Trump ya ce yana son mallake man ƙasar Iran

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump na Amurka ya ce yana son mallake man Iran, kuma mai yuwuwa ya ƙwace tsibirin Kharg - inda yawanci Iran take samun man da take fitarwa waje.
Shugaban yana magana ne da jaridar Financial Times, yayin da dubban sojojin ƙundumbala na Amurka ke kan hanyarsu ta zuwa yankin na Gabas ta Tsakiya.
Wakilin BBC ya ce, da yake magana a cikin jirgin shugaban ƙasa - AirForce One a daren da ya gabata - Trump ya ce Iran a shirye take ta miƙa tsibirin, in ba haka ba zai zama ba ta da wata sauran ƙasa kuma.
Sai dai kuma daga baya Trump din ya ce za a iya cimma matsaya da Iran, yana mai bayyana jagororin ƙasar da cewa suna yin abin da ya dace.
Yaƙin na Iran ya sa farashin mai a duniya na ta tashi, inda a yanzu haka ɗanyen man samfurin Brent ya sake tashi zuwa kusan dala 116 kan kowace ganga.














