Yadda ake tababa kan zaɓen fitar da gwani na Tinubu

Bola Tinubu

Asalin hoton, @officialABAT

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wasu masana siyasa a Najeriya, na nuna shakku a kan yawan kuri'un da aka ce Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta gudanar.

Masanan sun ce nasarar da Tinubun ya samu ba abin mamaki ba ne, amma yawan kuri'un da aka bayyana su ne abin mamakin.

Farfesa Abubakar Kari, na jami'ar Abuja, ya ce akwai ayar tambaya wadda za a sa a kan jumullar kuri'un da Shugaba Tinubu ya samu.

Cikin wata hira da ya yi da BBC, Farfesa Kari, ya ce," Ba makawa dama zai samu wannan takara domin wanda suka yi takara da shi ba a san shi ba.

To amma babban abin mamakin shi ne zaben da aka yi a dubban rumfuna ya samu miliyan takwas da 'yan kai, to sai ga shi wanda aka ce an yi a daidaikun wurare a ce an samu kuri'a fiye da miliyan 10, gaskiya wannan jumulla mutane da dama za su yi shakku a kanta."

" Baya ga shakku a kan wannan zabe ko kuma yawan kuri'un da aka ce Tinubun ya samu a zaben fitar da gwanin da mutane za su yi, tsoro ma zai shiga zukatan jama'a a kan abin da zai je ya dawo." In ji Kari.

A ranar Asabar, 23 ga watan Mayun 2026, ne jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwamnoni inda a washe gari kuma jam'iyyar ta tabbatar da shugaban kasar, Bola Tinubu a matsayin dantakararta a zaben 2027 bayan nasarar da ya samu.

APC ta ce Tinubu ya samu kuri'u kusan miliyan 11 inda ya doke abokin hamayyarsa Stanley Osifo da suka fafata a zaben fitar da gwanin da aka gudanar.

Shugaban na Najeriya ya yaba da yadda aka gudanar da zabukan fitar da 'yan takara a jam'iyyarsu ta APC, inda ya ce ba wa kowa dama ya tabbatar da ci gaban dimokradiyyar musamman a jam'iyyarsu.

APC dai ta ce ta gudanar da zaben da ya tabbatar da Tinubun a matsayin dan takararta na shugaban kasa a kananan hukumomi 774 na jihohin Najeriya 36.

Shugaban kwamitin zaɓen shugaban ƙasa na APC, Sanata Anyim Pius Anyim ne ya sanar da sakamakon ranar Lahadi, bayan kammala tattara ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen na ranar Asabar a faɗin Najeriya.

Jam'iyyar ta miƙa shaidar lashe zaɓen ga Tinubu da kuma tutar jam'iyyar a matsayinsa na ɗantakararta na 2027.

Daga bisani Osifo ya taya Tinubu murnar lashe zaɓen, inda ya gaisa da shugaban a wajen taron.