Da me Turkiyya za ta taimaka wa Najeriya ta fuskar tsaro?

Asalin hoton, Getty Images
A ƙarshen makon da ya gabata ne Najeriya da Turkiyya suka amince da ƙulla yarjejeniyar tsaro tsakaninsu da nufin ƙarfafa rundunar sojin Najeriya a yaƙin da take yi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar tsaron Najeriya, Queeneth Iheoma-Hart ta fitar a ranar Lahadi ta ce yarjejeniyar ta ƙunshi cewa Turkiyya za ta kafa babbar cibiyar horon soji a Najeriya, a wani ɓangare na haɗin gwiwar tsaron tsakanin ƙasashen biyu.
An cimma yarjejeniyar ce lokacin wata tattaunawar diplomasiyya tsakanin ministocin tsaron ƙasashen biyu a gefen taron diplomasiyya na 2026.
Turkiyya na da ƙwarewar ƙera makaman yaƙi na zamani, musamman jirage marasa matuƙa.
Me yarjejeniyar ta ƙunsa?

Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Yarjejeniyar - wadda aka ƙulla tsakanin ministan tsaron Najeriya da takwaransa na Turkiyya - ta ƙunshi samar da babban sansanin bayar da horo ga dakarun Najeriya, kamar yadda shalkwatar tsaron Najeriya ta bayyana.
Inda dakarun tsaron Najeriya za su riƙa samun horo a fannoni daban-daban na yaƙi da matsalar tsaro, kamar ta'addanci da tattatara bayanan sirri da amfani da jirage marasa matuƙa da cire abubuwan fashewa da aka dasa, da kuma atisayen ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.
Baya ga wannan kuma akwai batun musayar fasahohin zamani da kuma fasahar ƙera sabbin makamai na zamani.
Akwai kuma batun ƙarfafa fannin tattara bayanan sirri ta hanyar amfani tauraron ɗan'adam domin magance barazanar tsaron da ƙasar ke fuskanta.
A cewar sanarwar da ma'aikatar tsaron Najeriyar ta fitar yarjejeniyar ta kuma ƙunshi ƙarfafa tsaron iyakokin Najeriya da taimaka wa Najeriya wajen karɓe makaman mayaƙan ƙungiyoyin da suka tuba da shirye-shirye sauya musu tunani.
Queeneth Iheoma-Hart ta ce akwai kuma batun horon ƙarfafa rundunar sojin saman Najeriya, da yiwuwar samun sabbin jirage yaƙi masu saukar ungulu da marasa matuƙa.
Sannan akwai batun horas da rundunar sojin ruwan Najeriya, inda ake sa ran tura wasu sojojin ruwan Najeriya zuwa Turkiyya domin samun horo da kuma yiwuwar samun sabbin jiragen yaƙin sojin ruwa na zamani.
Yarjejeniyar na zuwa ne ƙasa da wata uku bayan da Amurka ta aike da dakarunta kusan 200 zuwa Najeriya domin ayyukan da suka shafi bayar da horo da sojojin Najeriya da kuma taimaka musu wajen tattara bayanan sirri.
Wace riba Najeriya za ta samu?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana da masu sharhi kan al'amuran tsaro sun yi maraba da matakin ƙawancen tsaron Najeriyar da Turkiyya, inda suka ce hakan zai taimaka wa ƙasar yaƙin da take yi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Dr Kabiru Adamu, shugaban Kamfanin Beacon Security and Intellingence limited, ya ce matakin zai taimaka wa Najeriya a fannin tsaronta.
Cikin wata hira da BBC, masanin tsaron ya ce akwai rawar da Turkiyya za ta taka a wannan ƙawance la'akari da alaƙarta da abubuwan da ke haifar da matsalar tsaron.
''Misali, kimiyya da zamantakewar al'umma da kuma alaƙar addini, (Musulunci da Kiristanci)'', in ji shi.
Ya ce idan aka yi la'akari da dangantakar Turkiyya da manyan ƙasashen Turai da kuma yadda dimokradiyya ta yi ƙarfi da tasiri a ƙasar da kuma kasancewarta mamba a ƙungiyar tsaro ta Nato, hakan zai ba ta damar taimaka wa Najeriya a fannonin kimiyya da fasaha da kuam dabarun yaƙi.
"Idan kuma muka duba yadda ake magance ta'addanci, Turkiyya na da tarihin yaƙi da ta'addanci, da sauran matsalolin da suka shafi tsaro, to hakan zai sa Najeriya ta amfana da waɗannan dabaru'', in ji Dr Kabiru Adamu.
Ya kuma ce akwai yiwuwar sojojin Najeriya su samu horon tsarin gudanar da yaƙi da ƙungiyoyin ta'addanci.
''Kasancewar za a tura sojojin Najeriya kusan 200, kuma akwai yiwuwar kafa sansanin horar da soji a Najeriya, to muna fatan sojojin Najeriya su samu horon tsarin gudanar da yaƙi da kuma tattara bayanan sirri'', in ji shi.
Ƙawancen tsaron zai wadatar?
Ba wannan ne dai kaɗai ƙawancen tsaron da Najeriya ta ƙulla da wasu ƙasashe a ƙoƙarinta na magance matsalolin tsaronta.
Mutane da dama dai an ganin cewa ba ƙawancen tsaro kawai Najeriya ke buƙata ba, ita ma akwai rawar da za ta taka na ƙashin kanta don magance wasu matsalolin.
Dr Kabiru Adamu ya yi gargaɗin cewa dole ne Najeriya ta magance matsalolinta na cikin gida idan tana son kowace irin ƙawance tsaron da ta ƙulla ta yi aiki yadda ake so.
''Akwai matsalolin da ƙawancen tsaro ba zai magance wa Najeriya su ba, kamar yawan jami'an tsaro da kayan aikinsu da walwalarsu, dole ne sai Najeriya ta magance su da kanta'', in ji shi.
Ya ce Najeriya na buƙatar yin wani gagarumin garambawul a fannin tsaron ƙasar da kuma yadda ake gudanar da fannin tsaron.
''Waɗannan abubuwa ba ƙawancen tsaro ba ne zai magance mana su ba, mu ne da kanmu za mu tashi domin gyara su'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Yaya ƙarfin Turkiyya a fannin tsaro?

Asalin hoton, Getty Images
Turkiyya na cikin manyan ƙasashe 10 mafiya ƙarfin soji a duniya a 2026, kamar yadda shafin Global Fire Power (GFP), mai nazarin ƙarfin sojin ƙasashen duniya ya nuna.
Ƙasar - wadda mafi yawan al'ummarta Musulmai ne - na da tsohon tarihin yaƙe-yaƙe a zamunnan da suka shuɗe, inda take da manyan daulolin da suka yi tasiri a duniya a shekaraun baya.
A cewar shafin (GFP, Turkiyya na da yawan sojoji kimanin miliyan 1,011,000, da suka haɗa da 481,000 masu aiki da kuma 380,000 da ke jiran ko-ta-kwana, sai sauran jami'an tsaro 150,000.
Turkiyya na da sojojin ƙasa 401,500 da na sama 52,850 da na ruwa 100,000, in ji shafin na GFP.
Ƙasar na ta kafa kanta a fannin tsaro cikin takwarorinta ƙasashen duniya. Tana da manyan jiragen sama na yaƙi irin na zamani.
Kuma tana cikin ƙungiyar tsaro ta NATO, wanda hakan ya ba ta damar mu'amala da manyan ƙasashen duniya.
Turkiyya ta ƙware sosai a fannin ƙera jirage marasa matuƙa da sashen tattara bayanan sirri.
A a cewar shafin GFP, a wannan shekara ta 2026 Turkiyya ta ware wa fannin tsaronta dala biliyan 51 a kasafin kuɗinta, wani abu da ke nuna yadda ƙarfin ƙasar yake a fannin tsaro.











