan 'yan wasa masu ƙwarewa a cikin tawagarta.
'Yan wasa kamar Florian Wirtz da Alexander Isak yanzu sun fahimci yadda rayuwa da taka leda a Anfield take, lamarin da zai taimaka musu wajen bayar da gudunmawa mai yawa a yanzu.
Idan Bradley Barcola ya koma Liverpool daga Paris Saint-Germain, sannan kuma matashin ɗan wasa Rio Ngumoha ya ci gaba da haɓɓaka cikin sauri, Liverpool na da damar yin kakar wasa mai ƙayatarwa.
Haka kuma, matasan ƴan bayanta na tsakiya Jeremy Jacquet da Giovanni Leoni ana kallonsu a matsayin taurari masu tasowa nan gaba. A gefe guda kuma, ɗan wasan gefe na Sifaniya Victor Munoz zai kawo sauyi bangaren sauri da kuzari da ƙarin barazana wajen kai hari.
Aƙalla, ana sa ran Liverpool za ta kammala kakar wasa cikin manya huɗu na tebur, kuma za ta kasance cikin masu fafatawa wajen lashe manyan kofuna.
Chelsea
Ta kammala kakar bara a matsayi na 10, kuma yanzu,amma Xabi Alonso ƙwararren koci ne da ya zo ƙungiyar, kuma ya riga ya nuna abin da zai iya yi bayan ya jagoranci Bayer Leverkusen zuwa lashe kofin Bundesliga.
Haka kuma, ba shi kaɗai ba ne ya fuskanci ƙalubalen da suka biyo bayan aiki a Real Madrid.
Yanzu yana fuskantar babban aiki na tsara tawagar Chelsea mai cike da 'yan wasa da yawa, tare da warware batun Enzo Fernandez, wanda ake ganin bai gamsu sosai ba, idan har zai ci gaba da zama a ƙungiyar.
Duk da haka, Chelsea na da ƙwararrun ƴan wasa da yawa, kuma idan Alonso ya samu damar haɗa su cikin tsari mai kyau, ƙungiyar za ta iya zama mai matuƙar ƙarfi.
Sabbin 'yan wasan da suka haɗa da Morgan Rogers da Maxence Lacroix wani gagarumin ƙari ne ga tawagar.
Haka kuma, ɗaukar gogaggun 'yan wasa kamar Jordan Henderson da Danny Welbeck ya zo wa mutane da mamaki, amma a bayyane yake cewa an kawo su ne domin su taimaka wajen jagoranci a tsakanin 'yan wasa da kuma kafa kyakkyawan yanayin aiki a cikin ƙungiyar.
Aston Villa
A baya-bayan nan Aston Villa ta nuna kanta wajen shiga manyan ƙungiyoyin gasar, inda a kakar da ta ƙare ta kammala a matsayi na huɗu.
A bara ne Unai Emery ya jagoranci ƙungiyar ta lashe gasar Europa League tare da dawo da ita gasar Zakarun Turai.
Wannan ƙwararren mai tsara dabaru ba mutum ba ne da za a raina, amma ƙoƙarin da Aston Villa ke yi na daidaita harkokin kuɗinta ya jawo tafiyar wasu muhimman 'yan wasa kamar Youri Tielemans da Morgan Rogers.
Yanzu babban nauyi zai rataya a wuyan Alejandro Garnacho, wanda aka aro.
Haka kuma, ana sa ran ɗan wasan tsakiya na Brazil Joao Gomes, wanda aka saya daga Wolves kan fam miliyan 38, zai taka muhimmiyar rawa a sabuwar kakar.
Villa ta kuma ɗauki matashin ɗan wasan tsakiyar Freiburg mai shekara 20, Johan Manzambi, wanda ya yi fice tare da Switzerland a Gasar Kofin Duniya.
Ƙungiyar ta kuma ɗauko mai tsaron ragar Japan Zion Suzuki daga Parma domin ya zama golanta na dogon lokaci, yayin da makomar Emiliano Martinez a ƙungiyar ke ci gaba da kasancewa cikin rashin tabbas.