'Trump na son a kawo ƙarshen yaƙi amma Iran ta ƙi bayar da haɗin kai'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Jeremy Bowen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Amurka da Iran duk sun nuna cewa ba su son komawa yaƙi tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a ranar 8 ga watan Afrilu.
Dukkaninsu sun ƙi amincewa kurarin da suke yi wa juna ya sake jeafa su cikin yaƙi tsundun bayan yarjejeniyar da Pakistan da Qatar suka shiga tsakani aka cimma.
Har yanzu akwai sojoji da kayan yaƙin sama da na ruwa na Amurka jibge a kusa da Iran.
Haka nan akwai tabbacin cewa ita ma Iran ta sanya sojojinta cikin shirin ko-ta-kwana kuma ta yi amfani da lokacin tsagaita wutar wajen ƙara ɗamara da kuam gyara wuraren da Amurka da Isra'ila suka lalata mata.
Ɓarkewar yaƙi a yankin Gulf abu ne da ƙarara zai bude hatsarin rashin sanin abin da ka iya zuwa ya koma tsakanin ɓangarorin biyu.
Amurka na ƙoƙarin ci gaba da matsa wa Iran domin ta sassauto ta hanyar nuna cewa tana nan kusa kuma tana iya tafka ta'asa.
Ita kuma Iran tana tunatar da Amurka cewa tana nan kan bakarta kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba idan buƙatar mayar da martani ya taso, za ta iya kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ma fadin ƙasashen yankin Gulf.
Mataki na farko na abun da ya zama tamkar wata doguwar hanya maras iyaka wajen cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran shi ne ci gaba da tsagaita wuta da kuma yarjejeniya ta "fahimtar juna" inda ake ta tattaunawa bisa tattaunawa.
Kaiwa wannan mataki ya zamo mai matuƙar wahala.
Iran na neman diyya, misali ta hanyar cire mata takunkumi ko sakar mata kadarori kafin ta buɗe mashigar Hormuz, wanda hakan ya zama tamkar tushen duk wata tattaunawa mai ƙwari.
A yanzu jiragen ruwa ƴan ƙalilan ne kawai ke ratsawa ta babbar hanyar tekun. Iran ta rufe ta tun bayan da Amurka da Isra'ila suka kai mata hari a ranar 28 ga watan Fabarairu.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Saudiyya na tura wani bangare na man fetur dinta ta tashar jirgin ruwanta da ke kan tekun Maliya sannan kuma Hadaddiyar Daular Larabawa na da wasu’yan bututan ta yankin mashigin gabar Oman, gana da Mashigar Hormuz.
To amma duk da haka duniya na asarar kimanin kashi 20% na man fetur da gas din da ya kamata ta samu da kuma sauran abubuwan amfani.
Rufe mashigar jefa tattalin arzikin akasarin yankunan duniya cikin bala’i. Duk da cewa a yanzu Amurka ba ta dogara kan man fetur din da ke fitowa daga yankin Gulf ba amma farashin man fetur a kasuwannin duniya shi ne ke tantance farashinsa a cikin Amirka.
Donald Trump na cikin tsaka mai wuya. Yana a tsakiyar bala’in da ya takalo bayan ya fada wa Iran da yaki da sa ran cewa zai samu nasara cikin sauki.
Shugaban Amurka da aminisa Firaiminista Benjamin Netanyahu na Isra’ila ba su yi tunanin irin turjiyar da Iran za ta nuna ba da kuma irin hare-haren da za ta iya kaddamarwa ba.
Babu wata hanya mai sauki da Trump zai iya bi ya fita daga wannan yaki, kuma Iran ta fi so a ci gaba da tsayawa a hakan.
Yana bukatar a sake bude Mashigar Hormuz.
Amurkawa da yawa ba sa goyon bayan yakin da kasarau ke yi da Iran, kuma idan aka ci gaba da yakin akwai yiwuwar karin Amurka za su co gaba da nuna adawa da shi.
Babbar matsalar Trump a yanzu ita ce ‘yan barandar jam’iyyar Republican da kuma muradin Trump na ganin ya ayyana nasara kan yakin, ba za su bari ya amince da bukatun da Iran ta gindaya na sake bude mashigar Hormuz ba.
Shugaban na Amurka ba ya kaunar duk wani abu da ya ci karo da yarjejeniyar da ya kulla da Iran ba, hatta batun tsawaita wita domin samun damar tattaunawa da yarjejeniyar nukikiya da Barack Obama ya kulla a 2015.
Trump ya yi watsi da yarjejeniyar a mulkinsa na farko a matsayin shugaban kasar Amurka.
Shugabannin Iran na da imanin cewa suna yaki ne domin tabbatar da ci gaban wanzuwar kasarsu.
A bayyane take cewa duk wani hare-hare da Amurka za ta kai musu bai dame su ba.

Asalin hoton, EPA
Kasar ta yankin Larabawa mai dimbin arzikin mai ta kasance cikin kangin tattalin arzikin na tsawon lokaci, kuma ba za ta so ta ci gaba da kasancewa cikin wannan halin ba.
Tsarin kasuwancinsu da tsarin ci gaban yankin na tsawon lokaci ya dogara ne kan asashe na zama cibiyar tattalin arzikin duniya da zuba jari.
Wannan yaki ya yi mummunar illa ga yankin kuma dawo da martabarsa zai dauki shekaru masu yawa..
Qatar kasa ce mai son shiga tsakani, ga kuma Pakiatan da ke yunkuri a bangaren tattaunawar diflomasiyya.
Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya sun mayar da martani ga Iran ta fannoni daban-daban.
Daular Larabawa ta kara yaukaka dangantakarta da Isra’ila, kasar da ta aika da garkuwar kariyar hare-haren sararin samaniya ga kasar, tare da dakarun Isra’ila wadanda ke kula da su.
Bayanai sun fito cewa Saudiyya ta kai wa Iran hari, inda suka ce sun yi hakan ne domin mayar da martani ka hare-haren Iran. Amma wani abu mai muhimmanci shi ne gwamnatin Saudiyya ta sanar da Iran cewa ta kai hare-haren ne bisa radin kanta, ba wani bangare ne na hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kadammar ba.
Lokacin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran hari duk sun yi ikirarin cewa karfin sojinsu na sama ya isa ya kawar da gwamnatin Tehran.
Amma sun yi kuskure.
Sun gaza fahimtar juriyar gwamnatin da ta jure wa takunkumai da munanan jarrabawar yaki da kebancewa na taawon rabin karni.
Yanzu Amurka da Isra’ila na girbar abinda suka shuka - har ma da sauran duniya.











