Falle Ɗaya: Me take nufi kuma daga ina ta samo asali?

Asalin hoton, Dalung/Facebook
- Marubuci, Usman MINJIBIR
- Aiko rahoto daga, Abuja, Najeriya
- Lokacin karatu: Minti 5
Idan akwai wata kalma da za ta samu karɓuwa a wurin ƴan siyasa musamman a arewacin Najeriya to ita ce kalmar Falle Ɗaya wadda a yanzu haka amonta kawai ake ji na tashi a cikin wake da waƙoƙin siyasa.
Masana adabi da na kimiyyar siyasa na cewa ƴan siyasa kan yi amfani da salo na kalmomi a magana ko kuma a cikin waƙe domin jan hankali masu zaɓe.
Za a iya cewa a mafi yawancin lokaci irin waɗannan kalamai na jan hankali na samo asali ne daga birnin Kano wanda shi ne cibiyar siyasar arewacin Najeriya.
BBC ta yi nazari dangane da wannan kalma da asalinta da ma'anarta da kuma irin tasirin da za ta iya yi a kakar zaɓen 2027 da ke tafe a Najeriya.
Wane ne ya fito da sarar Falle Ɗaya?

Asalin hoton, A'in Jafaru/Facebook
Duk da cewa tsohuwar kalmar Hausa ce amma akwai saɓani dangane da haƙiƙanin mutumin da ya fara furta ta har ta janyo sara a baya-bayan nan amma kuma ta tabbata kalmar ta fito ne daga mabiya tafiyar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Wani wanda yake da masaniya da al'amuran tafiyar Kwankwasiyya ya shaida wa BBC cewa wata fitacciyar ƴar siyasa kuma ƴar Kwankwasiyya da ake kira A'in Jafaru Fagge ce ta fara furta kalmar.
"A'in Jafaru Fagge ita ce ta fara faɗin Falle Ɗaya a wani taro da ban iya tuna yaushe ba ne, inda take yi wa gwamna Abba Kabir Yusuf gugar zana dangane da barin jam'iyyar NNPP ta Kwankwaso zuwa APC ta Ganduje."
Sai dai wani mabibiyin Kwankwasiyya wanda ba ya son a ambaci sunansa ya shada wa BBC cewa Sanata Kwankwaso da kansa ne ya fara furta wannan kalma.
"Gaskiya ina kyautata zaton cewa Madugu ne ya fara faɗar kalmar Falle Ɗaya amma ba zan iya tuna yaushe ne ba kuma a wane taro ne. Amma tabbas ni a bakinsa na fara jin kalmar."
Ko ma dai daga ina ne wannan kalmar ta fito a yanzu haka ta samu karɓuwa a tsakanin ƴan siyasa tun bayan da mawaƙa suka kururuta ta.
Falle Ɗaya Ce - Tijjani Gandu

Asalin hoton, Tijjani Gandu/TV
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ko Kwankwaso ko kuma A'in Jafaru Fagge ne ya fara furta wannan kalmar, kalmar ba ta samu shahara ba har sai da mawaƙi Tijjani Gandu ya saƙa ta a cikin waƙa irin ta siyasa.
Tijjani Gandu wanda ya saki waƙar Falle Ɗaya Ce a ranar da ayyana komawa wurin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso bayan ficewa daga tafiyar Gwamna Abba wanda ya koma APC, ya kasance mataimaki na musamman ga gwamnan.
A waƙar ta Falle Ɗaya mai tsawon minti 4:59 kamar yadda take a shafinsa na Youtube, Tijjani Gandu ya yi ta zambo da habaici a waƙar da ake zargin da waɗanda suka bar tafiyar Kwankwaso suka koma APC.
A duk lokacin da ake buga waƙar a wurin taruka, masu sauraro na bin waƙar cikin nishaɗi tare da ɗaga ko jujjuya falle ɗaya na hula ku zani ko gyale ko kuma tsumman da ke hannunsu.
To sai dai wani mawaƙin na Kannywood mai suna Abubakar Sani wanda ake kyautata zaton yana tafiyar gwamna Abba Kabir Yusuf na APC, shi kuma ya yi wa Tijjani Gandu martani a waƙa mai taken Falle Biyu Ce.
A waƙar tasa ya yi zambo da habaici ga Tijjani Gandu da ma ƴan tafiyar Kwankwasiyya.

Asalin hoton, Tijjani Gandu/Facebook
Ma'anar Falle Ɗaya

Asalin hoton, Kwankwasiyya/Facebook
Malam Ibrahim Sheme, masani ko mai nazari kan adabin Hausa ciki har da waƙe da waƙoƙi ya ce kalmar Falle a Hausa daɗaɗɗiya.
"Ita kalmar falle ba yau aka ƙirƙire ta ba, tsohuwar Hausa ce. Tun dama can idan aka ce abu falle ana nufin abu guda ɗaya. Yawanci a kan danganta da warƙar takarda guda. Ko kuma ka ce wari ɗaya. Ko kifi ɗaya kamar idan ana maganar kifi na suga rawar doki..."
Sai dai masanin ya ce ma'anar da aka yi amfani da ita a waƙar Tijjani Gandu ta sha bambam.
"A ita cikin waƙar, mawaƙin ya yi amfani da kalmar falle ɗaya ana nufin kamar yadi guda ɗaya na tufafi wanda idan yadi guda ɗaya bai isa sutura ba wato ba za a iya ɗinka riga ko sutura da falle ɗaya na yadi ba," in ji Malam Ibrahim Sheme.
Dangane kuma da saƙon da mawaƙin yake aikawa ta ma'ana a cikin waƙar Falle Ɗaya Ce, Malam Ibrahim ya ce tana ƙunshe da saƙon siyasa.
"Manufar shi mawaƙin a yadda mutane suka fahimci saƙon shi ne wato falle na nufin wa'adin mulki ga shugaba. To abin da mawaƙin da ke nufi shi ne wannan wa'adin da mai mulki ya yi to ya gama tundaya yi falle ɗaya wato ba zai samu wa'adi na biyu ba ko kuma falle biyu."
Falle Ɗaya Ce - Solomon Dalung

Asalin hoton, Dalung/Facebook
Da alama kalmar siyasa ta Falle Ɗaya da ta faro daga Kano tana ci gaba da mamaye arewacin Najeriya da ma a cikin ƙasa.
A baya-bayan nan wasu jiga-jigan ƴan jam'iyyar ADC da suka hallara a Kano wajen tarbar sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar ta haɗaka su ma sun rausaya a lokacin da ake buga waƙar taFalle Ɗaya Ce.
Wani bidiyo na tsohon ministan matasa na Najeriya, Barista Solomon Dalung ya nuna yadda yake rawa a lokacin da yake bibiyar waƙar riƙe da falle ɗaya da ya nuna shi.
Wane tasiri Falle Ɗaya Ce za ta yi a 2027?
Malam Ibrahim Sheme ya ce wannan ba sabon al'amari ba ne a tarihin siyasar Najeriya wajen amfani da mawaƙa wajen isar da saƙon siyasa.
"Manufar ko wane mawaƙin siyasa ita ce ya ɗaga darajar ɗan takara ko shugaban da yake goyon baya sannan kuma a lokaci guda ya ƙasƙantar da wanda ba ya so duk da nufin ɓangarensa ya ci zaɓe ..saboda haka ma ita waƙa ta gaji habaici da zambo.
"Kuma wannan ba sabon abu ba ne. An ga yadda tun a zamanin jamhuriya ta ɗaya an yi amfani da mawaƙa irin su Alhaji Mamman Shata, Alhaji Musa Danƙwairo wajen ɗaga ƴan siyasa musamman firimiyan arewa, Ahmadu Bello. Haka a jamhuriya ta biyu ma mun ga mawaƙa masu kida da masu rubutu. Sai al'amarin ya ƙara rincaɓewa ne bayan dawowar dimokraɗiyya daga 1999 zuwa yau."
Dangane da tasirin da waƙa kan yi kan masu zaɓe, Sheme ya ce:
"Bincike ya nuna cewa farfaganda kan yi tasiri a siyar duniya ba ma nan ƙasarmu ba kaɗai. Idan ana farfaganda akan ja hankalin talakawa ne ba lallai mutane masu zurfin ilimi cancan ba. Saboda haka su waɗanda aka yi domin su su kan yarda da saƙon musamman idan aka rera waƙar a cikin murya mai daɗi da kiɗa ma jan hankali," in ji Malam Ibrahim Sheme.











