Su wane ne ƴan wasan gaba da suka fi ƙwazo da zura ƙwallo a tarihi?

- Marubuci, Alex Bysouth
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport senior journalist
- Lokacin karatu: Minti 4
Za a iya cewa tun yana shekara 18, gwarzon ɗan kwallon Brazil, Ronaldo ya shiga jerin ƴan wasan gaba da ake ji da su.
A lokacin yana zura ƙwallaye kamar ruwa a ƙungiyar PSV, ga kuma yanka a kafarsa da kuma salon burgewa wajen cin kwallo, abin da ya haska shi har ya koma Barcelona da kuma Inter Milan kafin shekara 21.
A matsayinsa na matashin da ya taɓa lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon duniya Ballon d'Or bayan zura kwallaye 200 ga ƙungiya da kuma ƙasarsa, Ronaldo mai shekara 23 ya nuna cewa zai mamaye ɓangaren kwallon kafa - idan ba gwiwarsa da ta kawo masa cikas ba a watan Afrilun, 2000.
Duk da haka, hakan baya nufin cewa tauraruwarsa ta dakushe a lokacin, sai dai raunin ya buɗe kofa ga wasu su ma su haska - shin wane ne ɗan wasan gaba mafi hazaƙa a ƙarni na 21?
Mun iyakance jerin zuwa ga mutum goma, wanda ba abu ne mai sauƙi ba.
Shin batun cin kwallo ne kaɗai?
Cin kwallaye, abu ne mai kyau da ɗan kwallo zai fara da shi. Olivier Giroud ya jagoranci Faransa lashe gasar Kofin Duniya a 2018 ba tare da cin kwallo ɗaya ba, amma wannan ba abu ne da zai ɗore ga ɗan wasan gaba ba.
Duk da cewa ba za ka yanke wa ɗan wasan gaba hukunci kan cin kwallaye kaɗai ba.
Lionel Messi ya lashe kyautar wanda ya fi zura kwallaye a Turai har sau shida - sama da kowa a tarihi. Erling Haaland shi ne ɗan wasa ɗaya tilo da zai iya zarta Messi a ɓangaren cin kwallo a kowane wasa a gasannin Turai biyar a wannan ƙarni.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai za a iya ɗaukar Messi a matsayin ɗan wasan gaba?
Neymar ma ya shiga cikin wannan jeri. Francesco Totti ya lashe kyautar ɗan wasan da ya fi zura kwallo a gasar Serie A, sai dai ba za a iya cewa ɗan wasan gaba ne kai-tsaye ba saboda an fi sanin da rarraba kwallo ko ta ina cikin fili. Raul yana cikin jerin ƴan wasan gaba masu haɗari da suka buga wa Real Madrid, ciki har da Ronaldo, Ruud van Nistelrooy da kuma Gonzalo Higuain...
Luis Suarez daga Barcelona yana cikin jerin shi ma, inda ya assasa kansa a matsayin ɗan wasan da ya iya zuwa kwallo, baya ga irin abubuwan da ya yi a Ajax da Liverpool.
Ɗan asalin Uruguay ya zura kwallo sau 195 a cikin wasanni 283, wanda na cikin abin da ya janyo masa farin jini a Barcelona, ga kuma hazaka da ya nuna a Atletico Madrid, inda ya taimaka musu lashe gasar Laliga ɗaya.
Erling Haaland ya shiga cikin jerin 10 da muka fitar waɗanda asalin gurbinsu shi ne buga gaba. Tsayi, ƙarfi da kuma kuzari - kaɗai bai wadatar ba ga ɗan wasan gaba, sai ya haɗa da cin kwallaye cikin sauri a gasar zakarun Turai fiye da kowa a tarihi.
Alkaluma sun nuna Haaland na cin kwallo ɗaya a kowane wasa, musamman a gasar zakarun Turai, inda yake da kwallaye 56 cikin wasanni 56 - ɗan wasan mai shekara 25 ya buga wa Red Bull Salzburg, Borussia Dortmund sai kuma Manchester City a yanzu.
Yawan kwallayen da Messi da Ronaldo suka ci lokacin da wasan Clasico ta kai kololuwa sun zarta tunani - ba kamar waɗannan biyu ba, Haaland ya zura kashi 95 na kwallayensa ne a cikin yadi na 18
Ɗan asalin Norway, ya kuma kasance ɗan wasa tilo da ya karkare gasar Premier da zura fiye da kwallo ɗaya a wasa.
Miroslav Klose ya samu shiga jerin mutum 10 bayan kasancewa wanda ya fi zuwa kwallo a gasar kofin duniya - kwallo 16 a gasanni huɗu a wannan ƙarni ya sa ya ɗara Ronaldo na Brazil da kwallo ɗaya. Shi ne kuma ya fi kowa zura kwallo a tarihin Jamus.
Sai kuma, Robert Lewandowski, ɗan wasan gaban Poland ya zura aƙalla kwallo 30 a cikin kakar wasanni 14 da suka wuce, in ban da guda uku - ya kuma taimaka an zura 141.
Lewandowski ya taimakawa Dortmund lashe Bundesliga biyu, sai kuma guda takwas da Bayern Munich da Champions League, kafin ya koma Barcelona ya kuma lashe Laliga biyu.
Harry Kane ya maye gurbin Lewandowski a Jamus yadda ya kamata.
Kane mai shekara 32 yanzu, ya lashe Bundesliga a bara, ga kuma kyautar ɗan wasan da ya fi zura kwallo - ya zama mutum na farko da ya zura kwallo 100 cikin wasanni 104 ga ƙungiya ɗaya a wannan ƙarni.
Yanzu kwallayensa sun kai 500.
Salon wasansa da kuma yadda yake sarrafa kwallo, ya sauya yadda mutane ke kallon ɗan wasan gaba.
A question of aura?
"Na zo kamar wani sarki, na tafi kamar gwarzo," a cewar Zlatan Ibrahimovic bayan zura kwallaye 38 a wasanni 31 a gasar Ligue ta Faransa a shekararsa ta karshe da PSG.
Ya lashe gasanni 12 a ƙungiyoyi da ya buga, sai kuma Europa League a Manchester United.
Thierry Henry na cikin ƴan wasan gaba da suka iya zura kwallo, inda yake cin kwallaye masu armashi da kuma saka annashuwa.
Arsene Wenger ne ya taimaka wajen sauya salon taka leda na ɗan wasan, inda har ta kai ya zura kwallo 18 bayan juyawa zagaye na biyu na gasar Premier a kakarsa ta farko, kafin daga bisani ya lashe Euro da Faramsa.
Ya lashe Champions League a 2008 da ƙungiyar Barcelona.
Didier Drogba ma na da wani irin salo na daban. Ya kasance mai haɗari ga ƴan wasan baya. Ya koma Chelsea yana da shekara 26.
Ya kasance ɗan wasa mai muhimmanci lokacin zamanin Jose Mourinho a Chelsea.
Mutane da dama za su kalubalanci jerin. Yayi da Cristiano Ronaldo ya kasance ɗaya daga cikin ƴan wasan da suka fi iya zura kwallo, bai fara bugawa a matsayin ɗan wasan gaba har sai da ya kai shekaru 30.
Sai dai, tsohon abokin wasan Ronaldo, Wayne Rooney shi ma ya ƙware a ɓangaren cin kwallo musamman idan aka duba wannan jeri.
Maimakon haka, ana cewa Karim Benzema na cikin mutanen da suka taimakawa Ronaldo zama haɗari a lokacin da yake Real Madrid. Ya zura kwallo sama da 30 a cikin kakar wasanni huɗu cikin biyar bayan tafiyar Ronaldo zuwa Juventus, ya kuma lashe Ballon d'Or a 2022 da Champions League biyar jimilla.











