Hana wasu yin takara da Tinubu a 2027 a jam'iyyar APC ba daidai ba ne — ACF

Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, TWITTER/@officialABAT

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya, ACF ta yi watsi da kalaman da ke cewa babu wanda zai fito ya yi takara da shugaba Tinubu a jam'iyyar APC a zaben 2027.

Kungiyar ta ce 'yan arewacin kasar na da damar fitowa takara duk da cewa wasu shugabannin APC a yankin sun goyi bayan takarar shugaban kasar.

ACF, ta ce wadannan kalamai sun sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma irin wadannan kalamai bai kamata su rika fitowa daga bakin wadanda ake yi wa Kallon yi wa shugabanni ba.

Farfesa Tukur Muhammad Baba, shi ne mai Magana da yawun kungiyar tuntubar ta ACF, ya shaida wa BBC cewa, idan dai har ana dimokradiyya sannan ana yenta bisa yadda tsarin Mulki ya tanadar a yanzu,to kundintsarin mulkin ta gindaya wasu ka'idoji da dan kasa zai cika kafin ya tsaya takara.

Ya ce,"A bisa tsarin doka duk mutum in dai dan Najeriya ne ba wai sai dan wata shiyya ko yankin ba kuma ya cika ka'idojin hukumar zabe na tsayawa takara, to zai iya tsayawa takara a duk mukamin da yak e so."

Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya ce "Mu kungiyarmu ba wai jam'iyyar siyasa ce ba, amma muna da sha'awa akan abin da yake na Mulki da kuma siyasa, mu fadakarwace ta mu."

Mai Magana da yawun ACF, din ya ce ya kamata jam'iyyar APC ta sake nazari akan wannan kalamai na ta a bawa kowa dama idan har yana son ya fito takarar shugaban kasa.

To sai dai kuma Malam Bala Ibrahim, daraktan yada labarai na jam'iyyar APC a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, ko shakka babu kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa kowanne dan kasa damar tsayawa takara muddin ya cika ka'idojin da suka kamata, to amma duk da haka akwai soyayya ta jam'iyya.

Ya ce,"Jam'iyya na kasancewa tana da wanda ta ke so ta tsayar ya yi mata takara wanda kuma ya cika sharudan da jam'iyyar ke so don haka sai ta basu takara."

Malam Bala Ibrahim, ya ce "Ba wai dole jam'iyya zata hana mutane takara ba ne idan aka samu wadanda ke son takarar kuma sun cika sharudan da ake so to jam'iyya bawa kowa dama ya tallata hajarsa daga nan kuma sai tantance a zabi wanda ake gani ya fi cancanta."

A watan Mayu ne shugabannin APC a shiyar arewa maso yammaci da suka kunshi gwamnoni da shugabannin jam'iyyar na kasa da jihohi da 'yanmajalisar tarayya da kuma ministoci da jiga-jigan jam'iyyar su ma suka jaddada goyon bayansu ga shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

Duk da cewa kawo yanzu shugaba Tinubu bai fito ya ce zai nemi wa'adi na biyu ba amma masana na ganin yadda 'yansiyasaa suka bige da batun zaɓe tun a yanzu, babban ƙalubale ne ga dimokuradiyya da kuma ci gaban Najeriya.