Yaushe ne tashin duniya, kuma ta yaya hakan zai faru?

Hoton duniya

Asalin hoton, Fotograzia via Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Mutuwa mai sanyi, duhu kuma a hankali. Ƙarshe mara kyau. Ko kuma ƙarshen da zai buɗe hanyar sabon babi?

Waɗannan na cikin abubuwan da mutane ke faɗin cewa duniya za ta kasance ko hanyar da za ta kare a nan gaba - idan ma har za ta kare.

Batun ƙarewar duniya ya kasance wata tambaya da ke rikita kimiyya har zuwa yanzu, har ta kai masana sun ce yawan tambayoyi kan ƙarewar duniya sun fi amsoshi yawa,

Sai dai, domin sanin yadda duniya za ta ƙare, dole ne mu san yadda ta fara.

Farawar duniya

Duniya ta ƙunshi dukkan abubuwa da suke wanzuwa: Sararin samaniya, makamashi har ma da lokaci, a cewar hukumar sararin samaniya ta Amurka NASA.

Masana sun ce duniya ta fara ne shekaru biliyan 13.8 da suka wuce, lokacin duniyar na yanayin tsananin danshi da kuma zafi, kuma tun lokacin ne take ta yaɗuwa.

Yayin da ta yi ta wanzuwa, an kuma samar da ƙananan duniyoyi da taurari sannu a hankali.

Daga wancan lokaci ne kuma duniya ta yi ta faɗaɗa har zuwa yau.

Duniya

Asalin hoton, FlashMovie via GettyImages

Bayanan hoto, Duniya ta fara ne a wuri ɗaya sannan ta yi ta wanzuwa

Maganar gaskiya ita ce abu kaɗan ne kawai muka sani kan abubuwan da suka faru.

"Aikin mu shi ne kamar saka ido a ɗaukacin kogi da ɗabi'unsa, ba tare da duba yanayin kowane irin ruwa da ya wuce ba," in ji Farfesa Alexander Zabot, malami a jami'ar tarayya ta Santa Catarina da ke Brazil.

Gaɓar mutuwa

Idan duniya ta ci gaba da faɗaɗa, makamashi zai ƙaru ta yanda dunyoyi da ke sararin samaniya za su yi nausawa, taurari za su daina samuwa, sannan waɗanda ake da su za su mutu.

Yayin da tiriliyoyin shekaru suka wuce, duniya za ta yi ta zama cikin duhu, inda za a kusa kai ka tsananin sanyi, inda za ta zama tamkar babu abin da ya rage.

Za kuma a kai ga matakin yanayi zai kasance wuri ɗaya.

Wani Farfesa a jami'ar Sao Paulo da ke Brazil, raul Abramo ya ce: "alamu sun nuna cewa a lokacin duniya za ta kasance babu komai a cikinta, mai tsananin sanyi da kuma mai nisa idan ta kusa karewa.

Ya ƙara da cewa: "duniyoyi a samaniya za su yi nisa, sannan taurari za su tsufa su mutu... lokacin ne duniya za ta koma wani abu na daban tamkar makabarta.

Duniya

Asalin hoton, Arctic Images via Getty Images

Babbar rugujewa

Akwai ƙarin abubuwa da za su faru.

Idan ƙarfin abubuwa ya riƙa raguwa, za a kai yanayin da duniya za ta koma wuri ɗaya.

Wannan zai janyo afkuwar babbanrugujewa, a cewar NASA.

Wani abu kuma da masana suka bayyana shi ne duniya za ta koma wuri ɗaya kamar yanda ta fara.

Duniya

Asalin hoton, Fotograzia via Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai kuma wasu abubuwa da za su faru.

Idan aka ci gaba da samun duhu, tasirinsa zai mayar da ɗaukacin duniya zuwa wuri guda, inda duniya da kanta za ta ruguje, a cewar NASA.

Sai dai Abramo ya ce: "Wannan hasashe ne, saboda ba mu da alkaluma ko hujjoji na gaskata hakan."

Shin za a iya kayyade lokacin da duniya za ta kare? Amsar shi ba za a iya ba.

Abramo ya ce: "Babu alamu da ke nuna cewa nan gaba duniya za ta ruguje ko rufta baki ɗaya."

Zabot ya ƙara da cewa wasu sun yi hasashen cewa duniya za ta kare bayan tiriliyoyin shekaru, yayin da wasu kuma suka wuce zai zarta hakan.

Idan shekarun duniya ba su wuce aƙalla shekaru biliyan 13.8, to akwai sauran lokaci kafin ya kai shakaru tiriliyon.

Wani bincike da jami'ar Radboud da ke Netherlands ta yi, ya nuna cewa duniya na ruɓewa cikin sauri ba kamar yadda aka yi tunani a baya ba, yayin da ɓurbushin taurari zai ɗauki tsawon shekaru kafin su ɓace.

Babu tabbacin cewa akwai wani ɗan'adam da zai rage don ganin lokacin.

Ita duniyar da muke cikinta ta Earth ana sa ran za ta ɓace tsawon lokacin kafin karewar duniya, lokacin da rana za ta koma wani launi jazir bayan kusan shekaru biliyan shida.