Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilan ƙungiyoyin fararen hula na kiran Sanata Akpabio ya sauka
Wasu fittatun ƙungiyoyin kare fararen hula a Najeriya sun yi kira ga Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio ya sauka daga muƙaminsa.
Matakin ya zo ne kwanaki ƙalilan bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin wata ƙaramar kotu a kan Farfesa Peter Ogban, baturen zaɓen ɗan majalisar dattijai na Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a 2019, bayan ta same shi da laifin tafka maguɗi.
A ranar Laraba ne dai kotun ɗaukaka ƙarar a Calabar, ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara uku da ƙaramar kotu ta yi wa Farfesa Ogban, saboda ta same shi da laifin shirya sakamakon ƙarya wanda ya bai wa Sanata Akpabio na jam'iyyar APC nasara.
Wata sanarwa da ƙungiyoyin fararen hula 56 suka sanya wa hannu, ta ce hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar, ya haifar da matsananciyar damuwa kan halarcin Akpabio a shugabancin majalisar dattijai.
Sun kuma ce "abin damuwa ne matuƙa cewa zaɓen da ya kawo shi Majalisar Ɗattijai a yanzu kotu ta tabbatar cewa na maguɗi ne.
"A duk wani tsari na dimokraɗiyya, irin wannan lamari yana neman bin bahasi cikin gaggawa da kuma sanin ya kamata daga shugabanni".
Cikin ƙungiyoyin dai har da CISLAC mai rajin kyautata faɗakarwa kan ayyukan majalisa da yaƙi da cin hanci da rashawa.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa, Mallam Auwal Musa Rafsanjani ya yi iƙirarin cewa Akpabio bai ci zaɓensa na 2019 zuwa Majalisar Dattijai ba, don haka kotu ta tabbatar da maguɗin da aka yi.
Ya ce Sanata Akpabio ba shi da cancantar da ta ba shi damar ci gaba da zama a kan muƙaminsa na shugaban majalisar dattijai.
Ƙungiyoyin sun jaddada cewa duk da yake Sanata Akpabio ya musanta hannu a maguɗin, amma samun jami'in zaɓen da ya ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara da laifi, ya dusashe sahihancin zaɓen nasa.
Sun dage cewa jazaman ne Sanata Akpabio ya sauka daga kan kujerarsa na wucin gadi har zuwa lokacin da za a warware wannan batu gaba-ɗaya, don tabbatar da ƙwarin gwiwar al'umma da tabbatar da ikon doka da kuma martabar hukumomin kare dimokraɗiyyar Najeriya.
'Ko Akpabio na da damar sake tsaya wa takara bisa doron ya kamata?'
Ƙungiyoyin fararen hulan sun kuma bijiro da wata muhimmiyar tambaya cewa: bayan tabbatar ya ci amfanin zaɓen da aka yi da maguɗi a 2019 zuwa Majalisa ta 9, ko Sanata Akpabio na da dama bisa doron shari'a da kuma sanin ya kamata, ya sake tsayawa takara zuwa Majalisa ta 10, balle ma har a yi maganar ya zama shugaba?
Sun nunar cewa lamarin, ba batu ne na kare wani mutum ba. Batu ne na dawo da yardar jama'a ga tsarin zaɓen ƙasar.
Rafsanjani ya ce matuƙar Akpabio ya ƙi sauka daga kan muƙaminsa, hakan zai sa 'yan Najeriya su riƙa tunanin dimokraɗiyya ba komai ba ne, face wata hanya " ta rinto, ta ƙarya, ta yaudara, ta cin amana, ta fin ƙarfi, ta nuna amfani da kjuɗi da jami'an tsaro da jami'an zaɓe, don biyan burin wasu"
A cewarsa, dole ne a yi gyara, a koyar da darasi ga waɗanda suka yi ba daidai ba.
"Barin Shugaban Majalisar Dattijai ya ci gaba da zama a muƙaminsa da irin waɗannan tuhume-tuhume masu nauyi, lamari ne da zai yi zagon ƙasa ga aƙidojin dimokraɗiyya kuma zai aika wani saƙo mai hatsari gabanin babban zaɓen 2027," ƙungiyoyin suka ce.
Shi ma shugaban CITAD, da ke cikin ƙungiyoyin da suke kira ga Akpabio ya sauka, Mallam Yunusa Zakari Ya'u ya ce sun shiga cikin waɗannan kiraye-kiraye ne saboda suna da yaƙinin cewa an yi maguɗi a zaɓen Akpabio, tun da kotu ta tabbatar da haka.
Ya kuma ja hankalin al'ummar Najeriya da cewa su ƙyamaci irin waɗannan hanyoyi waɗanda ba na dimokraɗiyya ba, da wasu ke amfani da ƙarfin kuɗi ko na mulki wajen ƙwatar zaɓe.
Ƙungiyoyin dai sun yaba wa Hukumar Zaɓe Mai zaman Kanta ta Ƙasa musamman ma tsohon shugaban INEC na jihar Akwa Ibom, Mike Igini saboda jan ragamar gudanar da binciken da kuma gurfanar da ƙara game da ƙorafin.
Sun kuma roƙi Majalisar Dokokin Ƙasar da INEC da kuma ɓangaren shari'a su ɗauki wannan hukunci a matsayin wata fargarwa ta ƙarfafa tsare-tsaren da za su hana maguɗin zaɓe a dukkan matakai.
Sun kuma yi kira ga shugabancin jam'iyyar APC da ya nuna ƙudurinsa na yi wa harkokin zaɓe garambawul da kuma kafa hujjar aiki da tafarkin dimokraɗiyya ta hanyar fara yunƙurin sake zaɓe a mazaɓar ɗan majalisar dattijai ta Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.