Sojojin Mali sun ce a ranar 25 ga Satumba sun kashe ɗaruruwan mayaƙa a wasu samame da suka gudanar a yankunan kudu maso yammaci da arewacin ƙasar, wato Dioila da Kidal.
A wata sanarwa da suka wallafa a shafinsu na Facebook, sojojin sun ce:
“Ranar 24 ga Satumba, mun samu sahihan bayanan sirri cewa mayaƙa tsakanin 200 zuwa 300 sun taru a arewacin Dandougou a yankin Dioila, inda suka kuma jibge manyan makamai da kayan yaƙi.”
Sojojin sun ce bayan sun tabbatar da sahihancin bayanan, jiragen yaƙinsu sun kai hare-hare ta sama kan wuraren da mayaƙan suke, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da lalata kayan yaƙinsu.
Sun ƙara da cewa an gudanar da wani samame a ranar 21 ga Satumba, gabashin birnin Kidal, inda aka kai hari kan wasu ƙungiyoyi biyu na mayaka ɗauke da manyan makamai.
Sojojin sun ce ayyukan tsaro da sa ido na ci gaba da gudana a waɗannan yankuna, domin zaƙulo sauran mayaƙan da suka tsira da kuma kawar da barazanar da suke yi.
A ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, hukumomi na ƙara fitar da bayanan da ke nuna nasara sosai a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Sai dai sau da yawa bayanan na saɓawa rahotannin majiyoyi masu zaman kansu da kuma labaran ƴan gudun hijira, waɗanda ke nuna cewa hare-hare da tashe-tashen hankula na ci gaba kuma babu alamar za su kawo ƙarshe nan kusa.