'Irin lalatar da Epstein ya yi da mu' - Matan da suka fuskanci cin zarafi

Asalin hoton, Thierry Humeau
- Marubuci, Ana Faguy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Washington
- Lokacin karatu: Minti 5
Joanna Harrison ba ta so yin magana kan cin zarafin da ta fuskanta a hannun Jeffrey Epstein ba, wanda aka samu da laifin cin zarafin lalata.
Kamar sauran mutane da suka fuskanci cin zarafi, ta ce ta ji ƙunyar abin da Epstein ya aikata mata.
Sai dai bayan fitar da sunanta cikin jerin sunayen miliyoyin mutane da gwamnatin Amurka ta yi, ta faɗa wa BBC cewa ta ji cewa akwai buƙatar ta fito ta yi magana.
"An kai lokacin da ka na cikin wani hali kuma ka na buƙatar numfashi, kuma ina jin wannan ita ce hanyar da na ɗauka na yin haka," in ji Harrison.
Wani shirin BBC ya tattauna da Harrison da wasu matan da suka fuskanci zarafi su huɗu, inda suka haɗu a ɗaki ɗaya.
Lokacin tattaunawar ta tsawon sa'o'i, sun fashe da kuka lokacin da suka ga hotunan haɗuwarsu da Epstein.
Sun bayyana labaransu masu cike da jimami, tausayi da kuma ɓacin-rai.
Wasu sun sake ziyartar wani tsibirin Epstein na musamman, yayin da wasu suka tuna fargaba da suka shiga.
Sun ce sun yi imanin cewa manyan masu hannu da shuni da ya yi alaƙa da su, wataƙila sun san abin da ke faruwa.
Abin da Harrison ta fuskanta
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta saki miliyoyin takardu da suka shafi binciken Epstein, sai dai wasu daga cikin takardun da ba su ɗauke da bayanan sirri, ba su ɓoye sunayen waɗanda ya yi lalata da su ba.
Harrison na ɗaya daga cikin mutanen da aka fitar da sunanta ga bainar jama'a.
Ta faɗa wa shirin BBC Newsnight cewa ba ta so a saki takardun ba, inda take fargabar za a ga sunanta.
"Ba abu ne mai kyau ka ga fuskar wanda ya ci zarafinka a talabijin kullu yaumin har na tsawon shekara shida ba," in ji Harrison.
Ta tuna lokacin da suka haɗu da Epstein a Florida lokacin tana shekara 18, kuma kamar sauran waɗanda aka ci zarafi, ta ce komai ya fara ne da tausa.
"Komai ya kasance a tsare," a cewar Harrison. "Lokacin da ya fara wasa da al'aurarsa, na tsorata matuka. Ba na tunanin na faɗi ko da kalmomi biyu a cikin mota lokacin tafiya zuwa gida."
Daga baya ta tuna yadda Epstein ya yi mata fyaɗe ranar murnar haihuwarsa.
Da take magana a bainar jama'a karon farko, Harrison ta ce ta yi shakkun cewa ita da sauran waɗanda aka ci zarafi ko za su samu adalci ganin yanzu Epstein ya mutu. "Ina da tambayoyin da ba zan taɓa samun amsarsu ba."
Balaguro zuwa ƙasashe 5 cikin kwana biyar
Chauntae Davies ta nuna wa BBC hotunan da ba a taɓa gani ba na lokacin da take balaguro da Epstein a jirginsa zuwa Afirka.
Hotunan sun haɗa da wasu mutum Ghislaine Maxwell da tauraron fim Kevin Spacey da kuma tsohon shugaban ƙasar Amurka Bill Clinton. Spacey da Clinton na balaguro ne don zuwa wani aikin jin-kai na ƙarfafa ba da agaji.
"Na rubuta a mujallata a lokacin cewa waɗannnan su ne manyan da mutane da za ka iya haɗa wa wuri ɗaya... balaguro ne zuwa ƙasashe biyar a cikin kwanaki biyar," in ji ta.
Mun ci abinci, mun yi wasa sannan mun ba da labarai cikin jirgin.
Davies ta ce Epstein ya yi mata fyaɗe a wani tsibirinsa bayan da aka ɗauke ta ta yi masa tausa.
Ta tuna cewa a lokacin ta yi wa Bill Clinton tausa a wuya da kuma bayansa a filin jirgin sama na Portugal yayin da ake saka wa jirgin mai. A lokacin, ta ce ta rubuta a mujallarta cewa shugaban ya na da dattako da kuma kirki.

Asalin hoton, Chauntae Davies
An tambayi tsohon shugaban ƙasar tattaunawarsa da Davies lokacin da ya bayyana gaban wani kwamitin majalisar dokokin Amurka a watan Fabrairu. Ya faɗa cewa ya so da Davies ta faɗa masa ɓarnar da Epstein ya aikata.
Sai dai Davies ta ce ba ta yi niyyar faɗa wa Clinton batun ba: "Ba zan taɓa yin maganar da kowaye ba."
"Me zai iya yi da an faɗa masa? Shin da Clinton zai iya dakatar da abin?" kamar yadda Davies ta yi tunani kan ɓarnar Epstein. "Ina ganin ba za mu taɓa sani ba."
Akwai wani lokaci, da Davies ta taimakawa Clinton sayan sarka wa ƴarsa a Portugal.
Clinton ya sha nanata cewa bai gamu da lalatar da Epstein yake aikatawa ba. Sunansa ya fita cikin ɗaruruwan takardu da aka fitar.
Bayyanar sunan mutum cikin takardun ba ya nufin cewa mutum ya aikata wani laifi.
Spacey ya fito ya yi kiran cewa a sake dukkan takardun Epstein, inda ya ce: "Ga mu da ba ma tsoron komai, gaskiya kawai muke so ta bayyana."

Asalin hoton, Chauntae Davies
'Ina son yin abubuwa kan mutane'

Asalin hoton, Thierry Humeau
Epstein ya sha alfahari da cewa ya san manyan mutane da kuma abokai masu hannu da shuni, a cewar Davies.
Ta ce ya yi alfaharin bai wa Sarah Ferguson, tsohuwar Sarauniyar New York rancen kuɗi. "Ba abu ne ɓoyayye ba," kamar yadda Davies ta faɗa wa BBC.
Akwai hotunan Ferguson tare da tsohon mijinta, Andrew Mountbatten-Windsor, da kuma ƴaƴansu mata a cikin takardun Epstein.
Wata mai kayan ƙawa Phillips ta bayyana alaƙar Epstein da Andrew kuma ta sake faɗin labarin wata ƙawarta, wada ba ta yi magana a bainar jama'a ba wadda aka umarta da yin jima'i da Andrew.
Ta ce ƙawarta ta je gidan Epstein a birnin New York a 2003 inda aka kai ta wani ɗaki don yin jima'i da wani mutum da ta ce Mountbatten-Windsor.
Sai dai Mountbatten-Windsor ya sha musanta zargin.

Asalin hoton, BBC Newsnight
Phillips ta faɗa wa BBC cewa daga baya ta tambayi Epstein dalilin da ya sa ya ce ƙawarta ta yi jima'ai da Mountbatten-Windsor. Ta ce ya faɗa mata cewa: "Ina son yin abubuwa kan mutane."
"Yana son ganin tsoro a idonmu," in ji ta. "Ina jin ya ji daɗin ganin mamaki da muka yi kuma bai san me zai yi ba."
A tattaunawar ta BBC, Phillips ta yi kira ga ƴansandna Birtaniya da su yi magana da ita kan abin da ta sani kan cin zarafin da ƙawarta ta fuskanta da kuma hannun Mountbatten-Windsor.
An kama Mountbatten-Windsor a watan Fabrairu kan zargin aikata ba daidai ba a wajen aiki.
Tuhumar ta shafi zargin cewa ya bai wa Epstein bayanan sirri da bai kamata ba lokacin da yake a matsayin jakadan kasuwanci na Birtaniya.
Waɗanda aka yi lalatar da su, da suka tattauna da BBC sun ce ba su amince cewa Epstein ne ya kashe kansa ba.
"Mun san shi, mun san wane irin mutum ne shi," in ji Phillips.
An samu Epstein a mace a wani gidan yarin birnin New York ranar 10 ga watan Agusta yayin da ake tsare da shi, kan zargin lalata na jima'i da kuma haɗa baki don aikata laifi.











